Sashe 21
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta tarar na gawar mahaifan nasu ya haifar mata da suman da sai da ta kwanta asibiti, ganin su kwance babu kyan gani yadda tukunyar gas ta yi bindiga suka kone har da wasu daga cikin ma'aikatan gidan. Hannu ta saka ta sharenhawayen da suka gangaro mata tana jin tamkar yau abin ya faru. A oye Baba ta kawo mata ku in zobe kulle.a bakar leda dubu ari biyu da hamsin da yake zoben da girmansa. Dubu ari ta ba Baba wanda dakyar ta kar a shi ma saboda HAWWA ta nuna mata ku in ya musi yawa. Da za su kwanta Baba ta musu sallama saboda gudun kar ta fiya zama tare da su zargi zai shiga idan aka neme su aka rasa. Tana jin babu da i rabuwar da za su yi. Tsakiyar dare wajen karfe biyu HAWWA ta tashi ta auki ruwan da ta ajiye a kofi ta zuba a hannunta ta shafawa SABEER a fuska yana warewa ta shiga ra a masa cewa za su tafi saboda dama ta fa a masa cewa za su gudu Kaduna gidan Baffa Nasiru. Yanzu murna yake don haka ku in ta saka a wata karamar jaka marar nauyi da Baba Sadiya ta bata ta ce ta saka, sai da ta goye shi a bayanta ta rataya jakar a wuyanta ta tsaya ta yi ta addu'a a kan Allah sa su fita ba tare da wani ya gan su ba. Dama tuni ta zari mukullin kofar da za ta sada ta da get in gidan haka ta fito cikin san a ta fara lalla awa har suka zo kofar gabanta yana ta fa uwa ta saka mukullin ta bu e a hankali ta fita ta ja kofar wurin mai gadi ta nufa da yake sharara bacci da munshari tana zuwa ta shiga dube-dube cikin ikon Allah sai ta ga mukullin a cikin hularsa ta ga mukullin ta lalla a ta auka ta bu e get in suka fita cikin san a ta ja musu get in. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ganin sun ku uto daga gidan, sai dai inda gizo yake sakar tana fatan su samu mafaka kafin da asuba su nufi tashar motar. A wani kango suka samu mafaka inda suka yi addu'a suka shiga saboda gujewa abu mai cutarwa. A nan suka karasa kwanan da asubar tun gari bai yi haske ba suka fito wannan karon hannun SABEER ta kama suka kama hanyar tashar. Sai da suka kusa sannan suka samu napep kai su suka yi sallah ganin mota za ta tashi suka shiga motar ta tashi duka lokacin shida da rabi, sai da ta ga sun aili hanya sannan ta sauke ajiyar zuciya tana rungume da SABEER wanda bacci ya yi awon gaba da shi kasancewar jiya basu samu wani bacci ba. *SALIMAH* Da tsananin murna da farin ciki wanda bashi da kwatankwaci ko misaltuwa da lokacin fa kwanakin iddarta suka cika, domin a wannan lokacin ne take ji ba ya ita domin ta samu cikakken anci, anci wanda take jin tamkar na wanda yake gidan yari ya samu fitowa daga ciki. A ganinta a yanzu ne take ganin tama da damar da za ta dama wacce ta da e tana jiran zuwanta a inda za ta ci karenta babu babbaka. Don tun da ya sayi kaya ta yi inkuna na kece raini inkuna na fita taro take jin kanta yana hayaki take jin kanta daidai da kowace shegiya da take jin ta samu dama. Kayan da suka janyo mata farin jini ha e da kwarjini, kayayyakin da take shiga ta kece raini wacce ta kara fitowa da aji da mugun kyan da take da shi wanda a da take ganin talauci ya yi wa mutane shamaki da ganin kyan nawa kasancewar tana gidan ABBAS babu kayan da za ta yi tinkaho matsayinta na babbar yarinya amma yanzu tana ganin buri da mafarkin ta zai cika na zama matar manya. Tun da ta yi idda ta fara ba mazan da suka yi mata caaa suna son samun dama a wajenta kasancewar bata yi idda ba sai ta an dakatar da su amma tana kammalawa sai ta shiga ranga a musu kira ta wayar salula da yake tana kar ar lambobinsu. Hakan ya sa lokaci kankani ta sha kwana kamar yadda ta yi tsammani. Manyan mutane ne masu hannu da shuni suka fara rububin aurenta wannan ne ya sa ta karyata maganar BASEERA, da kuma RUKY don yanzu dai ga maza nan kowa yana so ta bashi dama ya dama, kowa yana bayyana mata irin tsantsar son da yake mata tare da ko a irin baiwar kyawun da Allah ya mata. Wannan ya sa kanta ya fashe take ta jin takaici da ta kare a gidan talauci bayan ga rayuwar da ta dace da ita duk da tana ganin lokaci bai kure mata ba. "RUKY kin ga abin da nake fa a miki ko, zawarci ya danganta da irin kyau da aji da kuma iya kamun ludayin bazawarar yanzu dai idanunki sun gane miki dama bahaushe ya ce gani ya kori ji, kina gani har gajiya nake da amsa kiran maza a wayata kuma kaf cikinsu babu na jefarwa kowanne yana takama da dukiya yana kuma ji da kansa, kowanne yana nuna mini so da kauna da kulawa ga su wayayyun maza ba kamar wancan fakirin da na baro gidansa ba ga bakin talauci ga kansa kife a cikin kwarya ba ma tukunya ba" "SALIMAH ba za ki gane bane, ai fa haka suke fitowa a farkon zawarci ai kamar budurwa ce da za ki ga farkon fara budurcinta za ki ga maza gasu nan manema kamar me amma da ka an-ka an za su watse sai wanda yake da gaske da aure yake sonta shi ne zai tsaya. To zawarci ma haka yake farko ga mazan nan kamar jamfa a jos amma tafiya in ta yi tafiya za su zame su barka wani dama rage dare yake zuwa kuma ABBAS ai wayayyan mutum ne ke ce baki bashi damar nuna miki kulawa ba da kin ba shi da sai ya mayar da ke sarauniyar mata" "Hahahaha ni nawa ba irin na kowa bane, yadda nake mai kyan nan babu mai yarda na kufce masa, kuma ki daina kira mini sunan mutumin nan don muna iya yin uwar watsi da ke yanzu" Ta ce tana wani yatsina irin na wanda duniya ta aga, ko ka an ba ta tunanin akwai ranar da duniya za ta nanata da kasa don ta ga yanzu tana murza kambunta yadda take so. "Allah baki hakuri kawata kin san ni ruwa ya karewa an kada shi ya sa nake ganin kamar kowa ma haka ne" "Ban da kowar wake, ki bi sannu ki dangwali arziki ki bar shi nan, ni nawa zawarcin mai lasisi ne, kuma arzikin auren da zan yi sunansa kogi mai gudana wanda ruwansa ba ya ta a kafewa" Ta ce tana saka hannu a jakarta pink wacce ta yi macin da leshin jikinta mai ratsin pink da takalmi da mayafinta. Dubu ashirin ta lissafa ta ba RUKY godiya ta mata tana ta mamakin yadda zawarawa suke wa SALIMAH arin ku i tamkar basu san ciwonsa ba. "Kina lokaci!" i ki kara RUKY ban rasa komai ba ga iphone 16 ga keypad hr biyu ga android nan kina dai ganin hannun Umma ita ma tana rike wayar dubu ari biyu da ashirin ai mu kam mun yi ban kwana da talauci" "Na ga Umma ita ma yanzu ba kowa take kulawa ba, ranar nan yarinya ar makotanmu ta je siyan koko da kosai da sassafe amma ta yi ta buga gidan ba a bu e ba wai sai ma karan jannareto da take ji har safe ba a kashe ba" "RUKY kenan ai mu da sana'a sai dai mu ga ana yi, kina dai ganin yadda aka gyara mana gida kai gaskiya ku i ya yi a rayuwa mai ku i bai kwana da haushin kowa ba" "Wai yanzu a cikin mutum ukun nan da kike ji da su duk cikin zawarawan ki, Alhaji Tahir, Alhaji Mubarak, Alhaji Abdullahi wanne za ki aura? Kowanne dai ji yake da ke kuma burinsa ya zama gwani wato zakaran gwajin dafi" "Lokaci zai nuna" Ta ce tana jin kanta saboda ta san a halin yanzu ita allurar ruwa ce mai rabo ne zai auka. *BAYAN WATA GUDA* Tafe suke a mota ita da Alhaji Tahir da ya zo suka je ya mata siyayya, suna hirar soyayya abin su, saboda ta nunawa ABBAS cewa ga irin matsayin da ta taka yanzu ta saka Alhaji Tahir in ya biyo ta wajen kafintocin da ABBAS yake aiki wai za ta saya kujerar yar tsugunno irin ta tsakar gida, wai Umma ce ta ce ta siyo mata kuma kawai don ta kuntatawa ABBAS ne ta san in ya ganta hankalinsa zai tashi, shi kuwa Alhaji Tahir ya amsa mata da "Ranki ya da e tauraruwar mata an gama ai sai yadda kika ce za a yi, matsayinki ya fi haka" Ya ce yana wani ko a ta, wani murmushi ta yi wanda ya kara bayyana kyan ta, a daidai wajen ya gangara gefen hanya ya faka motar har yana cewa ta zauna ya fita ya siyo da yake bai san manufarta ba sai ta nuna masa ai Ummar akwai kalar wacce take so. Fita ya yi daga motar ya kewaya zai bu e mata don ko yaushe shi yake bu e mata ta shiga haka idan za ta fita ma. Sosai ta ki da i domin kuwa tarkonta ya kama, hango ABBAS yana ta yanka katako sai gumi yake ga shi inda suka tsaya saitinsa ne dole idan za ta fito zai ganta. Zagayowa Alhaji Tahir ya yi ya bu e mata kofar fararen kafafunta ta ziro wanda suke sanye cikin goldin in takalmi, a adaidai lokacin wayar ABBAS ta yi kara ya fito da ita daga aljihu zai amsa kiran, a hankali ta fito sanye take cikin doguwar rigar bakar atamfa mai goldin, ta sha aurin ankwali mayafinta yana yafe a kafa arta da yake yau yafawa ta yi ba kamar kullum da take sakalawa a gefen kafa a ba ta yi bala'in kyau la