← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 43

Sashe 20

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaishe da aisha" Hajiya Rayyanatu ta ce rai a matukar ace. "Na ji kuma zan fita muku a gida amma ina so ku sani zalunci ba abu ne mai kyau ba, kuma cin dukiyar maraya haramun ne domin Allah ma aukaki ya fa a a littafinsa mai tsarki cewa, kada ku ci dukiyar maraya da zalunci, a wani wajen kuma ya ce hakika masu cin dukiyar maraya da zalunci ba komai suke ci ba a cikin su, illa wuta, kuma za su shiga cikin wutar sa'ira. Domin na sam tabbas kun hau dukiyar marayu kun yi kaka gida, saboda dukiyar da mahaifansu suka bari basu ba hatta a da jikokinsu sai sun mora, amma tun ba a je ko ina ba tun ana shekara biyu da mutuwarsu ga shi nan suturar kirki ta gagari ansu suna rayuwa kaskantacciya, yanzu da iyayansu za su dawo duniya mai za ku ce musu? Tabbas duniya ta zo karshe zumunci ya ki da i amana ta yi karanci amma a juriya zuwa tafi wata rana tulu zai fashe! Na bar ku lafiya" Ya ce yana juyawa ya fice. Daga Baban har Hajiyar ransu ne ya yi matukar aci don kalamnsa basu shige su ba illa haushin sa da takaici. Haushi ne ya sa Hajiya Rayyanatu aga kafa ta ham are Umar da ya yi shame-shame don asara yana sakin munshari. Jin an masa kafa ya tashi zaune a ki ime yana rarraba idanu kamar shege a rabon gado. [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RU IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 9 "Sai ka tashi malalacin banza gobe aurin aurenka amma maganar auren kana yashe kamar kayan wanki" Ta ce tana harararsa ganin ya saki wata uwar hamma. "To a kai ni akin amaryar tawa mana" Ya ce yana kallonta da lunsassun bugaggun idanunsa. "Hajiya ki kyale wannan ba a hayyacinsa yake ba, da yana cikin hankalinsa da yanzu yana cikin farin cikin murnar auren nan" "To Alhaji" "Yanzu dai ita wannan ki binciko mata kaya a cikin kayan Lawisa wanda za ta saka goben' "Wallahi ba za a auko a kayanta ba wannan yarinyar da ta tsani a ta a mata komai nata, kana gani yanzu kamar ita ce uwata ko raga mini bata yi ina fa a tana fa "To ki akko mata marar inkawa a kayanki sai a bada inki" "Nawa ai sun fi karfin ajinta amma zan san yadda za a yi" "Don Allah Baba ka taimaka mini ni bana son a mini aure karatu nake so na yi" HAWWA ta ce tana hawaye. "Matsayinki na mai rangwamen gata wato marainiya, har kina da za in kan ki? To ai karatun secondry ma sa kika yi ya ishe ki son ko yo zurfi a karatu shi mijinki da bai san ko bihim ba ki zo kina goranta masa to ba za ta sa u ba bindiga a ruwa" Cewar Baba. Sai da suka gama fa ar abin da za su fa a suka ce ta tafi, dama ba shawarar ta ake nema ba umarni ne, haka ta tashi ta fito ta nufi akin Baba Sadiya tana zuwa Baba da take linke kaya ta je ta fa a jikinta tare da fashewa da kuka sosai Baba ta ji abin ya ta a ta lallashinta ta shiga yi har sai da kukan ya tsagaita, sannan Babar ta shiga tambayarta dalilin kukan nata, nan ta shiga labarta mata abin da ya faru, sosai ta tausaya mata kuma take jinjina rashin imani da tausayi na mutanen gidan uwa uba rashin amana. "Baba ki bani wannan zoben da na baki ajiya" "Hauwa'u shi ka ai fa ya rage miki mai ya za ki kar a suna ganinsa a hannunki za su kwace" "Guduwa zan yi Baba, barin gidan nan zan yi ba zan zauna a rusa mini burina na karatun likita ba, burina na taimakawa al'umma mararsa lafiya, burin da tun ban san inda yake mini ciwo ba yake damfare a zuciyata" "Haba Hauwa'u ina za ki dosa a halin yanzu?" "Kaduna zan je Baba wurin yayan Ummiena da aka hana ya tafi da ni, kuma da kunnena na ta a jin Hajiya tana waya tana cewa wurin malamai ta je aka masa mantau, wai ba zai kara tunowa da mu ba bare har ya zo neman mu, sai dai makarin abun shi ne idan ya yi ido hu u da mu tun da ta san mu ba za su bari mu je gare shi ba" Ta ce cikin sanyin murya sosai Baba ta jimanta maganar tana kallon HAWWA sannan tana jinjina rashin imani na su Hajiya Rayyanatu. "Kar ki damu zan baki ko ni ba zan so ki auri wannan yaron ba da shi kansa bai san kansa ba, amma wani hanzari ba gudu ba ta yaya za ku bar gidan nan bayan gobe ne aurin auren kar ki tafi da igiya a kan ki' "A daren yau za mu gudu Baba, ba zan bari igiyar aurensa ta ratayu a wuyana ba, ni dai ki taimaka mini Baba ki je kasuwa ki sayar mini da zoben ki bani ku in mu samu ku in mota " Shiri Baba Sadiya ta yi tana nazarin maganar tana son gano matsalar da za a iya samu idan aka aikata hakan ko aka san da saka hannunta a guduwar yaran sai dai irin halaccin da mahaifiyarsu ta mata da kirkin ta gare ta ba za ta bar anta su tozarta ba daidai gwargwado za ta yi iya yinta kuma ta shirya tunkarar kowane alubale a kan hakan. "Don Allah Baba" Muryar HAWWA ta katse mata tunanin. "Hauwa'u dama zan je kasuwa siyayya da Hajiya ta aike ni sai na tafi da zoben na sayar miki na kawo miki ku in" Sosai HAWWA ta shiga mata godiya domin har ta hango sun bar gidan ta tsallake auren mashayi. akin nasu ta koma ta samu SABEER zaune ya jingina da bango yana gyangya i a zaune ga rigar da take inke asa nan lokacin da aka kira ta a kan cinyarsa. Kai ta jijjiga cike da tausayin kansu da tausayin kaninta kasancewarsa karami wanda maraici ya masa dirar mikiya tabbas mutuwa tana da yankan kauna in ba haka ba mai zai raba uwa da a ko kuma mai zai raba iyaye da a sai mutuwa, domin mutuwa ba ta duban girma ko kankantar wanda za ta raba da iyayan. A hankali ta samu wuri ta zauna a kusa da shi, tare da janyo shi ta ora shi a kan cinyarta, tana karewa fuskarsa kallo tana tuno yadda mahaifansu suke kaunarsu tare da lulawa duniyar tunanin ranar da ba za ta ta a mantawa a rayuwarta ba, ranar da ya kasance rubutu a kan dutse wanda ba zai ta a goguwa ba, ba rubutu a kan ruwa ba wanda zai gogu. A ranar wata juma'a da yamma, HAWWA ta ce tana son zuwa gidan kawarta ziyarar juma'a ai kuwa SABEER ya ce sai ya bi ta, sai da Ummie ta saka baki sannan ta yarda za su tafi tare, lokacin da za su fita Ummie tana cikin kicin tana girki, a hanyar fita suka ha u da Abbie zai shigo gidan. "Sai ina kuma an Ummie?" Ya tambaye su yana murmushi mai nuna so da kaunar an nasa. "Abbie Aunty HAWWA ce za ta je gidan kawarta ziyara shi ne zan raka ta" SABEER ya ce yana rungume Abbie. "To kai da ba kawarka ba ya za a yi ka je?" Ya ce yana dariya saboda ya san yanzu HAWWA za ta ce wani abu. "Sai da na ce fa ba zai bini ba amma Ummie ta ce sai ya bini" Ta ce tana kumbura baki. "To ke da an uwanki ai sai ku je dama ai na ga tare kuke uzurinku ko my HAWWA" Ya ce yana kama hannunta. "Ai ni ma yawo nake son zuwa tun da yau babu islamiya ga shi na saka babbar riga da hula" Ya ce yana yi wa HAWWA gwalo. Sai da ya lalla ata sannan ya kama hannunsu aya a hannunsa na dama aya a hagu shi yana tsakiya, ya raka su har wurin mota suka za i wacce za su fita suka shiga direba ya ja suna agawa Abbie hannu yana aga musu har aka fita da su daga get in sannan ya juya ya nufi cikin gidan. Basu san mai ya faru ba sai dab da magriba direba ya zo a ki ime ya ce su zo su tafi gida in ji Ummie sosai HAWWA ta yi mamaki don ta ce za ta kira shi a waya in sun gama amma kuma ga shi bata kira shi ba ya zo kuma ga shi duk ta gan shi a rikice, ko da ta tambaye shi dalilin rashin nutsuwarsa sai ya ce mata waya aka masa daga garinsu mahaifiyarsa ba lafiya. Ko da ya akko su maimakon ya nufi gidansu sai ta ga ya nufi gidan kanin mahaifinta, da ta tambaye shi sai ya ce wai Ammie ce ta ce ya kar o mata sako. Tun kan su karaso gidan ta hangi yadda jama'a suka yi dandazo a kofar gidan, sosai ta ji fa uwar gaba ganin mutanen babu alama ta abin farin ciki ko abu mai da i ne ya tara su, sannan ta san dai da aurin aure ne ko makamancinsa da za ta sani saboda shakuwar Abbie da ta kaninsa Baba ta wuce a ce an yi wani taro ko da kuwa na wani ne da ban ba tare da Abbie ya sani ba. Ta shiga tashin hankali da ta gane mutuwa aka yi tun da lokacin Baba da Hajiya Rayyanatu so da kauna marar algus suke nuna musu kamar su ha iye su. Don bata ta a kawowa cewa mahaifanta bane. Tashin hankalin da
Chapter 20 · 0% Book details