Sashe 14
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*ZARIYA* *Unguwar Gwalagwaji* Kwance take a kan tsohuwar tabarmar wacce ta shimfi a musu zannuwa guda biyu, SABEER wanda ya ora kansa a jikinta duk ya takura saboda fitsarin da ya yi an yalolon zanin da ta rufe su ta cire daga jikinta ta rufa masa, a haka bacci ya yi awon gaba da ita kasancewar ayyukan da ta yi ta gaji. Hajiya Rayyanatu wacce ta nufo akin nasu da sanyin safiya auke da ruwa a jug ta shigo akin tana jan wani tsaki tare da toshe hanci, ruwan ta aga ta sheke musu a jikinsu a gigice suka falka SABEER yana sakin kuka da sauri ta ja shi jikinta ta rungume shi tare da jijjiga shi alamar rarrashi duk da yake in da sabo ya ci a ce sun saba don kullum ruwan shi ne abin da ake tashin su da shi daga bacci sai dai hakan ya ki zama sabo kasancewar mai bacci ba ya son a zuba masa ruwa hakan yana zuwar wa mutum a bazata kuma duk wanda yake da ikon tsawatarwa kan cewa kar a zuba masa ruwa ko da ba a bacci bane zai tsawatar amma a inda yake da iko ba kamar su ba da basu da kata us maraici ne silar komai mutuwa mai yankan kauna da yanke jin da in duniya a lokacin da ba a zata ba, kuma ba a tsammata ba mai raba a da mahaifi ta musu shigar sauri ta yanke musu rayuwa da mahaifansu a lokacin da suka fi bukatarsu a lokacin da suka sakankance suna rayuwar da basu kawo rabuwa da juna ba. Sai dai shi tsari na an adam da ban yake tsarin ubangiji na da ban yake, a lokacin da kake lissafin sherakara goma za ka yi kaza kai baka san cewa saura minti goma ka bar duniyar ba Allah ya bar wa kansa sanin wannan ya oye shi ga an adam sai dai zama koyaushe cikin shirin da sakawa a rai cewa ko da yaushe mutuwa na iya riskarka shi zai sa ka yi duk wani abu wanda zai kusanta ka ga aljanna, ka nesanci wanda zai kai ka ya zuwa wuta!. "Ki tashi ki tafi ki ha u da an aiki kin zo kin kwanta gari har ya waye ko har yanzu dakikiyar kwakwalwarki tana miki tunanin rayuwarki ta baya ne? To nan ba da gidan ubanku bane gidan kanen ubanku ne, uban naku yana can cikin kasa a rufe" Hajiya Rayyanatu ta ce tana aika musu kallon mugun tsana. Kallon ta Hauwa'u( Hawwa) Ta yi tana jin zafin kalamanta bata san irin zafin da take ji ba idan aka sosa mata mikin mutuwar mahaifanta wanda mutuwa ta auke musu su a rana aya a lokaci guda ba tare da ciwon komai ba sai kaddara da karar kwana. "Ai Aunty Hawwa ta ce Ummie da Abbie za su bu e kasar su dawo mu koma gidanmu ko Aunty Hawwa" SABEER ya ce yana karkarwar sanyi. Kai kawai Hawwa ta gya a masa tausayinsu yana kara shiga zuciyarta har gwara ita yanzu shekarunta sha takwas, iyayanta sun rasu tana da shekara sha shida, shi kuma SABEER shekara bakwai lokacin yana an shekara biyar suka rasu amma kasancewarsa yaro mai wayo da rashin mantuwa har yanzu bai manta komai ba. "Kai dalla rufewa mutane baki uban waye ya ce maka idan an mutu ana dawowa duk wanda ya mutu ba zai ta a dawowa ba, su ma suna can sun tafi kenan" Da kuka ya fashe yana kifa kansa a kirjin Hawwa ita ma Hawwa hawayen take tana jin kukansa har kasan ranta tana kuma jin haushin maganganun Hajiya Rayyanatu wacce ta kasance matar kanin mahaifinsu. "Za su dawo mu koma gidanmu" Ya ce cikin kuka, Hajiyar ce ta karasa gabansu ta saka jug in hannunta ta kai masa bugu ai kuwa Hawwa ta saka hannu ta kare dukan da ta kawo ita aka same ta a hannu, ganin haka sa i Hajiyar ta juya akalar dukan zuwa gareta ta ranga a masa jug in a ka da karfi. Bata ce komai ba kuma bata yi yunkurin komai illa iyaka ta sunkuyar da kanta kasa hawaye suna malala daga idanunta tana tunanin ranar da za su bar gidan nan su fita daga ukubar da ake musu da gallazawa. "Idan kika kara minti biyar baki fito ba wallahi sai kin gwammace ki a da karatu shegiya mai farin fatar zabiya, wannan farin naki na maita ne gadon tsiya gayyar na ayya gayyar tsiya" Ta ce tana juyawa ta fita daga akin. Hannu SABEER ya saka yana share mata hawaye n. "Aunty Hawwa ki yi hakuri daga Ummie da Abie idan sun dawo za mu bar musu gidansu mu koma gidanmu ko? Inda muke kwana a saman bed, har Ummie take ce miki Hawwa in kara gani kin ce a akin SABEER za ki kwana shi akin naki dafawa za ki yi ki ci? Muke cin abinci mai da i direba ya kai mu makaranta ya dawo da mu Abie ya ka kaimu wurin wasa da gidan zoo" Ya ce har yana murmushi tunowa da ya yi da rayuwarsu lokacin iyayansu suna raye. Rungume shi ta yi tana tuno abin da ya ce Ummie tana cewa in har jiyo sautin maganar ta yi yadda take mata fa an cikin wasa saboda tsokana irin ta Hawwa sai ta je ta kwanta a akin SABEER yana tashi ya ganta a kan gadonsa tana bacci sai ya ringa kuka wai ta zo masa akin bayan fitsarin kwance ma yake. Da sauri ta tashi tana kama SABEER in suka fito suka nufi bayin wanda yake na an aikin gidan ne, dama a angaren an aiki aka basu aki. Ruwan umi ta kar a a wajen Baba Sadiya mai aiki dattijuwa mai sanin ya kamata sosai take tausaya wa yaran ganin yadda masu gidan suka mayar da su tamkar ba an zumunsu ba, har yau tana mamakin yadda duniya ta lalace wasu daga cikin mutanen cikinta suka auki duniyar tamkar matabbata, yadda suka auke ta wuyarta mutum ya mutu yanzu komai zai canja daga fari zuwa baki wani idanunsa ne mashi daga babu idanunsa shikenan komai an dainawa ansa dama na ganin ido ne ake. Wani ko a kwnce yake ba ya iya komai amma albarkacin numfashin da yake da idanunsa da suke kiftawa sai ki ga ansa basu tagayyara ba amma daga ranar da aka ce ya bar duniya sai komai ya sauya wani duk abin da yake maka na kyautatawa daga ranar ya daina wani ko magana mai da i ba zai kara maka ba. Wanka ta masa ta je Baba Sadiya ta lakuta mata man shafawa ta shafa masa ta saka masa kayan makaranta wanda makarantar gwamnati ce aka saka shi bayan gaba aya yaran gidan a makarantun ku i suke amma shi a makarantar gwamnati yake. Lokacin iyayansu suna raye Abie ne yake biyan ku in makarantar har an kanin mahaifin nasu, makaranta ce mai tsada da sai wane da wance ne suke, duka a makaranta aya suke kuma shi yake biya ba don kanin nasa bashi da hali ba sai don zumunci Allah, don hatta gidan kanin nasa shi ya gina shi ya bashi. Direban gidan Abie shi yake kai su makarantar tare ya akko su ya kai su gida sai ya wuce da su Hawwa gidansu. Amma su Abie suna mutuwa Alhaji Bukhari ya cire su daga makarantar ya mayar da su ta gwamnati kuma a kafa suke zuwa su dawo a kafa suna gani za a auki an gidan a mota su kuwa kafarsu ce take aiki haka Hawwa take goyon SABEER a bayanta idan ya gaji da yake makarantar da nisa da gidan, har ta karasa secondry scul dama tana aji hu u iyayan nasu suka rasu, yanzu kuma da ta kammala sai take raka SABEER in ta dawo in an tashi ta je ta taho da shi. Kasancewar dama ba sallah take ba, shi bayan ta shirya shi ta saka shi ya yi alwala ya yi sallah. A akin ta bar shi ta tafi kicin inda masu aikin suke hada-hadar ha a kayan karin kumallo, ha uwa ta yi da su suka cigaba da yi tare don tun da ta dawo gidan komai na aikace-aikacen da ita ake yi jin da inta aya Ummie ta koya mata girki da aikace-aikace, duk da kasancewar mahaifinta mai tarin dukiya amma Ummie bata bar su kara zube ba tarbiya da sanin ya kamata girmama na gaba. Duk da gatan da suke da shi amma tana fahimtar da su rayuwa. Sai da aka gama ha awa ta fara kwasa tana kai wa kan dinning in tana jerawa lokacin har takwas ta kusa ga shi tana so ta tafi kai SABEER makaranta kullum yana fa a mata in ya je class in su sai an masa bulalar makara kullum shi ne na karshen zuwa class, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba za a kai shi a mota ba sannan ita ba za a bar ta ta tafi ta raka shi da wuri ba, dole sai an yi karin kumallo an gama karin kumallon da ko a hannu basu isa an basu sun ci ba sai dai su ci abincin an aiki da yake na an aiki da ban na masu gida ma da ban. ."Wane shegen ne zai zuba abincin da kika gama jerawa za ki tafi Yaya Umar ya ce yana mata wani kallo" .."Ban gama kawo wa ba " Ta ce cikin muryarta mai sanyi. "Kai mene ne na tuna mata baka bari ta yi kuskuren jikinta ya fa a mata" Alhaji ya ce yana aika mata harara ya tsani yaran ba don yana so ya yi kakagida da sama da fa i da dukiyar da ubansu ya bari ba da babu dalilin da zai sa ya kar i rukonsu da ko za suke yawo suna bara ba zai rike su ba!. "Ai Baba yarinyar nan mugun taurin kai ne da ita wai jiya na dawo da dare na ce ta zo akina ta mini ta i wai taki har ni take fa awa wai babu kyau namiji da mace su ke e kamar dai wani sa on Allah na ce