Sashe 11
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da danne acin ranta duk da dama mari ba wani bakon abu bane a wurinta. "Durkusawa fa kika ce EESHART? To ko jiya gama baki labari ne ban yi ba ni da ABBAS ya tsinke ni da mari a take na aga hannu na rama, sannan na bishi da bakaken maganganun da suka fusata shi ya sawwake mini amma ke ba wani babban abu ba ya mare ki amma kin kasa kata us, dama haka masu ku in suke?" Diriricewa ta yi ta ma rasa abin cewa nan ta kawar da maganar tare da shigo da hirar babban rashin da ABBAS ya yi da ya da ya rabu da ita tabbas za ta auri attajiri nan ta ci gaba da ota ta a RU IYAR IGIYA ita kuma tana hawa. Sai da ta yi magriba sannan suka ci abinci don ko da Alhaji Yusuf in mijin EESHART ya sakko zai fita sai bu a kamshi yake watakila ita dai SALIMAH ba ta raba ayan biyu zance zai je duba da yanayin shigar da ya yi. Ko da SALIMAH ta gaishe shi a ciki ya amsa ita kuma EESHART cikin kalmashe murya ta ce masa. "A dawo lafiya" Amma ya ba bango ajiyarta. Sallama ta mata ta bata kama hanyar gida, da ta saba in ta zo tana bata dubu biyu ta ce ta hau napep amma yau ko naira biyar bata ba ta ba, tana zuwa gida ta yi sallar isha'i ta kwanta tana an charting yau dai EESHART ta kula ta sun yi magana ba kamar jiya ba amma da alama har yanzu tana jin kunyar abin da ya faru. Wannan karon mmn afrah ba dariya za ta baku ba, labarin yana auke da sarkakiya, cin amana, butulci soyayya mai zafin maraici labari ne da zai ta o mana angarori da dama. Ba zan warware muku komai na labarin ba ku dai ku yi jumurin bina har karshe mu warware tufkar a tare a nan ne za ku gane mai ya sa aka sanyawa labarin RU IYAR IGIYA. 09013181851 IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 5 "ABBAS" Suka ha a baki wajen fa a cike da mamaki, wani takaici ne ya turnuke SALIMAH ita a halin da ake ciki ko sunansa bata so ta ji an ambata. "Umma kin ga an nacin nan ya zo ko? Har kina cewa tun da ya ji ciwon abin da na masa har ya iya furta sakin ya rabu da ni kenan, ina ganin na yadda kwallon mangwaro kuda ya daina addabata ashe dai na fahimci abin a baibai" SALIMAH ta ce tamkar ta yi kuka. Shi yaro yana gama fa a musu sunan mai kiran ya juya ya tafi ya je ya cewa su ABBAS in tana zuwa. "SALIMAH idan baki yi da gaske ba wannan an anacen sai ya hana ki rawar gaban hantsi, domin zai hana ki cin duniyarki da tsinken tsire, dole ki tashi haikan ki je ki tauna tsakuwa don aya ta ji tsaro. Idan har kika masa sakwa-sakwa ya samu dama wallahi zai kore miki duk wani bazawari da zai zo wajenki da sunan so, idan baki sani ba ki sani, idan bacci kike ki farka duk wata bazawara da ta fito daga gidan aure to idan har tsohon mijinta zai ke diddiftu a kofar gidan su to babu mai cigaba da zuwa wajenta kowa zai ke ganin gidan tsohon mijin za ta koma ko da kuwa ita bata da niyyar hakan, shikenan zai sa ki yi biyu babu gwara ki fita a yi ta a watse" Umma ta ce cikin hargagi saboda gaba aya ta auka wani Alhaji ne mai fa a a ji ya zo ashe dai wancan ahalul fukara'un ne da bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba. SALIMAH da ta cika ta yi fam gaba aya ku ubar mahaifiyarta ta shiga kunnuwanta da kwakwalwarta, ta kara gane irin rusa mata burin da ABBAS zai yi in dai yana zuwa hakan ya sa ta ci alwashin taka masa birki. "Wallahi Umma bai isa ba, na rantse da Allah ba zan lamunci wannan abin ba, wannan talakan ya ga makwacina da yawa wane shegen ne ya ce masa ni SALIMAH zan ta a komawa gidansa wallahi ko a mafarki na ga na doshi cikin gidan ABBAS zan kwa awa kaina mugun marin da zai sa na farka daga mugun bakin mafarkin komawa gidan talauci" Ta ce a fusace don har ta fi Ummar ma fusata saboda sai yanzu ne ma Ummar ta haska mata wani duhun ta ga haske. Buguzum-buguzum ta shige aki sai ga ta ta fito da mayafi sakale a kafa a, wani karanin bokiti ta auka ta nufi wajen gasarar kokon Umma wanda ruwan saman gasarar yake da tsami irin na ruwan tsari, tsiyaya ta yi sai da ta cika bokitin fal, ta nufi hanyar fita. "Kar ki masa da sauki kin ji na fa a miki" Umma ta ce amma SALIMAH ko amsa bata samu damar ba wa Umma ba, saboda yadda take jin tukukin bakin cikin jin ABBAS a kofar gidansu.. Tsaye ta same su, FAROUQ jingine da machine yayin da ABBAS yake tsaye yana rungume da hannunsa a kirjinsa, wurin gaba aya ya kaure da kamshin turare musamman na ABBAS da ya fi yawa da da in kamshi. Da yake dama kofar gidan yake fuskanta tun da yaron ya ce tana zuwa sai ya ji da i a ransa ko ba komai zai ganta don bai ma yi zaton za ta fito ba, don lokacin da ta yi yaji sai dai ya gaji da tsayuwa ya tafi ko ta cewa an aiken ba za ta zo ba shi kuma ba shi da damar shiga gidan nasu yadda suke tsaki da tsakuwa shi da Umma tun da bata kaunarsa.. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke hangota da ya yi ta fito, a duniya ba ya ganin kowace mace sai SALIMAH ya auke ta tamkar sarauniyar mata kasancewarta sarauniyar zuciyarsa, ganinta yake tamkar awisu jin ta yake tamkar numfashinsa, rayuwarsa ha e yake da ita saboda kaunar da yake mata. Bai lura tana auke da wani abu a hannunta ba, ya shagala da kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata da ya haske duniya. Tunani yake a ransa ya aka yi ya aga hannu ya mari wannan fuskar da take da matukar daraja a wajensa. "Waye yake kirana a cikin ku?" Ta tambaya cike da rainin hankali ko arzikin yin sallama basu samu ba. FAROUQ da dama a kufule yake na shanyar da aka musu suke tsaye zaman jiranta jin kalaman rainin hankalin da ta yi ya mayar mata da martani. "Waye kike ganin zai zo wajenki a cikinmu? Ni dai ban miki kama da wanda zai zo wajenki ba ko cikin mafarkin ki" "Haba FAROUQ kai da ka rakoni sasanci bai kamata ka mayar da martani haka ba, a kalla sai ka ce mata ABBAS ne" "To kai in ba tambayar rainin hankali ba ai ta san waye ya zo wajen nata ko yaron da ka aika ai ABBAS ya ce yana kiranta, kuma abin haushin kai baka fahimci ko darajar ta mana sallama bamu samu ba?" "Wa ya gayyatoku da har zai muku sallama? Ku kuka akko kafafunku masu kama da na kwa o kuka zo, to bari ku ji in fa a muku bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane iya gani iya kyalewa ni yanzu na maka nisa kwatankwacin nisan da yake tsakanin sama da kasa, sau nawa zan fa a maka ABBAS na tsane ka! Na tsani mai kaunarka, bana son duk wani abu da ya danganceka, mai ya sa baka da zuciya mai ya sa ka bari kare ya cinye maka zuciya? Mai ya sa kai kawai hangena kake baka ganin mugun talaucin da kake ciki wanda ya maka kamun kazar kuku, ka rubuta ka ajiye na barka har abada yadda na fito daga gidanka da sunan matarka na fito fitowa ta har abada ko gawata na ji an saka a gidanka idan da hali zan yunkura in fito daga ciki" Tun da ta fara maganganun yake kallonta duk da yana jin ciwo a zuciyarsa amma kuma a wani sashen na zuciyarsa ya kasa ganin abin da take yi laifi ne, bai san mai ya sa ba ba ya ganin laifin SALIMAH ko abu ta masa zai ji haushi amma na an lokaci ne daga abin ya gushe zai ji ba ya ganin laifinta sai dai wani ya ga laifin nata ko wani ya jiye masa ciwon abin da take masa shi kansa bai san mai ya sa ba, illa iyaka ya san so ne, son da yake mata ne ya lullu e laifinta. "Kar ki ce haka SALIMAH ki tausaya mini, ba zan iya rayuwa ba sai da ke, da wane amon murya kike so na fa a miki ina son ki ki yarda? Da wane martani kike so in fahimtar da ke irin son ki da kaunarki da nake yi ki yarda? SALIMAH ni kaina ban ta a ji ko a labari akwai irin son da nake miki ba Allah ne shaidata bayan mahaifana ba na kaunar wata halitta sai ke. Da a ce an adam yana iya tsaga kirjinsa ya nuna so a yarda da shi da na bu e miki kirjina da kin duba cikin zuciyata ki ga yadda son ki ya cika zuciyata ko da ba za ki so ni ba idan kin gani za ki yarda da imbin makahon son da nake miki wallahi ba na ji, ba na gani, bana gane rashin ki masifa ne a wajena sai kin yi nesa da ni, na yarda na amince ki koma gidana ki mini duk azabar da za ki gasa mini na yarda ki mini fiye da abubuwan da kike mini, zan auki komai