← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 41

Sashe 18

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

idanu gudun kada ta tashi hankalin iyarta. Kafin a hankali ta kamo hannunta. "Wai Laila yaushe ki ka ara zama raguwa?" Ta hau girgiza kai. "Ba haka bane Mamina, bana son gaba, bana son rayuwa ayita yinta ana gaba da juna ne. an uwana ne, amman ba su aunarmu, komai ina lura da shi ina dannewa ne ta hanyar kauda kai. Ba fa don bana damuwa sosai bane, da shi nake kwana nake tashi. Mamina ina son an uwana, ina son ganin kanmu a ha e ana zumunci, sai dai ni bansan dalilinsu na wannan tsanar ba, ke kuma kin i fa amin." Ta an rungumota zuwa jikinta, suka an ci sakanni a haka kafin ta mi ar da kanta su dubi juna. "Kinsan me? Ban ta a sanin iyata tana da wannan hangen nesan da tunani ba kamar haka. Kullum kallon yarinya nake maki, ashe bansani ba, a bayan wannan yarintar akwai oyayyar mace mai tunani da hankali wadda ni bansani ba." Murmushi Kurfi ta yi don ha a ta ji da in maganganun Mami, hakanan tunawa da yanayinta na rashin lafiya ya sa ta za i ta nuna komai ya wuce a fuska tunda hakan ta e so. Itama Mamin ganin haka sai ta ji da i, ta ci gaba da magana a nutse. "Alhamdulillah, ko iyakar haka na sani na kuma gani, na godewa Allah. Ni nasan ba za ki karaya da wuri ba koda kuwa ke ka ai aka bari da wannan ya in." Cikin rashin fahimta Kurfin ke kallonta, ita sam bata gane inda maganar ta dosa ba. "Eh Laila, kimin wani an al awari." Jin haka Kurfi ta gyara zama. "Al awarin me?" "Duk wuya duk tsanani ba za ki sauka daga kyakkyawar turba na tarbiyya da muka oraki a kai ba, hakazalika za ki yi imani da addara mai kyau da akasinta kamar yanda addini ya wajabta a kan kowane musulmi." Ta numfasa kafin ta ora. "Laila kwanaki su na ara tafiya, daga sati zuwa watanni sai ki ji shekaru, daga haka kuma a wayi gari bamu raye. Misali nake maki ba don na tashi hankalinki ba." Mami ta furta tana mai kamo yatsunta ganin ta soma shiga ru "Mutuwa dole ce, tunasarwa a kanta shima dole ne. Tana ara imani a zu atanmu, ko bamu mutu yau ba, gobe za'a iya wayar gari ki mutu ki barni, ko kuma na mutu na barki. Sai dai kawai mu an adam muna da burika da yawa a rayuwa. A cikin nawa har na ga aurenki. Ki yi ha uri da rayuwa, ki rage wannan saka abu a ran. Komai lokaci ne, duk runtsi duk wuya kar ki zama kamar su, ki fita daban, duk abinda zasu yi miki ya zamana kin maidashi ba komai ba. Ki daure ki yi ta addu'ar komai ya gyaru ayi zumunci ba tare da wata sa in sa ba. Da ace ni da an uwana bamu zama masu kauda kai ba, da kuma ace a an uwan Hajiya Saudatu babu wa anda suka fahimcemu ba, to da abinda zai afku zai fi haka zafi. Addu'a ce ke zaunar da ni a gidannan, Allah Ya addara sai na haifeki, kuma ina fatan na haifi na cikina ma." Ba nan Mami ta tsaya ba, haka ta ci gaba da yi mata nasiha sosai game da rayuwa da kuma nusar da ita ladanda ke cikin mai zumunci da arin gyarashi a yayinda ya nemi rugujewa da kuma azabar da Allah Ya tanadar ga mai yanketa. "Ko mu iyayenkimuna raye, ko bama raye, Laila kar ki bari ki aikata abinda zumuncinnan zai rabu. Komai da za ki gani ki ara ha uri karki yanke hukuncin da zai sa ki yi nadamarsa a gaba. Nasan maganganuna su a shigarki, nasan ba za ki watsan asa a ido ba." Kurfi dai murmushi ta ke tana gya a kai a arinta na danne kukanta. Kalaman Mamin su na tsumata, jikinta ya yi sanyi yainda irjinta ke bugawa da arfi. Mami ta sa mata albarka kafin daga bisani su mi e su arasa tafiyarsu. Hajja ta ji da in ganin surukarta ta mai yawan biyayya da kyautatawa gareta, sun ta a hira kafin su mi e. Abinda ya ba Laila mamaki har sashen su Mama Zahida da Hajiya suka shiga, a cewar Mami tunda zasu yi tafiya auyen urfi ta'aziyar wata rasuwa, ya kamata ta shiga su gaisa. To ba dai wani tarbar arziki su ka samu ba, gwara daga Mama Zahida ta oye nata kishin. Ummi (Raliya) kuwa lafiya lau suka gaisa domin daman bata da matsala. Kurfi dai ba ta yi mitar meyasa suka je ba don kuwa nasihar Mamin ta shigeta. Washegari cikin ikon Allah kuma na uda ta kama Mami. Kurfi na falo su na kallon Zee World su ka ji Mami na salati, daman tun safe ta ke yamutse-yamutsen fuska amman ta ce lafiyarta alau. Ganin yanda gaba aya ta rikice lokaci guda tana salati hankalinsu ya tashi. Ita batasan ma sadda ta soma kuka ba, Zeenat ce ta yi hanzarin fita ta sanar da direba ya matso da mota, Allah Ya taimaka direban su Abba yana nan. Suka unguma har Baba Asmau sai asibiti bayan sun auki akwatin da Mami ta ha a na kayan Baby. A hanya ne Zeenat ta ari wayar direba ta sanar da Abba. Ya ce shi inma gashinan arasowa. An shiga da Mami labour room, kusan awa aya har Abba ya iso ba wani bayanin ta haihu, Abba ne ya samu shiga kasancewar asibitin private ne san nan kowace mai haihuwa akinta daban. Can ya fito yana ha a gumi, karasawa ya yi ya an rungumi kafa ar Kurfi wacce ke kuka kamar ranta zai fita, ta dubeshi. "Abba, Mamina fa?" A sanyaye ya dafa kanta. "Addu'a zamu ci gaba da.." arar kukan jariri ne ya katse tunaninsu, kowannensu ya warware idanu, sai kuma suka hau hamdala, Abba ya shiga. Daidai lokacin Daddy ya iso tare da Yaya Khalid da Baba Mudassir don har lokacin matan gidan basu kai da dawowa ba daga Kurfi. Shiru-shiru Abba ya fito bai fito ba, Kurfi tana ji kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a akin. Sai safa da marwa ta ke bata ko damu da idanun Baba Mudassir da Yaya Khalid ba, ita dai burinta ta yi tozali da Maminta. Can sai ga Abba ya fito fuska fuskarsa jazur, da gani ba a hayyacinsa yake ba. Ya dubi an uwansa kafin ya kai duba ga iyarsa, a fili ya soma innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! "Abdulhamid meyafaru?" "Ta rasu, Sadiya ta rasu!" Iyakar abinda kunnuwanta suka iya tsinta kenan kafin ta kurma ihu. "Mamina!!" Daga haka ta bazama akin a guje, turus tayi hango mutum an lullubeshi da zani ga jaririya a gefe ana gogemata jiki. Jan afa ta hau yi har ta karasa gareta, ta bu e zanin a hankali, fuskar ta ara haske da kyau, tamkar ma tana murmushi. Kamar ta kira sunan ta bu e idanu. Hannu na rawa ta soma bugun gefen fuskar sannu-sannu. "Mamina, Mamina ki tashi mu tafi gida. Kinga bebinki, ki tashi ki auketa ni bana so, ba zan kar eta ba kamar yanda kike fa a ina murna. Mamina wasa nake, bebi naki ne." Tana ta sumbatu ba tare da sanin ruwan hawaye na zuba a saman fuskarta ba. Ji ta yi an janyeta an rungume. Abba ne, ta ago tana dubansa a yayinda take nuni da Mami. "Haka mutuwar take? Abba kalli Mamina, ba bacci take yi ba?" Abba da ke hawaye ya ma kasa magana. Tun tana iya sanin me ta ke fa i, har dai ta fita a hayyacinta. *** A sannu-sannu ta soma bu e idanunta, can Allah Ya taimaketa ta bu esu gaba aya. Kallon akin ta shiga yi, babu kowa sai ita da ke kwance saman gadon asibiti an rufeta da bargo yayinda sanyin Ac ke ratsata. Tiryan-tiryan komai da ya faru ya dawomata a kwakwalwa. Ai tuni ta yi cilli da bargon ta mi e za ta fita a guje. Ta ci karo da marasa lafiya kashi-kashi ga duhun dare. Dr Arfat ce ta hangota ta nufota da sauri. Itama ta ri e damtsenta. "Anti Arfat ina Mamina? Mafarki nayi Mamina ta rasu." Bata iya bata amsa ba sai da ta kammala aunata ta tabbatar komai lafiya san nan ta rubuta takardar sallama, batun ku i dama bill ake su na biya. Cike da tausayi Arfat ta ja hannunta suka nufi ofishinta. Nan ta zaunar da ita ta mi amata ruwa, amman ina, wannan ba shi ne a gaban Kurfi ba don haka ta ture hannun ta mi "Ina Mamina wai? Ki kaini wajenta." Ta yi maganar murya a age, ganin dagaske ba sauraronta za ta yi ba, yasa ta tattara suka fice a motarta don tuni har an kai Mami makwancinta. A hankali Dr Arfat ta dunga yi mata nasiha gami da mata nuni cewa dukkansu zamu mutu su koma ga Allah. Koda suka isa ba kowa a farfajiyar gidan, a angaren Mamin suka tarar da an uwa da basu wuce gida ba a cike mazansu da matansu ana ara jajantawa da fa in kyawawan abi'un Mamin. Tan haka ta sulale saman gwuiwoyinta tana binsu da kallo kamar lokacin ta soma ganinsu. Sai kuma aka yo wurinta, wasu na kuka yayinda Anti Bara'atu ta mi ar da ita ta rungume. Kawai sai ta saki kuka arfa. "Anti na zama marainiya! Na rasa Mamina, shi ke nan Mamina ta bar ni!" Sambatu sosai ta ke tana kuka da iyakar arfinfa. Dakyar suka samu suka rarrasheta ta zauna saman kujera. Nasiha da ban baki suka shiga yi mata, arshe ta bi umarninsu ta shiga ta ora alwala ta auki Alkur'ani ta soma karanta Suratul Yasin san nan Mulk. Yi ta ke tana hawaye yana ta iga saman Alkur'anin, ji ta ke babu wani abu a duniyar da ya yi mata saura. Ranar ba ta iya ta runtsa ba. *** BAYAN KWANA UKU Ta zama kamar mutum-mutumi, *DUNIYA SABUWA* ta tsinci kanta mai wuyar sabo, kallon kowa a gidan take tamkar sababbin halittu. Jaririn Mami wanda tun zuwansa duniya bata aukeshi ba, shi ta urawa idanu a yanzun ma tana kallo. Yana ri e a hannun
Chapter 18 · 0% Book details