← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata wace mace ce za ta yarda ta aure shi? In ba wacce bata san ciwon kanta ba, ko iyayanta mararsa sanin darajar ar su ba, amma ita saboda maraici da rashin sanin ya kamata da kuma rashin tsoron Allah za a aura mata an shaye-shaye. Da a ce ar su ce ba za su ta a yarda su aura mata shi ba. 09013181851 [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RU IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 7 *SALIMAH* Kwance take a barandar kofar aki tana charting da EESHART yanzu kam ta sakar suna hul arsu kamar da, sai dai ita a angaren EESHART dama abij da ya da ta fara yi wa SALIMAH wulakanci lokacin da aka yi sakin saboda kuduri da burinta ne ya cika a fili tana kaunar SALIMAH kamar me amma a zuciyarta ta tsane ta hassada take mata musanman da take zaune a gidan aurenta lafiya bata san matsaloli da kalubaken da mata suke fuskanta a gidanjen aurensu ba. Duk da dama aure an hakuri kuma hanya ce ta samu aljanna ita kuma aljanna ba za a same ta a haka ba dama an kewaye aljanna da abubuwan da zuciya bata so, kuma an lullu e wuta da abin da zuciya take so. Ma'ana duk wani abu wanda yake sa on Allah ne sai aka ce sai mutum ya bar shi zai shiga aljanna, haka ma duk wani abu da zuciya take so sai aka hani mutum aikatawa sai hakan ya zama mukullin shiga aljanna. Misali idan mace ta yi hakuri ta jure a gidan aure ta yi biyayya ga mijinta to za ta shiga aljanna sai dai wannan biyayyar ita ce mai wahala wata tana gani mijim ya tauye ta ne bayan kuma Allah ne ya yi umarni da hakan. Idan kuma ta bijire hakan zai sa ta shiga wuta Allah kiyaye. Har sai da ta ga ta kashe mata auren sannan hankalinta ya kwanta ko kyautata mata da take yi a gidan auren, saka kati da data bata ku i da sauransu din ta kara saka mata kwa ayi da burin auren mai ku i ne ta kashe auren saboda ta san da wahala ta samu miji mai hakuri mai sonta wanda ya ha a komai kamar ABBAS. Ganin kar SALIMAH ta yi saurin harbo jirginta tun lokaci bai kure mata ba ta koma gidan ABBAS in shi ya sa ta sauya shawara a kan bin komai a sannu har sai ta yi wani auren duk da ta san yanzu burin auren mai ku in ya zauna a zuciyarta daram ta yadda duk runtsi duk wuya ba za ta koma gidan ABBAS in ba. Sallamar BASEERA ce ta katse mata dariyar da take kyalkyalawa, EESHART tana bata labarin wani littafi mai ban dariya da ta karanta na maman afrah mai suna AN ADAIDAITA SAHU har tana ce mata tsabar dariya sai da ta tuntsuro daga kan kujera, tamkar ita take karantawa haka ta ji labarin ya bata dariya tana cikin wannan halin ne BASEERA ta yi sallama. Amsa mata ta yi tana mai ha e rai tamkar ba ita ce take dariya yanzu ba. Karasowa ta yi ta zauna tana murmushi dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya. "Hajiya SALIMAH ikon Allah kamar kin ga makiyiyarki?" Ta ce tana murmushi har lokaci. "Mai kika gani?" "Mene ne ma ban gani ba, kin ga yadda kika ara rai?" Majewa ta yi ba tare da ta amsa mata ba. "Ina wuni, ni in gaishe ki tun da ni ban samu arzikin a gaishe ni ba" "Yo katin gayyata na aika miki da zan gaishe ki? Ke babu mai yin magana da ke cikin da in rai sai ki hau wa'azi tamkar ke kika fi kowa sanin dai dai da sanin ya kamata" "Allah sarki kawata, ita dama ai gaskiya ciwi ne da ita kuma tana da aci amma ki saki ranki yau ba wannan ne ya kawo ni ba dama na ga na miki magana saman whatsapp baki bu e ba na kira ki ya fi a kirga bakya aukan kirana, sgi ne na ce bati na zo in ji laifina tun da ni ba za a je inda nake ba" Sakin fuskarta ta yi, ta ce "To ai ke in ce daga nasiha sai wa'azi kin ga kuwa ai ba kullum akw kwana a gado ba" "Haka ne" "Yanzu ya kike, kuma ina kika baro mini baby da babanta?" "Ina lafiya, baby tana gidanmu a can take yau tun safe, shi kuma Habib kalbi yanzu ya ajiye ni" "Inyeee ka ga tattabaru masoyan asali in ka ga wata ka ga zarah ni na kasa sanin yaushe ne soyayyar nan za ta tsufa don kullum sai hauhawa take tamkar an zubaaa fulawa yis" Ta ce tana dariya. "Ke ko, wa ya fa a miki soyayya tana tsufa ai sai dai masu yin ta su tsufa, kuma a gidan aure in dai miji zai samu abin da yake so daga gare ki, na daga biyayya kuma kina girmama shi, sanna uwa uba tsafta da kwalliya gyara jikin ki matsayinki na a mace idan na ce gyara kowace macs ta san mai nake nufi to matsawar kika kiyaye wannan duk taurin kan namiji za ki samu salama da sasaauci za ki samu zaman lafiya shi namiji yana da son girma da son a girmama shi, sannan gyaran jikin ki ko yaushe ya jiki yadda ya kamata domin mu'amalar auratayya ita ce aure duk wanda ba ya samun biyan bukata kuwa wannan ne mafarin gur acewar zaman lafiyarsa a tare da abokin zamansa, wai ina Umma kin sa sai zuba nake ban tambaye ta ba". "Ta je asibiti dubiya, kuma wannan dogon jawabin naki zai fi kyau ga wanda yake tare da mijin da yake so yake kauna, idan fa aka ce babu so to babu magana duk wani abu ba zai samu ba, idan na yi sabon aure na auri za ina zan zo kike biya mini karatuttukan nan" Ta ce tana dariya, ita ma dariyar ta yi shiru ya an biyo baya. "Ga ruwa" Ta ce lokacin da ta akko mata pure water ta mika mata, kar a ta yi tana fasawa ta sha ka an ta ajiye. "Ni yanzu na matsu in gama idda ko na fara famtamawa na za a na darje" Ta ce tana kallon BASEERA. Murmushi mg ciwo BASEERA ta yi tana kallonta da tausayawa ta san SALIMAH ta yi rashin miji mai kaunarta da gaskiya kauna wacce babu algus duk da bata mata fatan wani abun a nan gama amma dai ta san ba za ta ta a samun kamar ABBAS ba sai dai wani lullu i mai cike da duhu ya mata shamaki da ganin hakan, duniyar ce w gabanta tana mamakin ma yadda ita ko mutuwa ba ta wani damuwa da tunaninta ko a cikin zance da wuya ki ji ta sako mutuwa. a da darjewa ai ba shi ne nagartar ba, wani za in ba ka gane za en tumun dare ka yi sai in ka je cikin gidan auren" "Ban gane ba mai kike so ki ce mini?" "Hmmm! SALIMAH kenan, shi fa samun nagartaccen miji dace ne kin san shi namiji ba kamar kwarya bane da za ki ce sai kin kwankwasa kin gane shi, kuma baka gane waye mutum har sai ka zauna da shi ko da kuwa cikin kawaye ne zama ne yake sa ka fahimci halayyar mutum idan zama ya yi zama, kin san hangen dala ba shiga birni ne ba bari na yi shiru kar na cika ki da surutu tun da kin ce ni wa'azi da nasihata sun yi yawa" "A'a ni fa a kan ABBAS ne bana son ki dame ni amma in dai a kan zawarawa ne idan akwai hanyoyin da zan gane wa zan aura ki fahimtar da ni duk da ni ban damu da kasancewar mutum na kirki ba bukatata in samu inda zan huta in ci uban naira har ta yi kukan dole" "To ai tun da tunanin da burinki ya sha bamban ba sai na mata lokacina ba, in dai mai ku i ne ai ana iya gane shi a kallon farko dama nagarta ce nake magana ke kuma ba ita bace a tsarinki, kenan ke ko buri da fatan ki za awa yaranki uba nagari bakya yi sai mai ku i kawai?" Sosai SALIMAH ta kyalkyale da dariya, hae tana rike ciki, mamaki BASEERA take yi don a cikin maganganunta ba ta ga wanda ta yi da har zai bada dariya kamar yadda ta ga tana yi ba. Kallonta take har sai da ta tsagaita sannan ta ce "Wai don Allah BASEERA sai yaushe za ki waye? Har yanzu idan kika yi wani furucin sai in ji tamkar a cikin tukunyar yake, baki san yanzu ka ya waye ba an samu cigaba ta angarori da dama, shin an fa a miki a banza nake son na yi aure a daula?" Ta yi maganar tana kafe ta da ido alamar tambaya. "Sai kin fa a na ji ai ba zan sani ba tun da ina cikin duhun kai da rashin wayewa kaina yana rufe a tukunya" Ta ce cike da gatse, amma da yake ita SALIMAH dukan iska ce bata gane magana BASEERA ta fa a mata ba. Murmusawa ta yi ta aga hannunta ta ora a kafa ar BASEERA ta ce "Yanzu da jike gani duniya ta lalace, idan kana da ku i kai ne mutumin kirki a idanun mutane ko da kuwa ka fi kowa rashin mutunci da halayen kyama, yanzu ba a duba wani hali kake da shi illa iyaka ana duba mai kake da shi mai ka tara? In har kana da ku i a gidanku kai ne babba ko da kuwa kai
Chapter 16 · 0% Book details