Sashe 42
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ai kujera ce ke ko don ya zauna zai neme ki da tsohuwar zuma ake magani" Ta ce tana jin ciwon abin da aka yi wa arta. "Yanzu ni ban san ya zan yi ba ko na fa awa su EESHART da RUKY su zo dannar kirji?" "Hauka kike SALIMAH son a saka ki a bakin duniya, yadda muka cika baki muna daga ke ba ari ya samu mace kyakkyawa kuma yanzu a ji labari ya sauya to wallahi da fita waje ma sai ta gagaremu daga ni har ke, bakin ki alekum ki zauna ke ka ai wani ma bai san an yi ba, shi kuma abin da ya yi ya je don kansa, saboda wallahi ba don mai ku i ne ba da a ce ABBAS ne ahalil fu ara'u ba zan raga masa ba sai na wanke shi tas" "Ai shi ABBAS cewa ya yi ba zai mini kishiya ba " Ta ce cikin sanyin murya tana tuna yadda yake ro on ta zauna da shi ba zai ta a ha a ta wata a mace ba amma ga shi a kwana uku da aure ranar na hu u za a dan ara mata kishiya. Haka suka zanta da Umma suka yi sallama Umma sai ashat take lu awa tana tsinewa Alhaji Tahir. Nan ta kwanta bata tashi ba, yau ko yunwar ma bata ji, wajen arfe takwas ta ji an turo ofar falo tana jin aran sauran ofofin akuna ana bu ewa ana rufewa wannan ya nuna mata cewa Alhaji Tahir ne ya zo nemanta shi ne yake duba akunan ko zai ganta amma ganin bata nan bai kuma bu e inda take ciki ba ya koma falon asan ya zauna a kujera ya kame yana danna waya. "SALIMAH" Ya wala mata kira, sai da ya yi sau uku don ya auka tana sama ma shi kuma ba ya son ya hau saman, fitowa ta yi ba tare da ta amsa ba, sanye yake da blue shaddar sabuwa dal sai she i take ya sha babbar riga da hula ga agogo takalmansa suna afarsa gaba aya falon ya bu e da amshin turarensa. Sau aya ya ago ya ganta da rigar bacci idanun nan jeme-jeme tana aika masa kallon tsana ta araso ta zauna a wata kujerar da ban. "Kin tashi lafiya? Tsakanin sama da asan wanne kika auka? Zan fita arfe goma za a aura auren" asa" Shi ne kawai abin da ta ce. "To ita amarya ASEEYA sai ta au saman" Ya ce yana tashi tare da gyara babbar rigarsa ya fita, da harara ta bi bayan nasa tana maimaita sunan amaryar a zuciyarta. Wai "ASEEYA" Ko da i babu. Haka ta wuni su u babu walwala yau ko charting in ma ta kasa yi bata ganr komai zuciyarta kawai zafi take ashe haka mata suke ji in za a musu kishiya? Har gwara wasu sun auki shekaru amma ita fa kwana uku a kwana ukun ko da ango bata tare ba. Bayan ta idar da sallar isha'i tana falon a zaune ta doka uban tagumi tana jiran zuwan an kawo amarya, aran bu e get ne ya sa gabanta mummunan fa uwa don ta auka an kawo amaryar ne amma abin mamaki aaran shigowar mota aya ta jiyo sai aka rufe get in wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana fatan Allah sa ba a aura auren ba, don a tunaninta Alhaji ne ya shigo gidan. Tsayuwar motar ta ji tare da bu ofa da rufewa sau biyu, tana ta sa a da warwara ba auki wani lokaci ba ta ji an turo ofar falo ido ta zubawa ofar, abin da ta gani ne ya so zautar da ita babu shiri sai gata a tsaye a kan afafunta, Alhaji Tahir ne goye da wata zanka iyar budurwa wacce fuskarta take a lullu e irin ta amare. "SALIMAH rufe ofar amarya na goyo wai bata son a zo kawota a taru ni ka ai na je na akkota kuma shi ne wai ba za ta taka da afarta ba sai na goye ta kin ji rigima irin ta amare ko" Ya ce bakinsa washe kamar gonar auduga yadda dai yake washe mata baki lokacin tana gidansu amma zuwanta gidansa ya sa dariyarsa ta yi atan dabo sai yanzu da yake cike da shau in ya goyo amarya. "Aunty SALIMAH ina wuni" Ta ji wata siririyar muryar amaryar da take bayan Alhaji ta fa a. Basu jira cewarta ba kawai ya doshi matakala suka bar ta a tsaye tamkar an dasa ta a wajen, da kallo ta bi su sai da suka gama hayewa ta hango amaryar ta aga mayafi ta mata gwalo ta rufe fuskar tare da ago mata hannu alamar bye-bye. Suna acewa ganinta ta dur ushe a wajen ta saki kuka marar sauti, ta fara rarrafawa ta shige akinta ko ofar falon da ya ce ta rufe bata rufe ba, a asan cafet ta kwanta ta kamo sunan Umma ta ranga a mata kira. "Allah sa an fasa ba a aura ba" Shi ne abin da Umma ta ce. "Umma an aura shi fa ya akko amarya goye da ita ya shigo falona, suka haye sama" "Shegu aniyarsu ta bi su, marar ri e al awari na mamajon banza na mamajon wofi" Umma ta shiga surfa fa a tana kumfar baki ita kuma SALIMAH kawai kuka take. *BAYAN KWANA GOMA* Alhaji da amarya sai da suka kwashe sati guda suna cin amarci, ta sha ganin takaici tsantsa da bariki, tana zaune a falo za su sakko hannunsu ma ale da juna, amaryar budurwa ce kuma tana da nata kyan daidai gwargwado, sai dai kissarta ka ai ta isa saka kishiya kuka, kissa take irin asan nan don hatta zaman falon asa sai da ya gagari SALIMAH saboda gani takaici sai bedroom ta mayar wurin zamanta. Kwanakin amarya suna arewa ya yi tafiya wai zai yi sati guda, dama ko da amarya tana nan ma saboda ri i a angaren suke basa tafiya nasa angaren kuma SALIMAH ta lura kullum sai ya fita da dare tsakiyar dare amma bata san ina yake zuwa ba. Ganin yau kwanasa uku da tafiya kuma ya ce sati guda zai yi ta saka a ranta yau sai ta ziyarci part in Alhaji Tahir, kawai so take ta ga uwar abin da ya saka a akin ya ce ba a shiga wata ila ma amaryar zai bar wa. Sai da ta bari sawu ya auke babu motsin kowa sha aya da rabi ta akko mukullin da ya bata guda ayan nan da ya ce za take amfani da shi ranar bakinta. Har ta araso part in tana waige-waige na rashin gaskiya, hannunta yana karkarwa ta saka mukullin ta bu e ta shiga ta rufe ofar ba tare da ta saka mukulli ba. Da fitilar wayarta ta haska kasancewar angaren duhu arin, direct sama ta hau duk da bata ta a hawa ba gabanta yana fa uwa saboda ya ce kar a shiga amma ita sai ta ga wal uwar daka. Gabas ta yi kamar yadda ya ce tana xuwa ta ga akin, ta haska ta ga sunansa da ya fa a a rubuce hannunta tsabar karkarwa har wayar neman su ucewa take amma a haka ta mur a handle in cikin sa'a ofar ta bu e alamar babu mukulli da sauri ta kutsa kai ciki don arfin hali har da mayar da ofar ta rufe.