← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 43

Sashe 3

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rayuwa" Ta ce tana kallon lesunan tana hango yadda da ita ce ta same su ba karamin kyau za ta yi a ciki ba amma ina bata da ko irinsa guda aya ma dama ko kayan lefe bai mata ba Babanta ya ce ABBAS ya kawo ku in da ya sawwaka ai aure albarkarsa ake nema kuma aure yana kawo arziki. Yanzu shekara biyar da auren amma babu wani ci gaba sai ma ci baya gaba aya talauci ya musu kaka gida ga tsadar rayuwa rashin isassun sutura ya sa ko biki da suna bata son zuwa idan ta je sai ta ga ta raina kanta musamman in ta ga kawayenta sun yi shiga ta kece raini ita kuwa daga atamfa leda sai leshin mama ta mutu irin na legas in nan da ake sayarwa na hannu. Saboda haushi bata san ma lokacin da ta fito daga bussines group in ba, wajen status ta je nan ma ta shiga ganin hotunan da aka ora a status wanda na jikin hotunan suke sanye cikin shiga ta alfarma wasu an musu make up gashi nan dai amma duk ciki bata ga wacce ta mallaki ko da rabin kyanta ne ko kirar halittarta. Wani hoton wata mata da ta gani a status in wata kawarta matar tana zaune a kayataccen falonta da yaranta guda uku da alama yarinya aya ce ake yi wa murnar zagayowar ranar haihuwar ta domin ga cake nan da lemuka. "Gida na alfarma shi ne rayuwa" Ta ce a fili tana sauka daga whatsapp in ma baki aya ta ajiye wayar tana sauke idanunta a nata falon wanda sai ta ga tamkar a kufai take. "Ga doya da kwai" Ta jiyo wata tana tallah. Kiranta ta yi ta saya ta dubu ayar ragowar ku in abincin ranar da yake doyar ari bibbiyu ce ta zauna ta ci ta yi sallah ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita. ABBAS tun da ya baro gida ya nufi an kafintoci inda yake aikin kafinta haka ya wuni yana aiki, ko da ya ji kewar matarsa SALIMAH ya yi ta kiranta a waya amma bata auka ba haka ya gaji da kira ya hakura. Bai karya ba ya fita saboda tuwon ka an ne ko dubu biyun da ya bar mata ma rantowa ya yi haka ya wuni bai ci komai ba sai karfe biyar ya baro kafintocin. Tun da ya doso gidan gabansa yake fa uwa duk da hakan ya san yana faruwa da shi amma sai yake jin kamar na yau ya fi kullum hannu ya saka a aljihu ya fito da ku in ladan aikinsa da aka biya shi dubu uku da ari takwas, mayar da su ya yi yana son gano ko ku in za su isa ya famshi kansa a wajenta duk da ya ranci ku i da safe don ba ya so ta zauna babu abinci, a duniya da SALIMAH ta rasa abu gwara shi ya rasa ko ta halin kaka yana iya bakin kokarinsa don ganin ya faranta mata amma bata ganin hakan kullum gazawarsa take gani kullum burinta ya sawwake mata auransa amma ba zai iya sakinta ba sakinta babbar barazana ce ga rayuwarsa gani yake ba zai iya rayuwa a wannan duniyar matsawar ba tare da ita ba, amma ita she an da muggan kawayenta suna mata hu ubar banza ta ganin sun kawo karshen zaman sa da ita. Da sallama ya shigo gidan amma shiru ba a amsa ba, dama ya saba da hakan amma kuma rashin amsa sallamar ba zai sa ya daina yi ba saboda wajabcin sallamar da kuma ladan da ake samu idan an yi sallamar. Buhunsa mai auke da kayan kwale-kwalensa ya ajiye a inda yake ajiyewa kicin ya nufa domin samarwa cikinsa da yake ta kugi abin da zai sa a ciki sai dai tun kan ya karasa kicin in yake hango tamkar dai babu wasu alamu na an ora wani abu, hakan ce kuwa ta tabbata da ya karasa domin idanu hu u da ya yi da tuwon safen da ya sadaukar shi ga SALIMAH shi ya auki na annabawa. Wani acin rai ne ya ziyarce shi shai an ya azalzala zuciyarsa yana jin wani tukuki inda ya ha u da acin ran da yunwar ta haifar. Amma yaki ya yi da zuciyarsa wajen dannewa ya nufi falon. Tana zaune a kasan ledar tsakar akin tana yin magana da alama voice take yi sai da ya jira ta kammala ya dube ta ya ce "Haba SALIMAH yanzu in fita tun safe in dawo amma babu abin da kika dafa, kuma tuwon da na hakura na bar miki kika zubar da shi a kasa yanzu a halin da mutane suke ciki na tsadar rayuwar nan wasu ma suna kwana da yunwa, wasu suna mutuwa da yunwa wasu dusar awara suke ci ke har da wanda suke sakawa ruwan anwake suga suna sha amma ke... "Kai ABBAS dakata! Ba fa haifata ka yi ba da za kake mini magana fa a-fa "Haba SALIMAH mene ne na fa an a nan daga fa ar gaskiya sai cibi ya zama kari... "Bana son jin komai yanzu don ban yi girki ba za kake wani maimaita mini magana ai hukunta ni ya dace ka yi, sannan batun tuwo,tuwo,tuwo kana maimaitawa tamkar ka samu karatu mene ne don na zubar da tuwon bana ci sai kawai in ci kuma su masu kwana da yunwar ai su suka so dama rayuwa ai hawa-hawa ce tun da ba ni na hana su neman abin da za su ci ba, wasu ma basu san mene ne wani tuwo a rayuwarsu ba daga nama sai kayan da i irin rayuwar da nake mafarkin yi, irin burin da na ci ka zo ka mini shigar sauri ni ba tsararka bace ni ba sa'ar aurenka ba ce ba ajinka ba ce ni ABBAS sau nawa kake so in maimaita maka cewa na tsaneka ka sake ni in je in auri wanda yake daidai da tsarin rayuwata, inda zan huta wani nawa ma ya huta wallahi wallahi wallahi ba zan ta a kashe yarintata a wannan kaskantacciyar rayuwar talaucin ba!" Yadda take maganar cikin hargowa da aga sauti ya sa gaba aya ya rasa bakin magana, ta saba masa hakan a kullum wani lokacin ma tsakar dare yana bacci take tada shi da wannan masifar da zancen saki ya sha fa a mata babu kyau mace take neman saki a wajen miji ba tare da wani kwakkwaran dalili ba na cutarwa ko makamancin su amma kururuwar shai an ba ta bari ta fuskanci komai sai ta ce ita kuwa take da hujja domin kuwa cutar da ita ake yi, saboda wata sabuwar rayuwar take so ba wannan ba. Sai dai yau maganganun nata sun masa zafi da yawa wani ciwo yake ji a zuciyarsa musamman saitin kirjinsa daga hagu inda zuciyarsa take dashe a wajen tabbas in bai yi wasa ba SALIMAH tana dab da saka masa ciwon zuciya don hawan jini tuni ya ha u da shi. "SALIMAH" Ya fa a da sanyin murya yana jin yadda kwalla ta taru a idanunsa, ga wani nauyi da yake ji a zuciyarsa tamkar an ajiye dutse a wajen. ."Sunan da ubana ya dasa mini" Ta ce tana rike da kugu tana wani jijjiga jiki. ."Na sani dama, amma don Allah ki bar zuciyata ta huta ina kaunarki SALIMAH na yi yaki da zuciyata a kan in sawwake miki ko don na ga hakan shi ne farin cikin ki, amma ba zan iya ba SALIMAH, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, ba zan juri rashin ki ba rasa ki tamkar rasa duk wani walwala da farinciki na ne duk da ina tare da ke in ma baki bar ni na samu hakan ba amma dai da babu gwara babu da i ko da a ce za kike yankar naman jikina a kullum na yarda na rayu da ke na zan iya rasa komai saboda ke na aminta a hana ni komai in za a barni da ke... "Ai kuwa wallahi ka kama RU IYAR IGIYA don wacce kake so in baka gabanta kuma ni zan iya yin komai don na rabu da kai kuma tun da kai babu zuciya a kirjinka zan cigaba da zame maka ciwon ido har ranar da wa'adin aurena zai cika ka sauwake mini, duniya ban ta a ganin marar zuciya ba sai kai ABBAS ni dai ina jin sai na fara rokon Allah ya auki ranka ka mutu in auri wani... "Zan fi so hakan ya kasance ni na fi son na mutu ke ki rayu, na fi so indai bana duniyar ki auri kowa ma na san tun da bana raye hakan ba zai yi wani sanadi a gareni ba, idan har kika haifa mini a wanda zai zama na bar tsatson ki a duniya wanda zai ke mini addu'a SALIMAH burina ya cika" "Albishinka ce goro ABBAS kalli nan" Ta ce tana aga hannun rigarta farin fatar dantsen hannunta ya bayyana. "Wannan tsinken hana haihuwa ne na saka tun ana gobe aurin aurena da kai na je na saka na shekara uku! Kuma bayan wa'adin shekarun sun cika na je aka cire aka mayar mini da wani na shekara ukun yanzu shekararsa biyu yana karasa shekara aya zan cire in maida wani, ko shekara dubu zan yi a gidanka sai na yi ta sakawa, ku tarayyar auratayyar ma ai ka san ba da ha in kaina kake yi ba, kai kanka ka san wata rana maganin bacci kake zuba mini a abun sha wanda bacci mai nauyi zai auke ni har ka gama uzurinka ban sani ba, saboda baka gabana uzurin auratayya da kai ma bana kaunar yi, kuma ina son ka san wani abu ni dama ba zan haifi yara a gidan talauci ba rainon madara rarrafen kafet da tiles nake so ba rainon tuwo rarrafen ledar tsakar aki ba" Tun da ta fara maganar hawaye suke ambaliya a idanunsa, wani aci yake ji a zuciyarsa tabbas SALIMAH ita ce kaddararsa da Allah ya ora masa masifaffan sonta yana hakuri da duk abubuwa da cin kashin da take masa, sai dai an zo ga ar da ba zai jure ba
Chapter 3 · 0% Book details