Sashe 31
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mini kasuwa, bana jin akwai wani a namiji da yana ganin tsinanniyar yarinyar nan zai zo gare ni har ya iya furta mini kalmar so? Ga ta ha iya ga kyau ga addini ga nutsuwa ta fi ni komai gaskiya sai na tashi tsaye a kan yarinyar nan in ban lallashi ziciyata ba sai na kwa e mata kyakkyawar fuskar nan tata da asid ya one fuskar ta dawo abin tsoro" Amrah ta ce a zuciyarta tana jin tsanar HAWWA a ranta musamman da Baffa ya bata ku in sayayyar nan sai ta ki kenan yanzu ta zama tamkar kishiyarta za a ke musu abu tare bare ma da ta ji HAWWA tana cewa za ta saya irin hijabinta wato gasa ma za ta tsaya yi da ita. "Don ma dai mazan basa gabana ina kula su ne don nake tati e musu aljihu, ga wanda zuciyata can ta mutu a kansa wato kyakkyawan matashi wanda yake ji da lokaci son kowa in wanda bai samu ba ha a in na mallaki ABBAS a matsayin miji kuma na dace yana matu aunata to ni fa na kasa na sayar" Ta ce tana yin juyi a katifarta tare da kamo hotonsa wanda ta auke shi yana jingine a jikin banci ba tare da ya sani ba. "Yaushe ne zan furta maka kalmar so, kalmar nan da ta da e tana yawo da addabar zuciyata, son ka wanda na kamu da shi tun ban san mene ne so ba, ma yi matu ar ba inciki a shekaru biyar da suka wuce lokacin da sanarwar aurin aurenka ta same ni na yi ba in ciki na yi kuka na shiga damuwa ganin za ka auri wata ba ni ba sai dai yanzu ina cikin tsananin farin ciki jin ka rabu da matarka sai dai ba a nan gizo yake sa ar ba shin za ka so ni? Har ka yarda mu yi aure mu rayu a inuwa aya? A duk ranar da na furta kalmar so a gare ka kuma ka aminci sai na zubar da ruwa a asa na sunkuya na kafa bakina na shanye shi tas" Ta ce tana shafa hoton nasa tana jin wani shau i na soyayya tana sawa a ranta a wannan ga ar dole za ta yi iya yinta don ganin ta cim ma burinta muradinta ya tabbata na zama matar ABBAS. HAWWA a waje ta samu mashin in Yaya Usman ya ajiye shi, shi kuma yana can tsaye yana magana fa a-fa " ABBAS to ni na ce ka ba Baffa ku in cinikin jiyan a kan mai za ka bashi, ai ka san dai ni ne magajinsa a kafintocin nan kuma komai a hannuna yake mai ya sa kai ba za ka bayar da komai ba gare ni kai wa ka fi? Shegen shishshigi da neman wuri don Baffa yake ganin ri on amanarka dama kullum yana yabonka so dai kake ya auki matsayina ya baka to wallahi baka isa ba matsayina ya fi arfin takawar afarka" Ya ce yana haki wasu daga gefe suna ta bashi baki amma tamkar zuga shi suke. "Haba Usman mene ne na aga jikiyoyin wuyan ni fa ku in nan ba cin su na yi ba kuma ba nawa bane laifi ne don na ba Baffa, kuma ka saka ranka a inuwa ni ba zan ta a kar e matsayinka ba kana matsayin an mai wurin nan baki aya mu ai cin arzi i muka zo" "Uban waye da ya ce ka isa ka kar e matsayinaa munafukin banza da wofi... "Dakata! Usman wasa ya yi wasa amma ban da tsikarin uwar miji, ka mini komai ka ce mini komai amma ba zan auko cin mutunci ba na tsani a kirani munafuki domin ba na munafurci saboda munfukin ko a cikin wuta yana asan kafiri saboda girman munafurci don haka ka kiyaye bana son a kira ni munafuki ko a zagi iyayena saboda iyaye su ne gaba da komai iyaye su ne jigon kowa duk wanda ya rasa su ya yi kuka don haka na san muhimmancin su bana so a zagar mini su" "Sosai HAWWA ta ji abin da Yaya Usman ya yi wa wanda ya kira da suna ABBAS ya ta a mata zuciya, saboda bata ga laifin da ya yi ba kuma jiya a gabanta ta ga ya kawowa Baffa ku in ya ce ga cinikin amma Baffan ma bai kar a ba bata sani ba ko bayan ya fita ba ya bashi, yadda ABBAS in ya nuna iyayansa suna da muhimmanci abin ya burge ta sosai saboda ko ita a duniya ta i jinin a zage ta ko a wula anta mata iyaye tun suna raye bare yanzu da basa duniyar sai take jin abin ya ara shiga zuciyarta ya zauna daram! Sakarai ne zai kasa sanin muhimmancin iyaye, uwa ita take aukan ciki ta raina ta sha wahala, ya zo ta sha wuya a na uda har ta haihu ba a nan abin ya tsaya ba ta shayar ta ba a kulawa har su girma aiyuka uwa suna da yawa haka uba komai shi ne ciyarwa shayarwa tufatarwa aukan nauyin karatu duk mahaifi ne komai in babu sai dai a fa a masa, tabbas wanda bai san muhimmancin iyaye ba ko bai auke su bakin komai ba ya yi babbar asara. Cikin sanyin jiki ta fara taka afarta a hankali ta nufi wajensu, Yaya Usman bai lura da ita ba idanunsa sun rufe sai masifa yake shi ya tsani ABBAS ya ba Baffa ku i saboda ya fi so ku e su biyo ta hannunsa ya ci karensa babu babbaka ya ba Baffa abin da ya samu, shi kuma Baffa ba ya tuhumarsa ko da kuwa ku in bai kai yadda ya tsammata ba kasancewar Yaya Usman yana nunawa Baffa shi mutumin kirki ne don ya yarda da shi amma a bayan idanunsa shi kura ne lullu e da fatar akuya. Fuskar wanda aka kira da suna ABBAS ta kalla cikin sanyin zazza ar muryarta mai da in amo a kunnen mai sauraro ta ce "Ka yi hakuri" Ta fa a tana ha e hannuwanta biyu wuri guda, saboda yadda ta ga yana magana cikin nutsuwa da kuma nuna abin da aka fa a masa ya masa ciwo musamman zagin sai ta ji tamkar ita aka zaga sannan sai kuma da aka kira shi munafuki ya musanta hakan har yana nuna yamar munafurcin yana kuma ambata makomar munafukin sai ta ji ya burge ta tana son mutum wanda ya san darajar kansa a rayuwa. urrr ya ago wannan kyawawan fararen idanunsa masu kallo tamkar na soyayya ya zuba mata su tare da son gaskata cewa shi in take ba ha uri a bisa laifin da ba ita ta masa ba, shin mai ya ja hankalinta har ta so bada ha urin?. Yaya Usman kuwa maganarta ce ta ankarar da shi zuwanta wanda fitar furucin daga bakinta ya zuwa kunnuwansa sai ya ji tamkar an zuba masa dalma, wani turnu in kishi ya yi wa zuciyarsa dabaibaiyi, yana hasko nan gaba ka an za ta zama matarsa kuma mallakinsa tabbas ba zai so ba kuma ba zai lamunci ta yi wa wani a namiji magana ba bare har wani namijin ya mata. Yana da kishi matu a a nashi tsari da halayya tun yana arami ya i jinin su yi abu iri aya da wani sabo da kishi irin nasa bare kuma yanzu da ya girma ya mallaki hankalin kansa kishin ma a kan wacce yake muradin ta zama mata kuma uwar ansa. Wata irin tsanar ABBAS ce ta shiga zuciyarsa ta yi masauki, a ufule ya ago ya kalle ta ya ce "Wa kike ba ha uri a tsakaninmu" HAWWA da har lokacin hannuwanta suke a ha e ta lunshe kyawawan idanunta ta bu e a hankali ta ce "Haba Yaya da wannan nake mana ai kai ne ka masa laifi jifansa da ka yi da kalma marar da i, bayan laifinsa bai kai matakin hukuncin da ka auka ba wato zagi... "Ya ishe ki HAWWA, yaushe na zama sa'anki za har za ki nemi nuna mini abin da ya dace in yi... Fitowar Baffa daga gida ne ya dakatar da Yaya Usman daga dokin zuciyar da ya hau cikin iya kissa da wayincewa ya saki murmushi tare da dafa kafa ar ABBAS ya ce "Ina son ri on amanarka ABBAS baka yadda ka ci ko da wandala ba in har ta kasance ba mallakin ka ba ce ka cigaba da tsayuwa a kan turbarka lallai duk wanda hul a ta ha a ka da shi ba zai so ka su uce masa ba" Ya ce yana dariya har ha oransa suka bayyana. ABBAS ma murmushin arfin halin ya saki don inda sabo ma saba da halin Yaya Usman na nuna halin rashin kirki a bayan idon Baffa amma a gaban idanunsa babu wanda ya kai shi kirki da girmama mutanen da suke ashin su. Cikin halin dattako Baffa ya araso gabansu fuskarsa cike da alamar abin da ya gani ya faranta masa ya zo, mi a hannu ya yi ya dafa ABBAS da hannun dama hagun in kuma ya dafa Yaya Usman ya ce "Ha a ina alfahri da dukan ku, kamar yadda kake yabon ABBAS kai ma haka kake ana ha a na yi sa'a da samunku a matsayin jigon jingina wanda a zamanin nan ba kowa bane za ka ora shi a kan kasuwanci na harkar ku i kuma ya ri e amana ba tare da ya cuce ka, tabbad kuna yamatar cin haramun wanda haka ya dace kowane musulmi ya yi" Su duka murmushi suke daga ABBAS har Yaya Usman, ban da HAWWA da take tsaye sake da baki tana mamakin abin da Yaya Usman ya yi lokaci guda ya sawaya tamkar hawainiya daga tafiya irin ta osasshen zaki zuwa tafiyar hawainiya wato yana cikin fa a da tada jijiyoyin wuya sai kuma ya yi sanyi alau tamkar ara. Kallon fuskar ABBAS ta yi tana son gane wani abu wato dalilin da ya sa shi ma ya sakar da maganar ya goyawa Yaya Usman baya, wato ya bi yarima ake shan ki a maimakon ta ga ya cigaba da nuna