Sashe 2
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bude. Mami na zaune a falo suna kallo ita da Dattijuwar 'yar aikinta, Asma'u. Kurfi ta shigo da sallama tare da Zeenat. Abba kuwa tuni ya bi ta kofar sashensa zuwa bangarensa. Suka amsa musu, Mami ta dubesu baki a hangame. "Wai, kun kuwa so dawowa yau?" Dariya suka yi. Mami ta wuce sashen maigidanta, suma kowaccensu ta nufi dakinta. Kurfi na shiga nata dakin ta yi wurgi da jakarta, kai tsaye bandaki ta fada bayan ta rage kayan jikinta. Kasancewar bata da sallah wanka kawai tayi ta wanke uniform dinta gaba daya san nan ta fito. Sai da ta shirya cikin t-shirt fara k'al da bak'in siket san nan ta rufe gashinta ta fita rike da bokiti, tana kammala shanya ta nufi sashen Daddy, bata bi ta kofar Umma saudatu ba, ta bi ta kofarsa. Tana sanya kafarta a falon ta tsinci muryar Yaya Khalid. Takaici ya isheta, babu damar ta juya kasancewar an riga da an ganta. Dole ta karasa shiga, bata ko kalli inda Khalid yake ba. Daddy da fara'arsa ya dubeta. "Kaga Laila ta Majnun." Murmushi tayi, sai sannan ta saci kallon Khalid, ya sauya kaya zuwa farar tshirt da blue jeans, launin idanunsa wadanda koyaushe suka fi kama da na mai jin bacci, hararar da ya watsamata ne ya sanya ta kasa ci gaba da kallon ta sauke nata idanun gami da maida hankali ga zancen Daddy wanda idan da sabo ta riga ta saba da wannan kirarin da ya radamata tun tana karama. Idan ta tambayi Majnun din ya ce ai zai zo idan Allah Ya so, lokaci zai kawoshi. Ta ga ba halin fadamasa laifin Yaya Khalid tunda gashinan zaune, kamar wata munafuka ta karasa a ladabce ta gaida Daddy. Murmushi ya yi don ba haka aka saba gaisuwar ba, yasan yanzun ma ganin dodonsu ne. Ya amsa gami da mata ban gajiyar makaranta, karshe ta mike da sauri ta fice acewarta tana da assignment don suna hutun islamiyya. Ba ta kai ga cimma bangaren su Mama Zahida ba sai ta tsinci muryarsa daga bayanta. "Ke" Sai da ta dan runtse idan yayinda gabanta ya fadi sannan ta juya gami da amsawa ba don ta so ba, rashin amsawar ma laifi ne awajensa. "Naam." "Idan anyi la'asar ki sameni a d'akina." Ta kalleshi a tsorace, kafin ta kauda idanun. "Toh." Ta amsa kamar tayi kuka. Bai saurari komai bayan hakan ba ya fice. Hawayen da babu shiri ta soma, ita dai yau Allah kadai zai fiddata daga tarkon Yaya Khalid, yanzun kuma me ta yi? Kodai wani abun ya gani a wayarta? Cikinta ta ji ya bada k'ara. Sai ta fasa shiga sashen kowa ta nufi bangarensu sakamakon damuwar dake cikin ranta, hatta da sashen Kakarsu bata samu damar zuwa ba balle ta cikata da hirar da ta saba. Yan aike kuwa ta sha su, yara da yanmata sa'anninta. Karshe ma ta ce kanta ke ciwo. Ana kuwa idar da sallar la'asar ta mike da saurinta ta zura hijab sanin wajen wanda za ta je, banda hakan, bata da wani ra'ayin sanya hijab idan ba sallah za ta yi ba. Ta sanarwa Mami kiran Yaya Khalid san nan tayi gaba, Mami dai kallo ta bita da shi sanin da tayi ruwa ba ya tsami banza. Tunda ta isa kofar sashennasa ta tsaya turus, ita bata shiga ba, ita bata kwankwasa ba. Addu'o'i kala-kala ta shiga jerawa har da daga hannuwa, kawai ba ta yi aune ba ta ji an bude kofar. Idanunta ya fada cikin nasa, da sauri ta wayance da goge fuska. Murmushi ya dan yi wanda ya yi sanadin lotsawar gefen kumatukansa. Ayyana irin rainin da yarinyar ta yi mishi kawai yake, wato shi ga bak'in azzalumi. "Idan kin gama neman tsari daga gareni sai ki karaso." Ya karashe fuska a murtuke kafin ya koma ciki. Ta bi bayansa da harara har da su murguda baki san nan ta karasa shiga da rangadediyar sallama. Falon tsaf, ga kamshi mai sanyi da ke tashi. Ta nemi wuri ta zauna a kasa, shi kuwa ya hakimce saman kujera har da dora daya kan daya. "Ke ga karamar yar iska, wato samari kike tarawa haka kina hira da su ko? A uwar ina kika iya shiga instagram har ta kaiki ga dora hotuna?" Ta hau murza idanunta ba don su na kaikayi ba sai don bata san me za ta ce ba. Shi dinma ba bukatarsa ce ta amsa ba hakan yasa ya ci gaba da magana. "From today, kada ki kara gangancin bari na ganki da waya tunda ke na lura kin fi sauran rawar kai. Amman bari nayi maganinku gaba daya." Waya ya dauka ya kira dukkan sashen da yasan akwai yanmata daya bayan daya yana bada umarnin a turosu sashensa. Hankalinta ya dan kwanta ganin abin ba iyakar kanta zai tsaya ba. Dadinta ma akwai masu wayar a hannu bayan ita. Ko mintuna uku ba'a rufa ba suka halarta, kowacce tana yin baya-baya tana jira wata ta soma yin gaba. Sai da ya dakamusu tsawa kafin su samu nutsuwa su karasa ciki. Zama suka yi, waccan a bayan wannan, wannan a bayan waccan. Kurfi duk halin da ta ke ciki na razana sai da suka bata dariya, ta soma yi, suna hada idanu da shi tayi gum gami da sunkuyar da kai. Tatas ya yi musu akan rike waya san nan ya dubi Munira wacce tasu da shi ta fi zuwa daya saboda hankalinta da kuma hakuri da rashin neman abin fada. "Ki fadamin sunayen duk wadanda ke rike da waya." Munira ta lissafosu, acikin su takwas da suka shigo, daga ita sai Rashida da Zeenat ne basu da wayar hannu. Aikuwa ya titsa su akan kowacce ta je ta dauko ta kawomasa. Jiki a sanyaye kowacce ta fice. Kurfi zata tashi ya dakatar da ita. "Ke kuma ina za ki je? Ku zauna nan ku jirasu ai ban gama ba." Ya fada a fusace san nan ya mike ya nufi daki. Kurfi ta dubi su Rashida idanu waje. "Mun shiga uku, kada dai yau duka zamu ci." Munira ce ta bata amsa. "Anya kuwa? Kinsan fa ba ya duka sai dai zamu sha fada." "Hum, ni wallahi fitsari ma nake ji." Cewar Rashida wacce har zufa ta soma karyomata. Ita kuwa Zeenat ba bakin magana, jikinta ne kawai ke rawa. Bata manta sadda ya ta6a ganinta ba dankwali a ka, wani rankwashi da ya bata a tsakar kai, sai da ta saki fitsari. Kafin ya fito sai gasunan sun dawo kowacce rik'e da wayar. Bayan sun zauna Kurfi ta dubesu ganin suna kokarin cire sim. "Wallahi karku sake ku cire, don gulma ba ku cire a can ba sai da ku ka karaso ku ka ga bayanan, ni kuwa idan ku ka cire sai na fadamasa don nima ya ban nawa." Harara mai kyau ta samu a wajen Hafsat, dama tasu sam bata zo daya ba tun can. "To sai na cire din, an fadamaki yana da bukatar wadannan, daga sim har memory ba wanda zan barwa. Banza kawai." Shine furucin Hafsa gareta, ta ji zafi matuka sai dai ta yi kwafa ta kyaleta. Ita ai ba'a yi mata ta kyale, sai ta san yanda ta rama. Tana kallo Hafsat ta cire sim dinta da memory card ta cusa cikin rigarmama san nan ta mayar da waya ta rufe. Hakan ya yi daidai da fitowarsa, ya baza turare sai kamshi yake, yanzun yadi ne a jikinsa. Kallonsa kawai suke saboda tsabar haduwar da ya yi. Yaya Khalid fari ne tas kuma dogo ne mai k'irar karfi amman ba shi da k'iba. Yana da lumsassun idanuwa hakanan yana da karan hanci daidai gwargwado. Bakinsa na da fad'i kad'an, yana da kwantaccen gashin jiki. Koren yadin ya kara fiddo tsantsar kyawunsa, sai bak'in agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa, ga wani gilashi bak'i da ya sanya. Idan ka cire Kurfi da kannensa biyu (Rashida da Batul), babu wacce bata kyasa ba a sauran, burin kowaccensu ya zamana an had'ata aure da Yaya Khalid. Hatta Zeenat ba'a barta a baya ba. Ita kuwa Kurfi harararsa take a fakaice, tana ayyana kamanninsa da aljanu, ba ma wannan ba, ita gani take duk matar da ta auri namiji mai kyau to tana tare da hakuri da wahala. Domin dai mata ba zasu barsa ba, asalima ita kanta duk sadda zai fita bata da wani kwanciyar hankali. Ta jima da sanin yanda yanmatan ke son Yaya Khalid, ita kuwa ta fi sha'awar ya auri Zeenat, ko babu komai ta ga yanda take sonsa. Karasowa ya yi har inda suke fuska a murtuke, daman sau tari bai fiye sakarmusu har ya dara ba. Hannu ya mik'awa kowaccensu, ba musu d'aya bayan d'aya suka shiga mik'amasa. Yana shirin magana ya ji muryar Kurfi. "Yaya Khalid." Kallonta ya yi ta gilas ba tare da ya tanka ba. Ta dora maganarta tana mai nuna Hafsat da yatsa. "Hafsat ta cire sim da memorycard, cikin riga ta sanya." Kallon Hafsat ya yi, tun kafin ya yi magana ta kai hannu cikin rigar ta ciro ta mik'amasa tana bada hakuri. "Don ubanki nayi kama da sa'anki? Ni za ki maida dan iska?" Za ta yi magana ya kai mata hauri da kafa da karfi kuwa. Tana kuka ta mik'amasa ya sanya ta ajiye saman tebur. "Wa zai ta6a cuta? Kin saka abu a riga san nan ki mik'omin don kin maidani 'kazami irinki. Stupid kawai! Daga yau duk shegiyar da na kara gani da waya wallahil azim sai na tattakata, su kuma samarin naku zasu zo su sameni. Na lura su ne ke baku waya, to kuwa zan yagamusu rashin mutunci! Ku tashi ku barmin d'aki." Ya karashe yana mai daukar room fresher ya hau feshe dakin da shi yana yamutse-yamutsen fuska. Gaba daya sun ji haushin yanda ya nuna suna wari. Kurfi kuwa, haushinta ya tafi sakamakon murnar da take ciki na yanda aka yiwa Hafsat. Suna yin nesa da wajen ta kalli Hafsat ta tuntsire da dariya. Hafsat ta dubeta fuska jage-jage da hawaye, bata ce komai ba ta fice bangarensu da gudu-gudu. "Ke dai Kurfi ba ki ji dadin hali ba wallahi, ba'a rufawa juna asiri kenan a rayuwa?" Cewar Rukayya kenan tana harararta. Itama din ramawa tayi.