← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 43

Sashe 32

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

acin rai kamar yadda yake sai ya sakar shi ma ya nuna babu abin da yake f aruwa kuma hatta sauran mutanen da suke wajen babu wanda ya tofa wani abu makamancin wannan. Suna ha a ido sai ta ga ya fa a murmushinsa tare da an rausayar da kai yana son nuna mata hakan ba komai bane, ganin dai tana ta masa kallon mamaki sai ya kanne mata ido aya da sauri ta juya har tana har ewa ta bar wajen wanda hakan sai da ya sa dariya ta kusa su ucewa ABBAS in ganin ta tsorata kuma ta auki kashe idon da ya yi a matsayin wani abu wanda shi kuma ya yi hakan ne don ya ara nuna mata komai normal kar ta damu. "Hauwa'u" Baffa ya kira ta. "Na'am Baffa " Ta ce tana juyowa duk ta duburburce. "Ku je ku dawo ko SABEER yana can yana jiran dawowarku ya matsu a masa wanka" Da to ta amsa sakin kafa ar su ABBAS in Baffan ya yi Yaya Usman yana murmushi ya juya ya nufi wajen machine in, Baffa wajen kujerarsa ya wuce ya zauna ABBAS kuma ya cigaba da buga hannun drower a jiki. Yaya Usman sai da ya tada machine in HAWWA ta hau suka zo giftawa ta gaban ABBAS wani kallo Yaya Usman ya aika masa irin na da ni kake zancen. ABBAS kuwa kallo aya ya musu ya auke kansa ya cigaba da abin da yake amma ko ba komai ya ji da in abin da HAWWA ta masa a alla dai gata yarinya amma tunaninta ya fi na Yaya Usman in ta fi shi hangen nesa da sanin darajar an adam, karon farko da ya ji wata mace ta burge shi bayan SALIMAH amma ba da so ba, burgewa kawai. *SALIMAH* Tun karon farko da ta farka babu wani bacci da ya yi nasarar aukanta ko da kuwa arawo ne, sa a da warwara su ne abin da ta fi yi ta rasa wane za ta auka daga cikin sa ar jakin da zuciyarta take mata. Ga shi kiran duniyar nan ta yi wa Alhaji Tahir amma wayarsa a kashe, ga shi da tsakar daren nan bata so ta kira kowa haka ta auki na annabawa har aka faramkiran assalatu, cike da takaici ta sakko daga kan gadon tana duba iya ha uwa da tsaruwarsa ha e da lallausan bedsheet da ta yi oder wajen Maman Afrah amma a ce wai ita ka ai ta kwana a kan gadon babu ango? Ita in ma da ta kwana a kai babu wani bacci mai da i tunani bai bar zuciyarta ta huta ba. Wucewa ta zo yi ta gaban madubi kallon kanta ya yi a ciki sai da ta ba kanta da kanta tausayi yadda fuskarta ta sha make up amma duk ya ca e a banza ango bai gani ba aurin ankwalin da mai aurin ankwali ta ata lokaci wajen tsantsara mata shi amma ya tashi a banzar bazara, a ce wai ko kayan bacci bata saka ba da leshin zuwa gidan mijin ta kwana ba ma wannan ba a ce tana amarya amma ko kazar amarci babu haka ta kwana da yunwa. "To ina angon ma mai kawo kazar bare ita kazar?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata tambayar da ita kanta bata san amsarta ba. Ganin eye lashes in guda aya ya far ale ya mayar da ita kamar aljana haka ta saka hannu ta cisge ko zafin cirewa bata ji ba ta yi cilli da shi ta bar gaban madubin saboda kallon kanta a madubi yana ara ago mata da acin rai. Tana tafiya a tangamememan falonta tana kallon ha uwa da kayan alatun da aka kashe kamar ba gobe, tunanin ranar farkonta a gidan ABBAS ya fa o mata, a ranar sai da awayenta suka yanka masa ku i mai tsoka ya bayar matsayin siyan baki duk da talaucinsa ya shigo da kaza da lemuka daidai arfinsa yana ta nan -nan da ita yana lallashinta ba ya ma ganin kyara da nuna masa tsanar da take yi, amma sai ga shi yau an mata wula anci iya wula anci am bar ta babu ango abin takaicin ma bai ce mata ga uzurinsa ba sai ka ce wata marar galihu ai an magana suka ce wai amarya ko ta kyankyaso ce ana ri in ta. Da wannan takaicin ta arasa bayin tana ganin yadda ya gaji da ha uwa alwala ta yi ta fito ta yi sallah tana jin ugin cikinta ha e da ciwon marar magungunan da ta bankamawa kanta. Hannu ta sanya ta dafe goshinta tana jin tamkar ta rushe da kuka amma sai ta dake ta tashi ta bar sallayar a wajen ko arzi in linkewa bata samu ba. Ganin shida da rabi sai ta nufi saman bene ta je windown ta tsaya tana ara arewa gidan kallo, tabbas gida ya amsa sunansa gida musamman yauzu da yake da safiya ce ba dare ba sai ta ga ta fi arewa komai kallo yadda ya kamata. A yadda gidan yake bata ta a zato za ta zama aya daga cikin wanda za su zauna a matsayin matar gidan ba ita ko a ar aiki bata ta a zaton zuwa gida irin wannan ba amma sai ga ta a matsayin matar gidan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana sakin labulen ta bar wajen, har ta juya za ta tafi ta dawo ta ara ta a labulen tana ara jin wari da nagartarsa . 'Lallai labulen nan yana da inganci tabbas maman afrah kayanta suna da kyau' Ta ce a zuciyarta tana barin wajen ta shiga arewa ko ina kallo ganin bata gane wasu abubuwan saboda yunwa sai ta sakko asa tana tunanin inda za ta samu abinci, ofar da take tunanin nan ne kicin ta nufa ta shiga komai tamkar a asashen etare murmushi ta saki ta fito ta nufi inda take tunanin nan ne a matsayin store tana bu ewa ta ga kayan abinci lodi guda katan in indomie ta bu e ta akko guda biyu ta fito ta dawo kicin ta kunna gas ta ora ruwa yana tafasa ta zuba indomie in, haka ta dafa ta da gishirin ta ta juye a plate. Har za ta akki wai ta soya sai ta ji tana jin jiri ba za ta iya soyawa ba haka ta kashe gas in ta fito daga kicin in a falo ta zauna a asan capet ko kan dining bata yi tunanin hawa ba saboda yunwa uwa uba babu ango bare ake bata a baki ita ma tana mayar da martani. Har sha aya a safe amma babu ango babu dalilinsa kuma har lokacin ta kira duka layilansa a kashe hatta whatsappa ma da ta duba shi ba ya hawa, ita kuma bata son fa awa kowa a mata dariya Umma ta so fa awa amma kuma ta kasa saboda bata son saka mahaifiyarta a damuwa tun da ita ka ai ta rage mata. Saboda ta san duk wanda ya ji abin zai ji wani bambarakwai. Kiran Ummar ta yi don su gaisa ringin aya biyu Umma ta aga cike da zumu "SALIMAH amarya" Ta ce bakinta har kunne tana samun wuri ta zauna saboda a yi maganar a nutse ta san akwai labarin yadda ta ga gidan nata. "Na'am Umma ina kwana" "Lafiya alau ya kwana ba unci" "Alhamdulillahi" "Oh kuma maimakon ki bu e baki tiryan-tiryan ki hau bani labarin gidan an gayu sai kike wani jan aji SALIMAH ko angon bai fita ba dama ai na san yanzu ba kasafai zai ke fita ba shi da ya ajiye amarya, ai jiya an kai amarya har sai da na gaji da labarin yadda ake fa a mini gida ya awatu" Umma ta ce tana dariya. "Umma ai abin sai wanda ya gani" Ta ce cikin arfin hali don ka an kuka ya wace mata gani ita angon ma ko eyarsa bata gani ba. Nan dau suka ta a hira suka yi sallama ta yi jigum bata son fa awa kowa. Wasa-wasa har kwana biyu babu ango kuma babu wanda ya zo ya ce mata wani abu daga cikin kishiyoyin nata tana so ta je ta tambaye su ko ina mai gidan amma rana tsoron raini kuma hakan ma tamkar zubar da ajinta ne a ce tana amarya bata san inda ango yake ba sai ta je ta tambayi kishiyoyi. Sawunta biyu wajen mai gadi amma yana tabbatar mata cewa tun ranar aurin auren Alhajin bai zo gida ba. Haka za ta koma jiki babu wari a kwana na uku ne ta dokawa RUKY kira ta ce ta zo tana son ganinta da yamma kuwa sai ga ta ta zo, amma sai ta kasa fa a mata ganin tana ta yaba kyan da ta ara amma ta ce ta ga ta an rame amma hakan ba ya rasa nasaba da shan amarci da ake yi. "Kai SALIMAH kin samu duniya saura iyama kai Allah ya saka mu a damshinku" Ta ce tana kai lomar jalof in taliya. Murmushin ya e da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce "Abin ba a cewa komai" "Wai ya kyan magungunan na da kika babbaka?" "Suna da mugun kyau kuwa" Ta samu kanta da kwararo arta tun da ita mijin ma bata gani ba bare ta tabbatar da kyan magungunan. "Kai ai kuwa in zan yi aure irin su zan saya" "Ai kuwa" Ta ce tana dam e baki jin mararta ta mur a mata. Hannu ta kai ta dafe wajen tana yamutsa fuska, ta san tarin kwamacalar magungunan da ta sha ne suke tambayarta. "Inyeee amarsu ko dai har ango ya yi ajiye ne? In k,uma priod ne zai zo gaskiya kar ya zo ya kawo cikas ana tsaka da cin duniya da tsinken tsire" Ta ce tana aga ruwan roba ta kwankwa Murmushi kawai ta yi. "Ai dai kin cire inplan in nan shi ya sa wata ila ciki ne ya shiga, kin san ai dama an ce inplan wankin mara yake shi ya sa ana cire shi ake samun ciki" Ta ce tana tuno ranar da ta raka ta asibiti aka cire mata saboda kar ta haihuwa a gidan ABBAS
Chapter 32 · 0% Book details