Sashe 10
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
idan ta kwanta ko mene ne sai dai ABBAS ya hakura da tambaya saboda kar ya tashe ta sai ta yi bacci son ranta take tashi amma ga shi tun da farar safiya Umma za ta aga mata hankalo. Wani dukan ta sakar mata a kafa tana cewa. "Wallahi kar fa in tafi ki koma bacci, ki tashi gari ya waye tangararai ana jimawa masu siyan kokon za su fara zuwa" Ba don ta so ba ta tashi tana murtsuke ido ta fito tsakar gidan ta wanke fuskarta, kujera ta akko ta zauna tana iza wutar ga uban hayaki duk ya turnuke da yake iccen anye ne. Haka ta cigaba da fifitawa idanunta yana ruwa, ita rabon da ta fifita wuta ma ta manta tun yajin da ta yi ta zo gida sai ko idan ta zo gida Umma ta ce ta iza wuta, duk talaucin ABBAS da take gani amma da gawayi take girki bai ta a siyan ita ce ba, sai dai da sallar layya in ya saya ma kuwa shi yake suyar don cewa take ita bata son zuwa wurin hayaki. Sai da ta dama kokon ya sha iska ta masa gasara sannan Umma ta shigo lokacin har an fara shigowa siyan koko, ita ta zauna tana zuba musu kokon tana aura sugar, ita kuma Umma ta ora kasko ta fara soya kosan. Sai da kokon ya kare ta auki wanda ta zuba a karamin kofi ta sa sugar ta zuba kosan a plate, aki ta shiga tana ci. Bayan ta gama ta share gidan ta hau wanke-wanke wanda a gidanta duk da ba wasu kwanuka ba ne sai da ta matsawa ABBAS ya auka mata mai shara da wanke -wanke. Da yamma ta shirya ta yi wa Umma sallama a kan za ta je gidan EESHART. "Ni ban ji kuna waya ba ma tun da kika zo, ku da kun saba kamar saurayi da budurwa ko yaushe kuna waya" "Ba ta jin da i ne wayar ma bata fiya amfani da ita ba" SALIMAH ta samu kanta da sharara karya. "Subhanallah, Allah sawake ki ce ina mata sannu" Umma ta ce tana jimantawa. Da to ta amsa ta fito ta kama hanyar gidan EESHART a kafa ga shi da nisa sai dai bata da ku in hawa napep kuma ba ta son tambayar Umma don yanzu za ta fara mata lissafi, kuma ma da ta san bata da ku i ai sai ta bata ba sai ta tambaya ba tun da jiyan ma ta san da ta zo a wajenta ta kar i ku in napep in. Tun da take tafiya ake mata magana amma sai ta ce tana da aure ganin bata gama idda ba kuma ma dai masu tsayar da ita in dai dama a mota suke tsayawa ita kuma duka motocin burinta ya fi karfin su, dama da a ce ta samu wanda ya mallaki tsadaddiyar mota da ta sanar da shi auranta ya mutu sai ta bashi lambar wayarta idan ta yi idda sai ya shiga sahu. A gajiye tikis ta karasa gidan EESHART saboda sanin da da mai gadin ya yi bata wani sha wahala wajen shiga gidan ba. ar aikin EESHART in ce ta mata iso zuwa falon ta kawo mata lemo da ruwa da kofi, bayan ta sanar da EESHART in zuwan SALIMAH. Shiru-shiru tana zaune sama da minti ashirin amma babu alamar EESHART in za ta fito. "Kin ce mata ni ce kuwa?" SALIMAH ta tambayi ar aikin tana kallonta. ."Eh na fa a mata" "Ko wani abun take yi?" "A kwance take tana danna waya" Sosai mamaki ya cika SALIMAH sai ta ma rasa wane kalar tunani za ta yi, tana ta tunanin manufar kawar tata amma bata gane komai ba. "Je ki kara tuna mata ce ina jiranta" Ta kara fa a mata ganin zamanta ma wajen sau hu u ta kira ta amma bata auka ba. Da to ta amsa mata ta koma akin sai ga ta ta fito jikinta sanyi kalau, da alama amsar da aka bata ce bata mata da i ba da alama ma ko koro ta EESHART in ta yi amma kuma sai ta kirkiri murmushin yake ta ce mata tana zuwa ta fita daga falon. Sai da aka auki kimanin minti biyar sai ga EESHART in ta fito sanye take cikin dakakkiyar shadda da alama ma yau ta fara saka shaddar ta sha aukin ankwali ta fito tana wani takun kasaita. Ko irin murnar da take nunawa idan ta zo gidanta yau bata nuna ba, zama ta yi tana mata magana ba yabo ba fallasa. "Haba EESHART wai mai yake damunki ne, tun jiya nake miki magana a whtsapp amma shiru har a group na sanar miki na ajiye miki sako amma baki bu e ba bare ki mini replay". "Ayya kin ga mantawa na yi ya kike ina Umma, don ba a ce miki ina mijinki ABBAS ba tun da yanzu bazawara ce ke baki da aure" Sasai ta yi mamakin kalamanta jin kamar ma har da gori take mata wai ta zama bazawara duk da ba son ABBAS take ba amma sai ta ji wani iri wani banbarakwai wai namiji da suna hajara. "Haba EESHART mu da dama burinmu kenan samun sakin to don ya sake ni na zama bazawara ai ba wani aibu bane, ba ma wannan ba duk kiran da na miki yanzu amma baki aga ba zamana a nan ma kusan minti talatin amma kin yi atan dabo a cikin gidan" "Ayya sorry fa ina can tare da baby nah ya saka ina masa tausa, kin san matar aure" Ta ce tana mata wani kallo mai ha e da murmushin da ta kasa gane inda ya dosa ko dalilin yin sa. an jim ka an ta yi tana nazarin maganganunta, da kuma maganganun ar aikin EESHART in da ta ce tana kwance tana danna waya kuma ita kuma ta ce tana wurin miji har da fa a mata abin da take yi a wajen miji. "Kai kawata kina wuta wallahi" Ta ce tana dariya don kawar da maganar da EESHART in ta yi da wacce ar aikin ta yi don kar ta ba kanta wahala, tun da ma ba daga akin mijin ta fito ba. "Ke ko" Ta ce tana an darawa. "Wai ni ko maganar sakin da aka yi mini jiya baki mini ba, kuma ko ki tuntu e ni" "Ki mini uzuri abubuwa ne suka sha min... "Aysha wai mai ya sa bakya jin magana ne, ba na ce in na ajiye abu a daina canja mini waje ba? amma saboda raini sai an ta a" Mijin EESHART Alhaji Yusuf da ya sakko daga saman bene bai gama sakkowa ba ya fa a cikin hargowa. an diriricewa ta yi saboda ganin SALIMAH tun da bata fiya zuwa gidan idan mijinta yana nan ba idan kuma ta same shi ma to wata rana har ta tafi bai fito ba. Maimakon ta bashi amsa jiki yana rawa kamar yadda ta saba, sai ta tashi cikin kissa da kisisina tana son ta tabbatarwa SALIMAH irin abubuwan da take fa a mata na tattalinta da mijin nata yake yi, don tana nuna cewa ita ta ha a komai ga miji mai ku i ga kulawar miji. Tana an wani murmusawa ta fara hawa step in shi kuma gaba aya ya kufula da abin da ta yi saboda dama ransa a ace karuwarsa ta gama masa rashin mutunci kuma ya je aukan agogonsa ya ga agogunan basa lokar agogunan. "Baby n... Maganar tata ta katse ne sanadin marin da ya auke ta da shi, a fusace ya shiga nuna ta da yatsa. "Mahaukaciyar banza da wofi, ina miki magana kika watsa yin maganata kamar wani sa'anki" Ya ce a fusace yana nuna ta da yatsa. Sosai abin ya ba wa SALIMAH mamaki sannan ta shiga ru ani ganin marin da aka auke da kawarta ba da wani kwakkwaran dalili ba, sannan aka bi ta da bakaken maganganu. A take maganganun da BASEERA ta mata jiya suka fa o mata, ta shiga jimanta wa a ranta ashe dai wasu masu ku in suna shuka rashin mutunci, tun da ga shi dai EESHART in bata rasa komai ba na morewar rayuwa ita za ta tabbatar da hakan don ko cima sai abin da take so take ci haka za ta tura mata hoton abinci kala-kala sannan suturarta ma in ka gani tamkar za ta bu e shago komai wadatacce amma kuma ga wani abu da ban wanda iya zamansu da shakuwarsu da EESHART bata ta a fa a mata hakan ba, sai ta nuna bata da matsalar komai. Yanayin yadda ta yi lokacin da ya mare ta in alamu sun nuna cewar ba wannan bane karo na farko. Ita kuwa ABBAS in ban da jiya ko yatsa bai ta a kaiwa jikinta ba, jiyan ma ta san tsinken hana haihuwar da ta saka ne ya kona masa rai tun da ta san yadda yake da son yara, sai kuma maganganun da ta fusata shi da su amma in ban da wannan tsawon shekara biyar ABBAS ko harararta bai ta a yi ba duk abin ta masa shanyewa yake ya nuna komai ba komai bane. EESHART kuwa dama ta saba idan da sabo sai dai yau bata ji da in hakan ba da aka mata a gaban SALIMAH shi dama mijin nata babu abin da ya dame shi a gaban an aiki na sai ya kai mata hannu shi dama wuyarta abu ya bashi haushi yanzu zai auke mutum da mari. "Ka yi hakuri Alhaji aya lokar na saka maka" Ta ce cikin sanyin murya idanunta yana cikowa da kwallar zafin marin. "Hakurinki na banza da wofi, uban wa ya ce ki canja mini ma'ajji? Sakarar banza da wofi" Ya ce yana doka tsaki ya haye saman ya bar ta rike da kumatu. Jiki ba kwari ta dawo tana wayancewa, duk da ta ji haushi kuma ya tsinka ta amma hakan ba zai sa ta rasa abin fa a ba. " SALIMAH kin ga baby ko da alama ransa ace yake yau amma ba komai na san ana jimawa zai durkusa ya bani hakuri" Ta ce tana sakin murmushin yake tare