Sashe 17
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne autan gidan, in kana da ku i ko shawara sai an jira ka zo za a yanke idan kuwa ka ce ga yadda za a yi babu mai canjawa. In aure ka je nema ko da an san duka kake wa matarka ta gidan ko kuma kana wulakantata to fa ba za a ga wannan ba ko wani ya yi yunkurin fa ar aibinka to cewa za a yi bakin ciki yake, yanzu akwai kawayenmu wanda muka taso tare tun da suka yi aure a gidan daula shikenan ko a hanya muka ha u kallon arziki ba ma samu, a takaice ko biki kika je ko suna kina dosowa kafin ki karaso zugar matan da suke wurin za su shiga karewa suturarki kallo tun daga tsakiyar kan ki har yatsan kafarki sai an kalla daga nan za a gane wacece ke idan aka ga kin gaza ta ko ina kina karasowa idan akwai wanda kika sani za su auke kai, idan kuwa sutura kika saka ta kece raini kina zuwa za a washe baki kowa yana kokarin miki magana wannan ne manyan dalilan da suke ci mini tuwo a kwarya, su ne suke sa burina yake karuwa ina so in ci mai kyau in kwanta mai kyau ni soyayya baya dame ni ba ko kasancewar miji na gari, kuma a ma idan suka taso suka ga talaka ka za a musu sai suke ganin abubuwan more rayuwa wajen wasu amma in ka za a musu attajiri if za ki ji kowa yana ji da su a dangi" Tun da ta fara dogon jawabin nan kallonta kawai take tana tunanin sabo da wannan ne ta kira ta kanta yana tukunya tabbas idan haka ne kuwa ta kama RU IYAR IGIYA. "Duk wannan ba gaskiya banr idan kuwa gaskiya ne ya ke antu ga wanda suke da gajeran tunani da rashin tauhidi, ai zama na gari ya fi komai a rayuwa, ku i suna karewa talauci ya baibaye mai su sai ki ga ya zama tamkar ba shi ne mai ku in nan ba da yake ta facaka, shi ma talaka arziki yana zuwar masa sai ki ga Allah ya azurtashi tamar bai ta a neman taro da kwabo ya rasa ba, a kuma uba na gari da shi ake ado, idan har dukiya gare shi yana da hali marar kyau wata rana sai an goranta musu wata rana sai sun tuhumi mahaifiyarsu da maganar ko tambayar da za ta nemi amsar basu ta rasa" "Ba za ji gane ba, shi ya sa na ce a duhu kike". "Ko kuma ke ce a duhun ba". "Ni a haske nake kuma ni idan na tashi sai na auri mai dukiyar da koginta ba zai ta a kafewa ba kin ga na yi ban kwana da talauci, ke ni fa saboda ba na son haihuwa gidan talauci ka taso babu ta baibayeka kai da yaran da uban ko asibiti za a kai yaro ana cewa ku je asibitin sai ki kawo katin idan na yi buga-buga na samo sai a saya maganin, in kin tambaya ku in cefane a ce babu a duniya na tsani kalmar babu nama kuwa daga sallar layya sai wata layyar ina dalili" "Allah shirye ki ya ganar da ke". "Ai kuwa ba zan gane ba, ke dai ce nake so ki gane bari sai na yi aure zan kara fahimtar da ke, shi ya sa na saka inplan a gidan ABBAS kar na haihuwa abubuwa su ca e mutumin da ko gidan kansa ba shi da shi, sai aikin kafinta ni karatun da ya yi ma ban ga amfaninsa ba wai mai digiri amma ya ajiye takardu saboda ba aiki yana fama da kusa da katako" Ta ce tana yatsina fuska da ta e baki. "Allah zai bashi" Ta ce cike da takaici don ba za ta iya cigaba da tattaunawa da SALIMAH ba saboda ta yi nisa ba ta jin kira in ban da toshewar basira har ta saka inpan lallai abin mai girma ne ba karamin gaba take yi da talauci ba tana mantawa Allah ne yake azurtawa kuma shi yake talautawa. Bata wani kara jimawa ba ta mata sallama za ta tafi saboda takaici, har kofar gida ta rako ta suka yi sallama ta tafi tana shirin shiga gida sai ga RUKY tare suka shiga gidan suna tattaunawa. "Wallahi RUKU har alla-alla nake na kammala iddar nan ko na fara tara zawara wa in ke kashe kala, don ni da na samu mai kumbar susa ba zan tsaya kallon ruwa kwa o ya mini kafa ba" "To ai ba a nan gizo yake sakar ba SALIMAH, zuwan zawarawa ba shi ne auren ba, bare ke da kike da kyau da kirar nan ai sai an miki layi sai dai... "Kamar ya? Dama ai na san abu mai kyau shi yake siyar da kansa a kasuwa, amma sai dai mai?" SALIMAH ta yi saurin katse mata magana. "Abin da nake so ki sani na gari sun yi karanci, yanzu za ki ga tarin zawarawa amma ba da aure suke zuwa ba" "Da mai suke zuwa to?" "Don a yi soyayya kawai" "To ba amfanin soyayya aure ba". "Hmmm! A baya kenan amma a wannan zamani akalar ta canja, kalilan ne masu zuwa da auren kuma wahala suke, daga namiji ya zo rimi-rimi sai ki ji ya fito fili ya fa a miki holewa ce ta kawo shi, ku kunya ma ba sa ji ke wani fa sai ki ji ya kama miki hannu ba da izininki ba in kika masa magana zai ce ai ba komai bane, saboda yanzu zina ma ba auke ta a bakin komai ba ado aka auke ta duniya ta lalace kuma ta zo karshe" .."Ikon Allah, to amma sun san matan da suke wa ko?" "Kamar ya ai abin ya zama ruwam dare gama duniya, sai ko ga babban mutum yana baza babbar riga a girme zai haife ki amma ya zo miki da magana ta banza" "Sai ka za i wanda basu da irin halayyar nan, kin san a duniya na tsani zina na tsani mai yinta ko abin da zai kusanta ni da ita" ."To kuwa ki shirya saboda ha uwa aya biyu za ki ji ya anbata miki so yake ku ke e, ko ya ce yana so ku je hotel ku huta". "Haba dai wasa ma ai wargi yake ai bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane" "SALIMAH duniyar nan fa da kika sani shekaru biyar baya kafin ki yi aure ba ita ba ce a halin yanzu, duniya ta lalace wallahi, yadda bakya zato yanzu tsawon shekara uku da aurena ya mutu ina gida amma har yau na kasa samun tsayayye, kowa ya zo ba da maganar aure zai zo ba, yanzu anmata ma gasu nan duk suna zaune a gida amma miji ya kasa samuwa bare bazawara, na bari SANUSI tsohon mijina ya su uce mini yanzu na zo ina da na sani da son komawa gidansa amma shi kuma yanzu ba ta ni yake ba ya samu wata ya aura" "Kowa da farin jininsa bari ki ga in yi idda zan baki mamaki" "Hmmm! Kin kasa fahimtata ina nuna miki maza za suke miki tururuwa amma ba da aure ba ko maganar aure kika yi wa mutum sai ya janye kafarsa, idan suna zuwar miki da hulewa kika nuna ke ba haka ba da ka an-ka an za su dare su barki" "Ki zuba ido kawai BASEERA kin san dai irin tarin farin jinin da na yi ina budurwa yanzu sai na kere" Ta ce tana wani murmushi. ."Wallahi da za ki ji shawarata da baki bari kin yi idda ba tun kina da sauran dama ki koma akin ki, ba za ki gane mai nake nufi ba sai kin fara zawarcin" "Allah mini tsari kuma za mu ata idan kina mini maganar komawa gidan ABBAS" Ta ce tana jan wani tsaki. "Shikena SALIMAH tun da haka kika ce amma akwai ranar da za ki tuna da wannan tattaunawar" "Wai ya maganar Alhaji ma'ilu naki?" Ta jefa mata maganar don son kawai da wancan maganar. Shiru BASEERA ta yi tana tuno yadda suka rabu jiya baran-baran saboda kawai suna hira a mota sai ji ta yi ya rungume ta dakyar ta kwaci kanta, bayan shi ka ai ne take ganin ta samu mai tsoron Allah ashe dai shi ma lumbu-lumbu ne wutar kaikayi, wannan dalilin ne ya sa ta zo don ta bayyanawa SALIMAH cewa ta rasa wanda za ta za a ta aura amma ta ki fahimta ita yanzu damuwarta ta samu wanda zai aure ta amma abu ya gagara. Ga shi ita mace sai ta jira an ce ana son ta ba wai ita ce za ta je ta za a ba ta ce tana so. Ita gaba aya sai yanzu ta gane aure ba karamar sutura ba ce ga mace sai yanzu da ta fito don takaici sai a mayar da mace kamar karya kowa ma sai ya zo ya ce yana sonta, kare da doki wani ma sa'an kanenka ne za a ce yana sallama da kai kana fita ka ga yaro a tsaye wai sonka yake tabbas akwai takaici da kalubale a rayuwar zawarci. "Ko bai zo ba jiyan na ga muna nan a tare ya kira ki yana zuwa" "Ya zo amma na sallame shi" "Ke ko saboda mai bayan kin tsayar da shi" "Saboda shi ma kamar sauran yake abin da yake kawo sauran shi ma shi ne ya kawo shi, kwantan auna ya yi shi ya sa bai fahimta ba, duk na sallami kowa na rike shi ashe dai RU IYAR IGIYA na kama" "Ikon Allah to Allah kawo miki wani" Shiru ta yi bata ce komai ba. "Ba za ki amsa da amin ba" "Wallahi SALIMAH na rasa wane kalar tunani zan yi, a zatona idan na yi idda ba zan wuce wata biyu ban yi aure ba, amma kin ga har shekara uku na rasa mai aurena kullum jiya i yau, ga yarana ba bar su gidan ubansu kullum idan suka zo wurina sai na zubar da hawaye saboda sun yi baki sun rame ko ka an ba sa cikin farin ciki ko walwala