← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 43

Sashe 7

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

karo musu, suka kara cinyewa sannan ta mika masa ruwa shi ma a baki. "Haba Mama aikin ai ya miki yawa ruwan ma sai kin bani a baki" Ya ce yana dariya har hakoransa suka bayyana. Ita ma dariyar ta yi ta ce "Ai gwara in karasa laifina, na bada abinci ma bare ruwa" Haka ya bu e baki suna rike da kofin a tare har sai da ya ago kansa alamar ya koshi sannan ta shanye sauran. "Mama saura nawan kika shanye?" "Ai uwa ba ta jin tsantsanin anta" Sosai suka ringa hira cikin farin ciki tana ta jan shi da hira tana bashi labarai don ta kawar masa da damuwa, domin ya ce ba zai koma gidansa ba a nan zai kwana. akinsa na da ta shiga ta share masa, katifarsa ce a ciki sai sallaya da qur'ani. Tana dawowa ta ga ya yi nisa a cikin tunani da haka ta ce ya tafi akin ya kwanta, a can ma zuwa ta yi ta zauna har sai da ta ji ya yi iff alamar bacci ya auke shi ta fito ta tafi nata akin. ABBAS kuwa dama ba bacci ya yi ba ya yi hakan ne don ta je ta kwanta ta huta kuma idan ta ga ya yi baccin za ta rage damuwa amma idanunsa biyu. Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kamo sunan SALIMAH "Duniyata" Shi ne sunan da ya yi saved da aya lambarta, ya da e yana kallon sunan amma sai ya kasa kira domin tsoron abin da zai biyo baya, watakila ta ki auka ko kuma ta auka ta fa a masa maganar da za ta tada masa mikin damuwar da ya ji ya kwanta masa. Har wajen karfe biyun dare idanunsa biyu, fitowa ta yi ya yi alwala domin zuwa ya yi nafila haske ya hango a akin Mama ya san ita ma kuma sallar take don tun yana yaro haka ya ga suna tashi da Babansa suna nafilar dare idan ya falka bacci, kuma ko yanzu ma ya ga inda ta yi alwala da butar a wajen. Sai da aka kira asuba sannan ya tashi daga kan sallayar ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari ya yi haske sosai ya ji damuwar ta ragu. Da ya dawo ma bai kwanta ba sai ya auki qur'ani ya shiga karantawa cikin kira'arsa ta Ahmad Sulaiman wanda tun suna islamiya an ajin su suke cewa suna son kira'arsa ko malamin su idan ya zo kar at harda sai ya yi ta saka ABBAS maimaitawa in ya gama bashi hardar ya ce ya kara maimaitawa ba don akwai kuskure a cikin karatun ba sai domin da in kira'arsa. Shi kuma tun yana karami Mama take kunna karatun Ahmad Sulaiman in sai ya taso da son zama kamar shi, kullum in ta kunna sai ya ce. "Mama ina son zama wannan malamin idan na girma, ina so in iya karatu irin nasa" Sai ya zamana ko surorin kasa da take koya masa sai ya ce sai ta masa kira'ar malamin haka take koya masa da kira'ar shi ma yana yi wannan ne mafarin koyon kira'ar idan yana yi tamkar Ahmad Sulaiman in ne yake ga ba wa kowane harafi hakkinsa, shi dama yaro yana tashi ne da abin da ya ga mahaifiyarsa tana yi, idan mai kyau ne haka zai ke yi in akasin haka ne ma koya zai yi saboda yara sun fi aukan abin da suke gani ana yi fiye da wanda ake koya musu ko ake umartarsu su yi.
Chapter 7 · 0% Book details