Sashe 40
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*HAWWA* Rayuwa ta yi musu da i hankali ya kwanta, SABEER an sanya shi a makarantar boko da islamiya private school Baffa ya saka shi sai dai ba wata mai tsada ba dai dai arfinsa amma makarantar tana da kyau sosai, Yaya Usman yake kai shi yana akko shi. HAWWA tun da Baba Sadiya ta sako mata takardunta a mota aka kawo ita ma aka sama mata tata makarantar ita mai napep yake kai ta arfe bakwai da rabi ya dawo da ita arfe biyu da rabi ita ma private ce ta mayar da hankali don ganin burinta na zama ma'aikaciyar jinya ya cika. Yau ma kamar kullum ta tashi ta yi shirinta tsaf bayan ta ci abinci. Wayarta ta auka irar infinix da Baffa ya saya mata ganin bakwai da minti ashirin da biyar ta fito daga akin lokacin Amrah tana ta sha ar bacci ko karyawa bata yi ba da yake iya takardun ta na secondry basu yi kyau ba kuma ta gyara ma amma duk bata ci ba kasancewar bata da mayar da hankali kuma ma Baffa ne mai matsa mata a kan karatun ita a nata burin ta fi son a yi mata aure amma bata son wani karatu ko secondry in ma dakyar ta arasa. "Malamar asibiti mai tabarau" Baffa ya ce yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa. "Ni dai ba za take mini allura ba Baffa bata iya ba fa kar a je in zama gurgu" SABEER ya ce yana saka littafi da pencil insa a jakarsa da ya gama home work. "To ban da abinka SABEER ai koya za ta yi, a makarantar ake koya wa ko su wanda ka ga suna allurar ai karatu ne da suka yi ya sa suka iya babu wanda aka haifa da iyawa" Baffa ya ce yana dafa kansa. "Ni dai soja nake son zama Baffa, in aka bani bindiga in harbe Baba Bukhari da Hajiya da Yaya Umar da Aunty Lawisa" "Ikon Allah kai dama don ka harbe mutane za ka zama soja?" Goggo ta tambaye shi. "Eh da lokacin kafin su Ummiena su mutu lawyer nake ce mata zan zama in na girma, amma yanzu na fasa soja zan zama" "To mai ya sa kake so ka harbe su iyayanka ne da an uwanka" Baffa ya fa "Bama jin da i a gidansu fa Baffa kayanmu a yage kamar mu ne almajirai, suke ta saka Aunty HAWWA aiki wata rana su mare ta kuma basa bamu abincin da suke ci, ga shi mu tafi school a afa ga nisa in na gaji Aunty ta goye ni kuma fa akwai motoci masu yawa a gidan amma mu ba a barmu mu hau" Ya arasa fa a kamar zai yi kuka. Kallon kallo aka shiga yi da Baffa da Goggo suna jinjina walwar yaro da bata mantuwa ko ka masa alheri ko sa anin haka yana sane da kai. "Ka yi ha uri ka ji yaron kirki yanzu ba ga shi ka bar gidan ba Allah yana son masu ha uri da masu yafiya" Baffa ya ce yana rataya masa jakarsa a bayansa tare da shafa kansa. Shiru ya yi bai yi magana ba. "SABEER zo mu tafi" Yaya Usman da ya shigo ya ce. Yanzu ya sakarwa SABEER sosai yake jansa a jiki don ya ara samun fili a zuciyar HAWWA da zai gina soyayyarsa. Yana aga musu hannu suka fita. Ita ma sallama ta musu ta fita don ta san yanzu mai napep inta ya zo. Sanye take cikin riga da wandon farare tass babu sirki a jiki, rigar tana da an tsayi iyakarta cinyarta sai aramin hijabi da bai kai cibiyarta ba, afarta cikin farar socks da ba afa ciki, jakarta ba a rataye a bayanta sai wayarta a hannunta. Tun bayan fitowar su SABEER yake kallon ofar yana jiran fitowarta bai san mai ya sa ba kuma bai san dalili ba yarinyar tana matu ar birge shi halayenta kyawawa ladabi da biyayyarta uwa uba girmama ta gaba da ita ya jima bai ga mai halayya da sanyin hali irinta ba. Sautin ira'ar karatun ta da ya ji ranar da Baffa ya bashi kaya ya kai cikin gidan, sosai ya ji da in karatun tana ba kowane harafi ha insa, tun daga ranar ya ji ya bata matsayi na musamman, tun daga ranar ya ji yana son ganinta wanna dalilin ya sa yake yin sakkon zuwa wajen aiki don ya sanyata a idanunsa, saboda sai ya ji idanunsa sun kasa jure jiran har sai ta dawo daga school zai ganta, idan ya koma gida tunaninta ya yi ta yi masa kai kawo a zuciya. Fitowarta daga gidan ne ya tsananta bugun zuciyarsa ya aru dakyar ya saisaita kansa yana an satar kallonta farin siririn gilashin da ta sanya ya awata fuskarta tare da ara bayyana dogon hamcinta da yake kwance a kan kyakkyawar doguwar fuskarta. Ko ka an bata lura da shi ba, hankalinta ya yi school bata son malamin da zai shiga da safen nan ya hana ta shiga kawai haka yake yi idan har ya riga ka shiga da minti biyu to ba za ka shiga ba. Ta yi mamakin ganin mai napep in bai zo shi da kullum a wajen take samun sa, lambarsa ta binciko a cikin wayarta ta shiga doka masa kira sai dai a kashe wayar, fuska ta marairaice tamkar za ta yi kuka, hakan da ta yi sai da ABBAS da yake dakon kallonta ya ji abin ya daki zuciyarsa, da a ce za a masa tambayar waye baya son ya gani cikin damuwa to bayan Mamarsa HAWWA zai ce, amma shi bai yarda wai so bane tun da ya yi ittifa in ya daina soyayya daga kan SALIMAH ba zai ara son wata mace ba da sunan soyayya wannan yanayi da alamomin da suke farmakar zuciyarsa game da HAWWA ya aryata zuciyarsa da kuma FAROUQ ya ce kawai kyawawan halayenta ne kawai suke birge shi har yake jin ta tamkar anwarsa. Yanzu idan suka zauna da FROUQ ba shi da magana sai ta HAWWA ta gaishe ni da safe da yamma da za ta je islamiyya ma ta gaishe ni ta yi kaza ta yi kaza amma in ya ce ya kamu da sonta sai ya ce ba haka bane. Kallonta yake har ba ya son iftawa, ganin narai-narai da ta yi da fuskar sai da ya ji tamkar ya je ya tambaye ta damuwarta duk da yanayinta ya nuna masa mai napep take jira. Wata ajiyar zuciya ya sauke agowar da ya ara yi sai kuwa suka yi ido hu u da ita, da sauri ya sadda kansa yana danna waya duk sai kunya ta kama shi. Ita kuma sai lokacin ta gan shi, cikin takun ta mai tattare nutsuwa ta tako zuwa wajensa. Subhanallahi kawai yake ambata don tana tunkaro shi bugun zuciyarsa yana aruwa. "Yaya ABBAS" Har tsakiyar zuciyarsa ya ji sunan sai yake ji a duk lokacin da ta kira shi tamkar duniya babu wanda ya fi iya kiran sunansa ya yi da i sama da HAWWA. "Na'am anwata har an fito" Ya ce yana arfin halin kallon fuskarsa wani abu ya fusge shi, wanda ba don yana aryata kansa a kan ba zai so wata bayan SALIMAH ba da sai ya ce so ne ya fusge shi, ji ya yi dama a ce ta tsaya a haka kawai yake kallon fuskarta ba ya jin zai ta a gajiya amma fa a hakan ma wai matsayin anwarsa. "Na fito Yaya amma ban ga mai napep in ma kuma wayarsa a kashe ko ka ga zuwansa tafiya ya yi?" Tamkar kar ta tsaya da magana sosai yake jin kalamai da sanyin murya yadda take magana yana shiga dodon kunnensa tare da ratsa argo kai hatta asusuwansa bai bari ba, ji yake tamkar muryarta ma tana gudana a jikin jijiyoyin jikinsa. Yadda ta langa ar da kai tana yin tamkar ta yi kuka sai ya ji tamkar ya zama tsuntsu ya sunkuce ta ya kai ta school ina minti alilan don kar ya ga alamar damuwa shimfi e a fuskarsa. "Ki yi ha uri mana, ba sai kin shiga damuwa ba, ban gan shi ba amma na yi mamakin rashin zuwansa" Ya samu kansa da bata ha urin laifin da ba shi ya mata ba sai don kawai ba ya son ta damu, sannan arinsa na faranta mata don ko shi a ranar da ta fara bashi ha uri da Yaya Usman yana fa a masa maganganu ha a ya ji sanyi a ransa. Shiru ta yi ganin kiran awarta Afrah ya shigo wayarta, agawa ta yi. "Wai ya baki taho ba har yanzu? Sai an hana ki shiga" "Mai napep in ne bai zo ba amma bari na samu wani ko machine sai na taho" Wani abu ne ya caki zuciyar ABBAS jin wai za ta hau machine sai ya ji wani abu kawai ba ya son ganin ta hau bayan machine in wani namiji har gwara napep a kan machine, kafin ya ce wani abu sai ga Baffa ya fito. "Hauwa'u baki tafi ba dama?" "Bai zo ba Baffa ga shi ina neman makara kuma layin nan da safe abin hawa wahala yake" Wannan maganar ta yi dai dai fa zuwan FAROUQ abokin ABBAS da yake ta kiran ABBAS a waya zai tura masa lambar wani abokinsu da yake nema da gaggawa amma bai aga ba ya je gida Mama ta ce masa ya tafi wurin aiki shi ne ya biyo shi. ABBAS kuwa wayarsa a silent take ya ga kiran FAROUQ na farko kafin ya aga HAWWA ta zo sai ya sha'afa da kiran wani FAROUQ kasancewar wayar bata ara shi ya sa bai sake tunanin kiran yana shigowa ba bare har ya bi kira. Tun kan ya araso ya hangi ABBAS in HAWWA tsaye daga gefe a gabansa, shi dariya ce ma ta kufce masa saboda ya tabbata ABBAS ya kamu da son yarinyar amma ya i yarda da haka, ya yale shi sai son ya gama masa dabaibayi yadda a lokacin bai isa ya yi musu ba. Baffa barka da safiya" ABBAS da FAROUQ suka ha a baki wajen fa a. Amsa musu ya yi sai kuma ya