← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 43

Sashe 25

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA MAMAN AFRAH *First Class Writers Asso* Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 11 Hajiya Rayyanatu da bata san shirin Baba ba ko ka an bata san mai yake wakana a can in ba tun lokacin da ya kashe mata waya, suna zance da ma ociyarta tana ta nuna cewa iya yarinyar ai kanta ta yi wa da ta gudu don su gaba ta kai su gobarar titi. Da yake ita da ita in sammakal jirgi aya ne ya akko su sai take nuna mata ta hutar da su Hajiyar wahala. Ita dai fatan ta Allah sa kar a aura auren a wannan halin ne suna ta dariya abin su da alama duniyar ta musu da i don a ganin Hajiyar da tafiyar HAWWA da zamanta duk uwar ubansu aya, idan ma aya suka yi su je dan kansu, ita dai fatan ta kar a aura auren a bar mata a da igiyar wata matar galihu in ban da ma suna son ya shiryu ai shi ba sa'an auren HAWWA bane domin kuwa wutsiyar ra umi ta yi nesa da asa. Kukan da Umar yake ta faman rafkawa tamkar wanda ake zare masa rai shi ne ya katse musu nisha in da suke ciki, dama su ka ai ne a falon da yake bata auki auren da muhimmanci ba ko gayyata bata yi ba ita ma Lawisa tana sama abinta. A ki ime Hajiya ta tashi ta fito daga falon ma ociyarta tana take mata baya saboda abin ya aure mata kai ya san dai matsawar an aura aure babu abin da zai sa Umar yake faman yage baki yana kuka da kururuwa tamkar uwarsa ta bar duniya, amma dai ta fi son tabbayar da gaskiyar lamari saboda masu iya magana sun ce wa a a bakin mai ita ta fi da in ji. Suna fitowa suka yi ido hu u da Umar da yake tamkar mahaukaci sabon kamu ya cire babbar rigarsa ya yi amara da ita a ugu ma'ana ya aure a ugunsa ga hular nan ta kalli arewa masu gabas uwa uba fuskar nan shar ar da hawaye har da majina yana kuka hai an direban yana rirri e shi, shi kuma yana fisgewa tamkar za a saka mahaukaci a turu. in ciki yake mini wayyo na shiga uku na lalace" Ya ce yana rusar kuka duk ya cika gidan da kururuwa abin da ya auki hankalin ma'aikatan gidan suka fara fitowa daga ciki domin an ce gani ya kori ji sai dai suna zuwa da suka ga angon ranar a rikice sai suka sha jinin jikinsu. "Duk wanda ya kara minti biyu a wurin nan a bakin aikinsa" Cewar Hajiya a ufule tana jin haushin su kowa ya ya dare ya koma ciki suke us ban da Baba Sadiya da ta shige aki ta tuntsure da dariya don ta san zancen gizo ba ya wuce na i ma'ana kukan nashi da haukar da yake ba ya rasa nasaba da tafiyar HAWWA. "Wallahi Hauwa'u ta maka nisa yaro dama ba sa'arka bace addara ce wacce ta riga fata ta kusan giftawa a tsakaninku kuma Allah ya kare yarinyar kirki, ai Hauwa'u da nagartaccen miji ta dace ba kai ba sangartacce" Ta fa a a fili tana zaumawa ta cigaba da abinnda take yi. "Wai kukan uban me yake?" Hajiya ta fa a tana zare ido ranta in ya yi dubu ya aci. "Auren ne ba a aura ba taron ma ya watse shi ne yake kuka yana cewa wai Alhaji ne ya masa ba inciki" Direban ya fa a dariya tana neman kufce masa ya danne ganin gaba aya abubuwa sun ca e sai ka ce wata dirama ake yi. "To sai mai don ba a aura ba aikin banza da wofi yarinyar da ta gudu yawon ta zubar ko a gida bata kwana ba ai dama ruwa ba sa'an kwando bane, kuma ko da an aura ma arshen alewa asa!" "Ta gudu?" Umar ya fa a a ki ime tare da yin kukan kura ya fisge ri on da direban ya masa sai ga direba wancakar an jefar da shi gefe, yana kwace kansa ya zura a guje ya yi hanyar ficewa daga gidan, hularsa ta yi tsalle ta bar kansa. "Wallahi wani abu ya same shi ka kuka da kanka ragon banza da wofi ka yarda ya jefar da kai gefe kamar wani kayan wanki in baka dawo da shi yanzun nan ba a bakin aikin ka" Hajiya ta ce tana zabga wa direban harara. Mikewa ya yi tare da cire takalmansa ya marawa Umar baya, jin za a yanke masa hanyar cin abinsa. Daga nan su Hajiyar suna iya jiyo maganar Umar da arfi yana cewa. "Sai na bi HAWWA yawon ta zubar" Fa a yake tamkar zararre. "Hajiya amma yaron nan yana shaye-shaye ko?" Ma ociyar Hajiya ta tambaya ganin abin da yake ya wuce misali. "Ah bushe-bushe yake ba shaye-shaye ba" Hajiya da maganar ta mata ciwo ta fa a tana aika mata harara da jajayen idanunta da takaici ya sa suka yi ja. An auki kamar minti goma suna tsaye da ita da ma ociyar cirko-cirko ita dai ma ociyar bata ara cewa uffan ba ganin daga tambaya cibi ya zama ari. Ri e take da tsantsa sai huci take ta rasa mai ya sa take ta kiran Baba bai auki waya ba, ta ma rasa takamaimai mai ya sa bai dawo gidan ba tin da an fasa aurin auren, ya barta da ganin tashin hankalin da Umar yake duk zai janyo hankulan jama'a su gane halin da ake ciki. Suna nan tsaye sai ga Lawisa ta sakko daga sama ri e da glass cup mai auke da lemo a ciki. "Hajiyancy uwar amarya da ango" Ta ce tana ar dariya don ita bata san mai yake faruwa ba. "Ubanki ne angon?" "Mai ya yi zafi shi ba wuta ba Hajjaku mutanen saudi arabiya" Ta ce cikin wasa tana kur ar lemon hannunta. Shigowar mai gadin gidan da direba da wasu artan samari guda biyu sun iyo wa Umar cali-cali sai zufa suke na tseren wahalar gudun da suka sha a titi yadda ya hau kwalta yana zabgar gudu yana kiran sunan HAWWA da yar suka cim masa ana hayya-hayya aka kamo shi. "Ango ranar aurin auren ka sha ka yi tatul" Lawisa ta ce tana juyawa ta shige falo don bata iya ganin wannan kayan takaicin ganin ya fusge-fusge yana ambaton HAWWA sai ta auka a buge yake bata san duk zafin so bane. akinsa ta ce su kai shi su saka cike da takaici ana saka shi a akin ta kulle da mukullin tana jin yadda yake dukan ofar, ita kanta ta fara zargin ko dai kafin ya fita aurin auren ya sha wayar ko dai akwai wata a jikinsa wacce bata sake shi ba don lamarin abin mamaki ne da al'ajabi. Tana fitowa za ta nufi angarenta ta samu samarin nan biyu da suka taimakawa mai gadi da direba aka shigo da Umar suna tsaye. Hatara ta wurga musu ta ce 'Tsayuwar mai kuke ko ganin waf?" "Sallama muke jira" "Sallamar uban me, saboda kun kamo Umar in ne har sai an biya ku? Sai ka ce wanda kuka kamo ra umi ko doki?" Sumi-sumi suka fice suna jan Allah ya isa a zukatansu su dama sun auka za a basu wani abu shi ya sa suka zage suna zabgar gudu har aka ci nasarar kamo shi aka kawo shi gida. Falo ta koma duk tanta a jagule ma ociyar tata ce take bata baki, waya ta auka ta dokawa direban nan ta ce ya zo ba a auki minti uku ba sai ga shi ya shigo. "Wai Alhaji a masallacin can wajen aurin auren kuka baro shi? Ina ta kiran wayarsa a kashe" "Alhaji fa yana asibiti... "Yanzu fisabilillahi maimakon ya zo gida ana bu ayarsa ya wuce dubiya asibiti" Ta katse shi ba tare da ya kai aya ba. "Jiki ya yanke ya fa i a wajen aurin auren fa aka kwashe shi aka tafi da shi asibiti bai san ma a wanda yake kanshi ba, shi ne taron ya watse ba a aura auren ba" "Ya fa ai innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu tsakani da Allah ka san Alhaji yana can asibitin amma baka fa a mini ba ka barni gaho a nan ina aikin banza da wofi har da wani cewa aka kwashe shi ba za ka ce aka taimaka masa ba" Ta ce lokacin da ta mi e tsaye daga zaunen da take tamkar ta kai masa duka shi da ba shi ya kai zomon ba rataya aka bashi. "To fa! Iko sai rabbani su Baba ko dai lokaci ya yi" Lawisa ta ce cikin halin ko in kula. Wani dundu Hajiya ta sakar mata a baya har sai da ta gantsare. "Shegiya marar tarbiyaina zaman zamana za ki jaza mini takaba to a bakin ki" Ta ce tana nufar hanyar fita ankwali yana neman fa uwa duk ta rikice. Ita da ma ociyar tata suka shiga motar direban ya ja suka nufi asibitin don Lawisa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa sai ma haushin dukan da Hajiya ta mata tana jin ba don ba don ba da sai ta rama dukan amma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!. A harabar asibitin ya tsayar da motar tun kafin ya gama fakin Hajiya ta fito hankali tashe ma ociyarta ta bi bayanta hango wasu abokan Alhajin a tsaye cirko-cirko daga can an nesa da su wurinsu ta nufa hankali tashe tana tambayar ya jikin nasa ko dai mutuwa ya yi nan suka shiga bata ha uri da kwantar mata da hankali a kan cewa yana nan da rai kawai
Chapter 25 · 0% Book details