Sashe 18
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matar ubansu ta sako su a gaba basu da anci uban nasu ma bai damu da su ba. Kin san mata nu ne natsalar kan mu da kan mu, idan kika samu yara gidan ubansu don kin aure shi maimakon ki rike su da amana amma sai ki au tsana ki ora musu kike kishi da su kina gana musu azaba na yi da na sanin fitowa daga gidan aurena ga shi na yi saki na dafe a kan karamin abu na kasa hakuri har sai da na ga na kashe auren yanzu abin yana damuna na yarda duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba zai godewa azabarsa, yanzu ina so in koma in rike yarana amma bani da wannan damar" Ajiyar zuciya SALIMAH ta sauke jin abubuwan da RUKY ta zayyano mata, duk da bata wani ji maganar ta shige ta ba amma dai ta ji babu da i amma tunaninta ya bata cewa RUKY don ba ta kai ta kyau da diri bane ta kasa samun tsayayye amma ita tana ganin babu mai kawo mata wargi a nata zawarcin. 09013181851 [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RU IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 8 *ABBAS* Ya sha yaki da zuciyarsa kafin ya samu zafin so da na rabuwa da SALIMAH ya sassautu a zuciyarsa haka ya danne ya hakura ba don ya so ba sai don haka Allah ya tsara masa kaddararsa kuma bai isa ya guje mata ba. Sai da Mama ta dage da addu'a da nasiha sannan ta samu ya dawo hayyacinsa, addu'a sallar dare da karatun qur'ani wanda ya kasance magani kuma waraka ga dukkan komai, a hankali nutsuwa ta saukar masa a ruhinsa har ma ya ji son na SALIMAH ya kwanta masa a zuciya tun da yanzu sai ya wuni ma bai fi ta fa o masa sau aya a zuciya ba kuma ko da ta fa o masa yana kokarin kawar da tunaninta a zuciyarsa, da kuma nesanta kansa da yake sa zaman ka aici domin zaman ka aici yana sa mutum yake tafiya tunani. Gaba aya kayansa na gidan ya kwashe su ya kaura gidan Mama, dama yanzu ku in hayar ma ya kare, ganin ya dawo daidai sai ya aura amarar komawa bakin aikinsa, tare da kudurtar zai yi aiki tukuru tun da yanzu babu wani mai aga masa hankali ba kamar a baya ba idan zai tafi aiki ta aga masa hankali haka idan ya dawo yana wurin aikin zuciyarsa bata huta ba. Sai dai kash! Duk buri da kudurin da ya ci na yin aiki sai da ya je wurin ya tarar da abin da ya karya masa zuciya, wato kayan gadon da SALIMAH ta je wurin ta siyar, da kujerun ko kallon wurin ya yi sai ya ji wani rauni a zuciyarsa, musamman idan ya kalli kujerun sai take masa gizo yana hangota zaune a k an kujera kamar yadda yake samun ta idan ya shigo gida. Ko mudubin ya kalla hangota yake tsaye tana gyaran gashi kasancewarta ma'abociyar gyara gashinta. Da farko ya yanke shawarar canja sana'a sai da FAROUQ ya hau kansa da fa an yana nuna masa ita tana can ta manta da shi amma shi yana nan yana wani maganar fasa sana'arsa saboda kawai ya ga kayan akinta, ita kuwa dama SALIMAH da gayya ta yi hakan saboda tsabar rashin tausayi. Irin furucin da FAROUQ ya yi ta amfani da su hakan ya saka ya dake zuciyarsa sai ya zo wurin ya tafi ma amma bai ko kalli kayan ba har aka zo ga ar da ko ya kalli kayan ba ya jin komai, har dai Allah ya kawo wanda suka siye kayan ma ko a jikinsa ma lokacin don yanzu kam ya fara aniya da amarar haka rami ya binne duk wani son SALIMAH da yake addabar zuciyarsa. Aiki yake tukuru a rana sai ya yi aikin dubu goma kasancewar yanzu ba shi da wata damuwa sai wacce ba a rasa ba, sa anin da idan ya zo hankakinsa yana gida idan ta kira ta a waya ba za ta aga ba idan ya dawo gidan ma babu kwanciyar hankali wannan dalilin ya sa yanzu ya kara gane cewa ka samu mace ta gari mai sonka wacce za ta faranta maka shi ne samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. *HAWWA* Kwana biyu a tsakani da faruwar abin na ganin kwalabe giya a akin Yaya Umar sai ga shi ya shigo gida da gabannin magrina a buge ya sha giya ya yi tatul. Sosai Hajiya ta shiga tashin hankali tana kuka wiwi kamar matar marigayi. "Na shiga uku yanzu Umar abin naka har ya kai ga shan giya? Ni duk tunanina an kodin nw kawai kake afawa ashe har da giya da kwaya wannan wace irin rayuwa ka sa kan ka?" Ta ce tana rusa kuka ganin ya kwanta male-male a tsakiyar falon yana ta wani surutai cikin muryar bugaggu ga kuma kwaya nan da tje jimke a hannunsa. "Ke ma in za ki sha kwayar ai sai ki kar a ni ba hana ki zan yi ba, akwai ma giyar a akina a kasan gado sai ki akko ko da kwalba goma kike so" Ya ce cikin muryar maye yana mika mata kwayar. Jin furucinsa na cewa akwai kwaya a gidan sai hankalinta ya kara tashi, ko ta kan kwayar da yake miko mata bata bi ba ta yi hanyar akinsa a ki ime cikin tashin hankali tana zuwa ta ga akin a rufe a 360 ta dawo duk ta fita hayyacinta wannan ahi ake kira tashin hankali wanda ba a saka nasa rana da lokaci. Cikin kukan ta da ta kasa rikewa ta kama wandon Umar in ta saka hannunta a aljihinsa za ta akko mukullin akin nasa. "Wai waye yake saka mini hannu a aljihu zai mini sata, to wallahi zan sa kulawa( an sanda) Su kama mutum" Ya ce yana mika hannu ya dafe hannun Hajiya da yake aljihu za ta akko mukulli. "Ubanka ne, na ce ubanka ne, sakaran banza da baka san inda yake maka ciwo ba" Ta ce lokacin da ta saka aya hannunta ta aka masa duka a hannun da ya danne hannunta da yake cikin aljihu. Yana auke hannun ta zaro mukullin da kuma wasu kula-kulai da wani abu da ta kasa gane mene ne, sai dai mai, tana fitowa da hannun ta ga mugun abin da ya kusa tarwatsa zuciyarta, condom ne da kuma sarkarta da an kunne na gwal da suka he dubai ta siyo wacce ko sakawa bata yi ba. Hannu ta ora a kanta ta shiga runtuma ihu tana ambaton ta shiga uku. Zaman dirshan in da ta yi a wajen tana rasgar kuka tamkar an mata mutuwa, cikin kukan ta tafi da rarrafe ta auki wayarta da take kan kujera da dokawa Alhaji kira, sai dai har ta tsinke bai aga ba, kiransa ta yi a karo na biyu ringing aya biyu ya aga, kuka kawai take ta kasa cewa komai, Alhaji jin kukanta ya shiga tashin hankali don ya auka ma mutuwa aka yi. Ganin ta ki cewa komai sai ya kashe wayar yna yi wa direbansa umarni a kan ya yi sauri akwai matsala a gida, abokin sa da suke tare a bayan motar ya shiga tambayarsa amma sai ya ce shi ma bai san mene ne ba. A ki ime suka shigo gidan Baban a gaba abokinsa yana biye da shi suna sauri tamkar su kifa, tun da suka doso gidan suke jiyo ihun kukanta, falon suka nufa suna zuwa suka ganta zaune dirshan tana kuka. Baba rasa bakin magana ya yi don ahi tsabar tashin hankali da rikicewa ko lura bai yi da Umar da yake yashe a falon ba amma shi abokin Baban ya gan shi. "Yawwa kulawa kun iso ku mini ram da wannan arauniyar ta sace mini makudan daloli a aljihu" Maganar Umar ce ta ankarar da Baba. "Hajiya wai mene ne kike kuka kika tada mini hankali?". ."Yanzu Alhaji baka ga abin da ya saka ni kuka ba?" ."Ina yake?" Ya tambaya cikin rashin fahimta. "Wai har tambaya ma kake? Kana ganin Umar a buge" Wani dogon tsaki ya ja kafin ya ce .."Wai a kan wannan ne kike kukan in ce dai kin da e da sanin yana shaye-shaye to mai zai aga miki hankali ne har kika aga mini nawa hankakin" "Giya ce fa ya sha" "Giya???" Ya tambaya hankali tashe yana rarraba ido. "Giya ya sha, kuma ya ce akwai ta a akinsa ko kwalba nawa ake so akwai a kasan gado, zan je in akko na ga akin a rufe shi ne na dawo zan auki mukulli a aljihunsa, ina saka hannu na samu sarka da ankunne na wanda na siyo a dubai kimanin miliyan uku ya auka, yanzu Umar mashayin giya kuma arawo " Ta ce tana rushewa da kuka. Gaba aya gumi ya jika Alhaji. "Kai kuna tsaye gaban manya kowa ya kama kunnensa dole a ladabtar da ku... Kafin Umar in ya kai karshe maganar Baba ya karasa gabansa ya aga hannu ya wanke shi da mari, da sauri abokinsa Alhaji Khamis ya rike shi yana ba shi baki. Sosai hankalin iyayan ya tashi amma sun manta cewa su ne suka bar kashi tun ran kwasa, domin tun ran gini ran zane. Sun sangarta a babu kwa a babu tsawatarwa komai suka yi daidai ne da wayewa sai yanzu da abubuwa suka ca e ne suka gane wautar da suka yi. Karasawa ya yi ya zauna a kujera yana ta faman huci basu san ta ina za su fara ba don lokaci ya kure musu ita tarbiya tana farawa ne daga gida duk abin da yaro ya yi ka tsawatarsa masa, ka nusar da shi itace tun yana anye