Sashe 9
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zauna, Khalid ya russuna ya gaisheshi. Shi kuwa ya amsa idanunsa a kan Hajiya Saudatu, can kuma ya dubi dansa. "Ban lamunci ka biyewa shirmenta ba, ba kuma zan dauki sakarci ba. Ka je ka yi tunani, duk wacce ka za6a a duk inda take, ka je ka sanarwa . Allah Ya za6amaka mace ta gari. Tashi ka je." Ya amsa da amin san nan ya fice yana jin yanda Hajiya ke bambamin fadan ba ta lamunta ba. Baba Hamza ya dakamata tsawar da sai da hanjin cikinta suka kada, tunda take da shi bata ma ta6a ganinsa ya fusata haka ba, hannunsa har rawa yake ya nunata da yatsa. "Ki kiyayeni Saudatu, kina cin darajar yaranmu ne shiyasa nake dagamaki kafa. Ki kiyayi ranar da dubunki za ta cika a wurina. Wallahi alokacin za ki fahimci shayi ruwa ne!" Daga haka ya sa kai ya bar falon zuwa 6angarensa, ta bishi da kallo, inda Allah Ya taimaketa ma yaran nata duk suna can 6angaren Mama Zahida, ai da ya disgata. Tunowa da tayi da furucinsa ga Khalid ya sa ta fusata ainun, waya ta dauka ta aikawa Khalid sako cewar muddin ya ki bin umarninta toh fa za ta iya cireshi a jerin 'ya'yanta saboda bata kaunar abinda zai had'ata da zuri'ar Bara'atu. Ta furzar da wani huci mai zafi, wane irin zagi ne ubanta bai mata kan Bara'atu ba? Har kusan tsinemata ya yi saboda ta auri saurayinta ta yaudari aminiyarta. Har gobe ya na fushi da ita. A dangi ma har yau akwai masu gorantamata kan aurewa Bara'atu miji. Wannan ya karamata tsanarta. Don haka babu yanda za'ayi ta bari danta ya auri abinda ya jininsu. Shi kuwa gogan yana shiga bangarensa ya nemi wuri saman kujera 3sitter ya zube. Lumshe idanunsa ya yi sakamakon ciwon kai mai tsanani da ya addabeshi. "Sumayya." Ya furta a hankali tamkar ba ya so, a duniya ba ya zaton akwai matar da zai so kamar Sumayya. Abokiyar karatunsa ce a jami'a wacce suke a aji daya sai dai bambancin shekaru domin ya bata shekaru har biyu, a hakan kuma ta fi shi kokari nesa ba kusa ba. Itace kusan malamarsu a makaranta, tare zasu zauna su yi karatu, abinda ya shigemasa duhu ta kara dorashi a hanya. Su biyar suke harkokinsu a makaranta, ita da kawayenta Naja'at da Nazifa sai Amininsa Dawud. Kusan kowane lokaci su na tare, a hankali kuma soyayya ta shiga tsakaninsa da ita, tun su na dauka kamar wasa har dai daga baya ga sanarmata. Kafin cikar shekara har an sansu tare har akwai masu kiranta Matar KK. Shi kansa yana jin dadi idan an kira Sumayya matarsa. Bayan kammala karatunsu kuwa akai magana gemu da gemu inda iyayen Khalid suka tambayo mishi game da Sumayya. Aka kuma bayar. Shekaru biyu da yin hakan, aka yi aurensu. Babu wata matsala da suka samu wajen auren sakamakon cewar iyayensa da nata suna so. Sun yi soyayya mai zafi, Khalid kusan ma son da yake yiwa Sumayya ya girmi tunanin mutane. Shi kansa yakan yi mamakin irin son da yake mata. Sumayya ta rasu ne a wajen haihuwa daga ita har abinda ta haifa babu wanda ya rayu. Kusan hauka Khalid ya yi domin har daina kula kowa ya yi a gidan. A hankali ana addua ya samu kansa. Wannan dalilin yasa ya guji gidansa gaba daya, ya gwammace ya dawo kusa da iyayensa ya zauna. Shi ne kuma dalilin zamansa a familyhouse dinsu. *** Ya jima zaune yana tunani kafin dakyar kuma ya mike ya shiga daki, paracetamol ya sha ya dauro alwala ya bi lafiyar gadonsa bayan ya kakka6e da abin rufarsa kamar yadda sunnah ta koyar. *** Da sauri-sauri take shiryawa. Ta kammala zura safa kawai sai ta rike takalmin a hannu ta zura silifas dinta. Jakarta tuni Zeenat ta yi gaba da ita. Mami da ke faman korafin ta i ficewa, tana mata adduar sa'a ba ta iya tsayawa ba sai a hakan ta amsa. Tana isa farfajiyar gidan babu mota sai filin wajen. Sai kuwa Yaya Khalid da ke tsaye karkashin bishiyar mangwaro sanye da kayan exercise yana dannomata harara. afafunta suka hau rawa, zata juya ya dakamata tsawar da ta sanyata gigicewa har ta zubar da takalman. Karasowa ya yi gareta yana furzar da huci kamar wanda yayi gudun sati. "Ke wacece da za ki dunga sa yara latti? Don iskanci kullum sai a zo a yita zaman jiranki? To yau sai dai ki fasa zuwa makarantar." Daga nan ya juya abinsa, rai a 6ace ta juya zuwa sashensu. Tun kan ta karasa ta soma kuka har ta isa falon. Mami da ke shirin shiga sashen mijinta sai ganinta tayi. "Ke kuma me ya dawo da ke?" Ta ta6e baki. "Yaya Khalid ne yasa suka tafi suka bar ni." Harararta tayi. "Yo shi ne me? Mene abin kukan? Ai koma mene ke kika janyowa kanki. Kuma wallahi ba za ki zauna ba, saka takalmin ko a napep ki wuce." Daga nan Mami ta dawo ta aga kasan Decoder inda ta ajiye dan chanjinta ta mik'amata tana fadin. "Ina jakarki?" Dakyar ta amsa tana turo baki ita a dole bata huce ba. "Zeenat ta tafi da shi." "Shikenan, gudun kada ta bar shi a mota zan kira shi Yakubun na ce ta tafarmaki da shi aji." Daga haka Mamin ta fice tana bambamin fada. Ita kanta Kurfi tana mamakin chanjawar Maminta a kwanakin nan, abu ma da bai kai ya 6ata ranta ba sai ya fusatata, idan a gaban Abba ne sai dai ya lalla6ata ya ce su yi mata uzuri. Wannan ma kamar kara tunzurata yake. Tunawa da tayi suna da test ya sa ta saurin mikewa a zuciyarta tana adduar bata yafe ba ga Yaya Khalid ta fice. Tun kan ta isa gate ta hangeshi yana kokarin bude mota, tasan wajen Gym dinsu na kata'i zai je. Ita kuwa da saurinta ta fice daga gidan ranta a hade, ko kallonsa bata kara yi ba domin a yau kam ya gaba kai ta bango. Ji take kamar ta karasa ta shak'eshi. Ta ja tsaki ya fi sau nawa sa'ilin da ta ke ta tafiya a titin dake kan layinnasu da zummar isa babban titi neman abin hawa. Wannan ma na daya daga dalilan da bata son unguwa mai shiru irin haka, sai mutum na sauri ya je wuri masu abin hawa su ce ki hau mu a inda kika ganmu. Hon ta ji a bayanta, jikinta ya riga da ya bata cewar shi ne. Kwafa ta yi. "Ai ka yi kadan na hau motarka, dan rainin kwakwalwa!" Ta fada a fili cike da mita, da haka ma sai ta kara sauri tana tafiya tana duba agogon hannunta, ga mamakinta bai kara yi mata hon ba, duk a zatonta ya juya ne. Ta k'i ta juya sam saboda tsaro ba don tsoro ba. Allah Ya taimaketa ta samu abin hawa, fad'awa kawai tayi, kafin mai adaidaita ya ja motarsa ta sha gabansu. Hanjin cikinta sai da ya kada tsabar tsoro. Fitowa ya yi ya dubeta kamar zai kai mata bugu. "Sauko!" Ganin a tsawance ya fadi babu wasa ya sa ta saukowar babu shiri. Mai adaidaita bai jira komai ba ya yi ribas ya bar wajen. "Shiga muje." Tana turo baki da kunkuni haka ta karasa ta zauna gaban motar. Shi dinma shiga ya yi ya ja da gudu kuwa wanda har sai da ta yi gaba ta koma baya. Ganin haka ta daura seatbelt. 'Jarababbe, ya kare a kanka dai.' Ta furta zancen a can kasan ranta. A fili kuwa hawayen takaici ta soma, babu komai da ke tashi sai kamshin freshner na mota, sai kuwa sanyin Ac. Ta langwa6e tana duban titi, masifar Malaminsu da kuma hukuncin latti kawai take tsoro. Kafin ma ta kammala shara da ake ba wanda ya je latti tasan cewar sun soma test din. Har suka iso ba wanda ya tankawa dan uwansa. Da saurinta ta bude motar za ta fita. "Hey, saurin me kike?" Yanda ya yi maganar a tausashe tamkar ba masifaffen yayansu bane yasa ta kallonsa bayan ta dakata, shima ita yake kallo san nan ya bude kofar ya fito. Ta window ya bata umarnin fitowa. Ta fito duk a tsorace ganin prefects a kofar makarantar tare da dispiline master. A sukwane take tafiya, baki ta saki tana jin yanda yake turanci. Dama ta riga tasan ya iya, ta jima dai bata ji ya yi ba. Yanda yake wani karya harshe tamkar ba a Nijeriya ya yi karatu ba. Hakuri ya bada bisa rashin zuwanta da wuri kafin ya rok'i alfarmar a kyaleta ta shiga nan gaba ba zata kara ba. Da fara'a da komai Malamin ya yi na'am. A karshe Yaya Khalid ya dubeta. "Shiga." Ina, ai bata san ma yana yi ba saboda gaba daya ta tafi a lissafoshi cikin jerin jaruman masu fina-finai a kasashen turawa. "Kurfi." Kiran da malamin ya yi mata ya sa ta firgigit, shi kuwa Khalid kallon da ya tsaya bibiyarta da shi bai wuce na mamaki ba, yau dai ba kalau take ba don ya riga da yasan kallo haka na kurilla ba ya daga cikin dabi'arta. Ya numfasa sa'ilin da ta shige shi ma ya shiga mota ya bar wurin. *** Shirye-shiryen bikin ya kankama a gidan. Yan matan kusan koyaushe babu zama daga wannan kasuwar sai wancan. Anko kala uku suka fitar nasu na yanmata. Sai kala daya wanda zasu sanya ranar wuni har iyaye. Daya zasu sanya ranar Kamu, daya kuwa ranar lunch da iyayensu mata suka shirya, sai daya ranar dinner da angwayen suka shirya. Kurfi tun wuri ta kai dinkinta tare da Zeenat. Ya kasance abin ya hademusu, ga shirye-shiryen jarabawa ga kuma na biki wanda ana cikin bikin ne zasu soma. Koda suka lissafa, ranar dinner ne kadai zasu shiga lokacin jarabawa don a ranar suke da paper ta farko. Wannan yasa hankalinsu kwanciya ba kadan ba. *** Mami na zaune a saman kujera a sashen Hajiya tare da sauran facalolinta inda suke faman lissafin kayan cefane da sauransu kamar dai yanda Mazajen suka sanyasu. Ta daure ne kawai ta kai zuciya nesa kamar yanda ta saba don abu kadan ake jifanta da bakar magana. Murmushi dai shi ne