Sashe 4
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
an zo wajen da bai ji zai iya ba dole ya yi hukunci dole ya au mataki a kan wannan mummunan laifin da ta aikata masa tana ikirarin shi juya ne ta sanya yake bin asibitoci yana biyan ku in gwaji ana tabbatar masa da lafiya yake ashe dai ga miciji amma yana abin ja. Bai san lokacin da hannunsa ya auki hanyar fuskar SALIMAH ba sai gani ya yi ya wanke kyakkyawar fuskarta da wani wawan marin da sai da ta ga gilmawar taurari. MAMAN AFRAH 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ka/ki ya yi daidai da labarin ki to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah ya saka da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 2 Cike da tsananin mamaki take duban ABBAS jin yatsun sa biyar a fuskarta. Bakinta take son motsawa amma ta kasa bu ewa bare har ta ha a haruffan da za su zama kalaman da za ta furta. Shi kuma ABBAS sai a sannan ya gane kato arar da ya yi. 'Ai ni wallahi ba a yi a namijin da zai kai hannunsa jikina ba, duk ranar da giggiwar namiji ta saka ya dake ni wallahi yana sauke hannunsa ina aga nawa, kuma daga ranar ya daki aurensa wallahi don ko kai ne autan maza na bar ka bari na har abada ma kuwa' Maganar wata mata ta fa o mata a rai wata rana a gidan biki tana tsaye take jiyo maganar wasu mata guda uku da suke jajantawa wai kawarsu mijinta ya mata shegen duka. A ranar da SALIMAH ta ji tattaunarwar su take kiyasta to ita wane tsautsayin ne zai sa namiji ya kai hannu jikinta ita bata yi kalar matan da za a duka a gidan aure ba, to kuwa tabbas shi ma da ya daki auren nasa bare kuma ita dama da take neman makala wato ABBAS lallai yau mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki. Sai da ta shammace shi ta aga nata hannun ta sauke masa a fuska. Al'ajabi ne ya hana shi yinkurin komai don bai ta a zaton SALIMAH za ta iya dukansa ba duk da shi ne ya fara ta a lafiyarta amma dai abin akwai mamaki. "SALIMAH ni kika mara?" "An mare ka who are you?" Ta ce cikin halin ko in kula. "Kuma idan har ka haifu an halal ba shege ba a cikin iyayanka to ka sawwake mini" "Na sake ki saki aya SALIMAH" "Ayyiriri yiriiii" Karan gu ar da ta saki ne ya dawo da shi hayyacinsa tare da ankara da abin da ya yi. Sai dai kalmomin da ta yi amfani da su wajen kar ar sakin ne sun zafafa sun rura masa wuta a zuciya, sai dai ba zai ce bai shiga ru ani da tashin hankali ba na kalmar sakin da ya furta mata wacce ta fito daga bakinsa tamkar an fisgo ta. Yaraf ya zube a kan gwiwoyinsa don ya san SALIMAH ta su uce masa su ucewa ta har abada kuwa, sai dai ya auki na annabawa amma da wuya ta yarda ta dawo gare shi domin abin da take nema ne shekara da shekaru ya samu. "Innalillahi wa inna alaihi raji'un" Ya fa i hakan a fili sai dai kafin ya ankara har ta fita daga akin ya san kuwa zancen gizo ba ya wuce na koki ma'ana zuwa za ta yi ta ha a kayanta. Da as ya zauna ya ha a kansa da gwiwa yana jin yadda gabansa yake bugawa gaba aya ya rasa ma wane tunani zai yi shi yunwar da yake ji ma bai san ta inda ta bi ba saboda wani ciwon ya danne wani zafin rabuwa da masoyi ya fi gaban wasa. SALIMAH kuwa wani irin da i da farin ciki take ji, ji take tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, har da wata rawa ta taka a akin kayanta ta shiga ha awa a wata babbar jaka sai da ta cika ta taf da sauran kayan amfanin da za ta bukata, kafin a zo kwasar kaya, rigar jikinta ta sauya ta yafo mayafi ta akko jakar ta fito a kofar falon ta ajiye jakar ta shigo falon domin aukan waya, jin shigowar ta ya tashi tamkar an tsikare shi yana jin da na sanin abin da ya yi. Cajar wayarta ta auka da kuma wayarta kallo aya ya mata ya gane tsantsar farin cikin da take ciki. "ABBAS saduwar alkairi Allah ha a kowa da rabonsa yau ka biya ni" Ba ta jira cewarsa ba ta banka a labulen ta fita ta auki jakar sai ga shi kamar an watso shi duk ya firgice sai ma ta so ta ji tausayinsa amma dai ganin bahaushe ya ce so, so ne amma son kai ya fi sai ta ji ta fi tausayawa kanta a kan shi. "SALIMAH don girman Allah ki yi hakuri" "Wa? Ai in ka ganni a lahira kai ni aka yi" Daga haka bata jira cewarsa na ta juya ta fice, zaunawa ya yi a kasa yana jin zuciyarsa tana suya tabbas in akwai abin da yake kaddararsa kuma jarabawarsa to bai wuce son SALIMAH ba, akwai lokacin da ta yi yaji ta ki dawowa ba tare da wani dalili ba dama mahaifiyarta ma ba kaunar auren take ba Babanta ne mai son auren kuma ya mutu. Tsawon sati biyu ta yi bata gidan amma sai da ya kwanta jinya hatta aikin kafinta ba ya fita, wata rana idan ya je gidansu SALIMAH aka ki kula shi kan maganar bikon sai ya zauna a kofar gidan ya wuni sallah ce kawai take tashin sa daga wurin idan ya yi ya dawo saboda kawai jurewa ya yi ta yi amma ya san ya azabtu da rashinta. Wasu hawaye ne masu zafi suke masa ambaliya a fuska tabbas ba kowa zai gane irin hali da ra in da yake ciki ba sai wanda yake cikin halin da yake ko wanda ya ta a shiga irin halin. 'A kullum addu'a ta shi ne in rayu a duniya aya da SALIMAH duk duniyar da babu SALIMAH sai in ji tamkar dai makabarta ce, amma yau kaddara ta gifta kaddara wacce take rubutacciya don in ba kaddara ba ba na jin akwai ranar da ni da bakina zan furta kalmar saki ga SALIMAH amma rubutacciyar kaddara wacce ba ta goguwa domin irin wannan kaddarar ita ce ake kira kaddara wacce ta riga fata, na san wasu za su ji haushina wani ya ji kamar ya hau ni da duka wani kuwa zai ga ai so ba hauka bane sai dai kash! Bai san irin inbin so da kaunar SALIMAH da suke dankare a tawa zuciyar ba ni ban ta a cin karo da irin son da nake yi wa SALIMAH ba, ko da kuwa a labari ne son da nake mata ya fita da ban ya fi karfin zuciyata, da ce SALIMAH za ta bukaci in aye fatar jikina in bata babu wani dalili da zai sa in kasa ko da za a saka bakin bindiga a kaina a ce in sake ta ko a harbe ni, to tabbas ba zan furta mata kalmar saki ba amma yau tsautsayi wanda ba ya wuce ranar sa ya sa giyar fusata da gajen hakurin acin rai da kasa jure kalamanta uwa uba shai an mai amfani da dama idan mutum na cikin acin rai ya ci galaba a kaina' Ya furta a zuciyarsa yana ha a kai da gwiwa ji yake duniya ta masa kunci tabbas yana cikin matsatsi. "Don Allah ki dawo gare ni SALIMAH" Ya furta a fili da karfi har jijiyar wuyansa tana bayyana ra o-ra o, yana mai fashewa da kukan tausayin kansa. *SALIMAH* Cikin wani farin ciki ta fito daga gidan kofar gidan ma a bu e ta bar ta ko darajar rufewa bata samu ba, ji take tamkar ta taka rawa ji take rabon da ta ji ta cikin annashuwa tun ranar da aka aura mata aure da ABBAS, tun daga wannan rana ta tsinci kanta cikin wani yanayi tun daga wannan rana wani abu ya tokare mata makoshi abin nan da ya tokare ta bata ta a jin ya gushe daga wurin ba sai yau da ABBAS ya furta mata kalmar saki abin dai tana jin sa kamar almara sannan kuma sai take jin tamkar a mafarki. Duk da soyayya suka yi da ABBAS in sai dai ita ta kauna ce shi ne saboda kyau da yake da shi duk cikin maneman ta babu wanda yake da kyansa, kuma babu wanda ya ha a duk abin da take bukata daga a namiji kamar ABBAS su dai sauran ku i da manyan motoci da gidaje za su fa a masa shi kuma Allah ya mallaka masa komai da mace za ta so ga a namiji matsalarsa aya cikas insa aya mugun talaucin da ya kananna e shi ya masa dabaibayi. Manyan alhazan da take kulawa masu hannu da shuni suna kashe mata ku e jikinta suke so, don sun sha zuwa mata da kalmar atanci amma ta ki bada ha in kai, shi kuma ABBAS kaunarta yake da gaskiya wannan dalilin ganin yana jumuri da jure duk wani abu da za ta masa kuma nutsatstsan matashi mai girmama na gaba, uwa uba ibada da tarbiya hakan ya sa mahaifinta ya dakatar da kowa daga zuwa wurinta ya ce ABBAS zai aura mata. Ta yi kukan bakin ciki tun daga ranar ta ji ta tsani ABBAS kyansa da take gani ya koma mata muni domin ta fi kaunar ku i da morewar rayuwar duniya a kansa. Kamar kumbo kamar katanta yadda abin nan yake a wajen SALIMAH haka yake a wajen mahaifiyarta, bakin su aya ita ma duniyar ce a gabanta, don duk abin da mahaifin SALIMAH zai fa a mata a kan rayuwar duniya da bin duniya a sannu da dai