← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 43

Sashe 23

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mutumin arzi i ne. 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un' Ya ce yana sauke wayar daga kunnensa yana kallon jama'a yana ganin ga oshi ga kwanan yunwa ba ya so a aura auren bayan bai san inda ta tafi ba kuma bai san ranar da za ta dawo ba kuma bai san lokacin da za ta dawo ba sannan bai san mai zai fa awa mutane a fasa aurin auren ba. Hukunci aya kawai ya yanke shi ne ya fa i a asa wannan ne ka ai zai sa a fasa aura auren. Wayar ya ara mayarwa kunne da gangan sai kawai ya fata ambaton subhanallahi, kawai sai ya yanke jiki ta fa i a take jama'a suna hayya-hayya aka yi kansa amma ya saki jiki har da auke numfashi kinkimarsa aka yi aka saka a mota, nan fa wuri ya kacame da hayaniya wasu suna a aura tun da an taru wasu suna cewa ya za a yi a aura auren shugaban aurin aure rai a hannun Allah, da haka mutane suka watse Umar zaman dirshan ya yi a asa yana shar ar kuka shi a dole ba zai tafi ba sai an dawo an taru an aura masa auren wai Babansa ba in ciki yake masa shi ya sa ya fa i ana shirin mayar da shi ango dakyar direban gidansu ya lalla a shi ya shiga mota don ya mayar da shi gida don da alama shaye-shayen ya fata ta a masa walwa. *ABBAS* Tun lokacin da ya hango SALIMAH da bazawarinta sarai ya gane ta amma kuma abin ban mamakin shi ne bai ji ya shiga tashin hankalin da yake tunanin zai shiga ba idan ya ganta, sannan ko a ransa bai ji wani kishi na ya ganta da wani namiji wanda a baya yake ganin idan har ya ganta da wani sai abin da ba a rasa ba ita kanta SALIMAH bai wani ji damuwa da ita ba, a baya ko wuri ta ziyarta in yana wajen sai jikinsa ya bashi, amma sa anin yau bai ji komai ba illa iyaka ganin ba zatan da ya mata da farko ya so ru a shi amma sa ya shiga ambaton Allah sai ya ji ya saitu. Abin da SALIMAH bata sani ba ya gane don ta nuna masa matsayin da take takawa a yanzu ta je wurin sai dai ya lura har yau bata gama gane waye shi ba, a duniya abin wani abi tsone masa ido ba ko da a ce bashi da naira biyar ta kansa idan wani yana da miliyan ari ba zai damu ba ya san Allah ne ya ba wancan shi ma kuma ba ya cire rai daga rahmar ubangiji domin Allah ne yake azurtawa. Talaucinsa bai koya masa kyashi ko hassada da son kai wa matsayin wani da Allah ya yi wa arziki yake ji dama shi ne. *HAWWA* Tun da suka auki hanya hankalinta ya kwanta ganin ta ku uta daga wannan kaddararran auren da ake son lakaba mata auren wanda bai sam kansa ba kuma bai san darajar an adam ba, ba za ta ta a yarda ya aure shi a matsayin uban anta ba don ba ta ga zai zame musu garkuwa ba. Kallon SABEER take da yake kwance a jikinta yana baccinsa tana tunanin rayuwa kenan yanzu ita yake gani madadin mahaifiya tana son ta faranta masa kuma ba ta so ya yi kunci ko bakin ciki a rayuwa amma ta san matsawar suna gidan Baba Bukhari to tabbas za su rayu a unci saboda rashin amana. A tasha aka sauke su lokacin SABEER ya falka amma bai ware daga baccin ba, goyonsa ta yi ta tsaya ta saya masa pure water jin yana cewa zai sha ruwa duk da ta san yunwa yake ji tun da bai ci abinci ba. Napep ta tare musu suka kama hanyar gidan Baffa Nasiru a kofar gidan aka sauke su ta bawa mai napep ku in ta kama hannun SABEER suna shirin shiga gidan ta hango Baffa. "SABEER ka ga Baffan can" Ta ce cike da farin cikin ganin an uwan mahaifiyar tasu mai kama da Ummien kamar an tsaga kara. Dariya shi ma ya yi yana an tsalle alamar murna kasancewar yana matukar kaunarsu. SABEER hannunsa ya kwace daga rikon da ta masa ya nufi wurin Baffa da yake tsaye a wajen amma shi da yake hankalinsa ba a wurin yake ba sai bai gan su ba, bai ankara ba ya ji an rungume shi ta baya cike da mamaki ya juyo don a tunaninsa ma cikin wasu yaran ne saboda shi mutum ne na yara. "Baffa!" SABEER ya ce yana kara kankame shi don tun bayan mutuwar mahaifiyarsu tsawon shekara biyun bai sanya shi a ido ba, sannan a halin yanzu bayan HAWWA sai Baba Sadiya ne kawai wanda ya san masu kaunarsa sai yanzu da ya yi ido biyu da Baffa. Yaro kenan duk antarsa ya san mai aunarsa ko da zare masa idanu kake wannan abin yana walwarsa ba zai manta da shi domin yaro ba ya mantuwa. "SABEER kai ne" Baffa ya fa a yana kama hannuwan yaron duka biyu yana kallonsa tamkar yau ya fara arba da fuskarsa. Washe bakinsa ya yi ya ce "Ni ne Baffa ga can Aunty HAWWA" Ya ce yana nuno ya da yatsa, ago kai Baffa ya yi ya ganta tsaye tana murmushi. Idanunsa ne suka kawo wallah ya daka hannu ya goge wacce ta gangaro ganin mutane a wajen sai ya kama hannun SABEER in, wurin HAWWA suka arasa, yana zuwa ita ma ta rungume shi don ganin kamannin mahaifiyarta a fuskarsa ya sa ta ga tamkar mahaifiyarsu ce. "Hauwa kulu" Ya ce muryarsa tana rawa yana matukar kaunar yaran yana jin kaunar har cikin zuciyarsa tun da mahaifansu suka rasu ya nemi Alhaji Bukhari da ya bar masa yaran ya tafi da su Kaduna su zauna a hannunsa amma fafur ya i wai dangin uba su ne suka fi cancanta da su ri a kuma ma a yadda ya fuskanta dukiya ce kawai a gaban Alhaji Bukhari har sai da Baffa ya ce shi ya amince a bashi yaran ba tare da an bashi ko da tsinke bane daga cikin dukiyarsu don shi dama tsoron cin dukiyar maraya yake, yana tsoron ranar da Allah zai tashi shi ya tambaye shi yadda ya ci shi hatta bashi tsoron cinsa yake, sa anin wasu mutanen da basu auki cin bashi a komai ba, suna mantawa da ranar karshe, suna mantawa da ranar sakamako suna mantawa da hisabi. Bayanta ya bubbuga tare da janye ta daga jikinsa ganin a kofar gida ne hannunta ya kama yana rike da su suka kama hanyar kofar gidan. "Baffa ga ku in kayan can da aka siyar azu" ABBAS da ya zo zai ba Baffa ku in ciniki ya fa a yana an sunkuyowa ya mika masa da hannu biyu. "Ka ajiye a wurinka ABBAS zan shiga gida ne in na fito ma yi maganar" Cewar Baffa yana oye fuskarsa da ruwan hawaye ya taru a kwarmin idanun, yana so ya tuna dalilin da ya sa ya manta da ar uwarsa, yana so ya tuna dalilin da ya sa ba ya zuwa ya gan su amma ya kasa tuna komai shi ba don ya gan su ba ma, ko a walwarsa ba ya tuno su. Ba tare da ya ara ko da bi ta kan ABBAS in ba ya juya yana rike da hannayensu suka shiga cikin gidan. ABBAS har suka acewa ganinsa yana tsaye a wurin ri e da ku in a hannunsa bai ta a ganin uban gidan nasa a yanayin makamancin wannan ba sai dai lokacin da ar uwarsa ta mutu a Zariya da ya dawo duk ya zama wani iri amma yanzu ya rasa wane yara ne da zuwansu a sauya shi cikin anin lokaci. Da sanyin jiki ya juya ya koma wurin aikinsa ya san sai dai Usman ya musu rashin kyautawa kasancewarsa an abokin Baffan da yake ri ewa sai ya yi ta musu agawa da rainin hankali amma shi Baffa ya auke su tamkar an da ya haifa. Suna shiga gidan da sallama da take hura wuta ta ago tana amsa sallamar cike da mamaki. "SABEER, Hauwa'u" Ta ce tana kallonsu, da gudu SABEER ya je ya rungume ta yana ta murna kasancewarta mace ta gari wajen Baffa kuma tana kaunar ar uwarsa kamar yadda shi ma yake kaunarsu kasancewar ma su basu ta a haihuwa ba sai an abokinsa kuma amininsa da ya mutu Malam Ashiru yake rikon ansa guda biyu mace da na miji Usman da Amrah. "Ina ka shige Alhaji SABEER " Ta tambaya tana kama hannunsa suka nufi baranda inda tabarma take a shimfi e.Lale marhabin da zuwanku ana" Ta ce tana ta murma ta zauna tare da zaunar da SABEER a kan cinyarsa. "Hauwa'u" "Na'am Goggo" "Ina can gidan Baba, kuma a akin da muke kwana babu gado babu katifa, kuma babu abinci mai da i, kuma yageggen kaya nake sakawa" Ya ce yana kallonta, sosai Baffa ya ji maganar ta ta a shi dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama Alhaji Bukhari ba zai iya ri e amanar yaran nan ba shi kuma ya rasa mai ya sa ya manta da lamuransu duk da ganinsu da ya yi yau ya sanya shi fara zargin wani abu a kan mantuwar ta tsawon shekaru biyu ba tare da ya waiwayesu ba sai dai ba ya son zurfafa tunani domin an ce zato zunubi ko da ya zama gaskiya. An kawo musu abinci da ruwan sha, SABEER zagewa ya yi yana ta cin abincin sa anin HAWWA da ta ci ka an saboda duk gajiya ta gama ratsa jikinta. "Hauwa'u ya aka yi tsawon lokacin nan baki zo nan ba? Kin san mahaifiyarki mai yawan zumunci ce kuma tana zuwa da ku ke mai ya sa baki zo sada zumuncin ba tun da kika ga ni Allah bai bani iko ba? " Baffa ya tambaye ta yana kallonta tana wasa da yatsunta shi SABEER ya samu abin wasa yana ta uzurinsa. "Baffa babu dama shi ya sa bamu zo ba, babu wanda zai barmu" Ta ce tana tuna
Chapter 23 · 0% Book details