← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 41

Sashe 6

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suke da Daraktansa a hanyarsu ta zuwa wani taro, kwanansu biyu da dawowa garin, yana zaune daga gidan gaba yayinda Darakta ke baya. Motar ma'aikatansu har biyu tare da su. Kamar an ce ya kalli gefensa yayinda zasu gifta, ya hango 'yan kannennasa a cikin motar wasu gardawa suna faman washe hakora kamar sabon shiga. Gaba daya ji ya yi hankalinsa ya tashi, ba lallai su ganshi ba sakamakon glass din motocinnasu tinted ne, amman shi kam kar yake ganinsu, duk maganar da Daraktan ke yi, ba sauraro yake ba adalilin hankalinsa da ya kad'a wajen kannensa. Yaushe suka samu wannan saken haka? Sai bayan sun giftasu san nan ya dawo nutsuwarsa amman cikin ransa ya kuduri aniyar daukar mataki idan sun hadu, sai sun gane kurensu. Tun a bakin layi suka sanya Nas ya diresu, su dinma basu damu ba don sun saba da yanmata haka, da yawa basu kaunar a kaisu har kofar gida saboda tsoron iyaye. Nas ya cakesu da kudi har dubu goma. Kafin ya nemi lambar wayar Kurfi, ta maze ta karanto mishi lambarta duk da tasan ko zai shekara yana kira ba shiga zai yi ba, karshe suka yi musu sallama suka kama hanya. Layin ma da aka ajiyesu ba shi ne ainahin layin gidan ba, su na shiga kuwa suka hau dariya kamar mahaukata. Zeenat ta dubesu. "Kai jama'a, wallahi ku yan iskan karshe ne, kai! Ashe abin naku har yakai haka?" Dariya suka kara yi, Kurfi da Tasleem suka cafke. "Zauna nan, an fadamaki mu na wasa ne? Cin uban maza kawai. Kema ki soma kin ji Iklima." Cewar Kurfi. Suka kara tuntsirewa da dariya, ranar dai an sha dariya saboda jinsu suke babu digon wata damuwa. Daki suka kulle suka ci suka yi nak bayan sun ba yara shawarma kadai gudun kada su basu fin haka Anti ta tuhumesu idan ta dawo. Sai bayan sun kammala suka kasafta kudin abinsu. Ko bayan dawowar Anti, ta tambayi inda suka je, nan suka rantse cewar Shawarma kadai suka je siya suka dawo da wuri kuma. Ta gaskata hakan. Karfe bakwai na dare kuwa saurayinta dake makwabtaka da su Tasleem ya zo hira. Da rawar jiki ta shirya ta feshe kwalliya. Duban kanta a madubi tayi tana jujjuyawa. Tsakin da Zeenat ta ja ya sanya ta dubanta ta madubi tana harara. "Meye ke kuma?" Ta6e baki tayi. "Ke dince kayan haushi, ko menene abin gani a so wajen wancan Mahmud din. Duk kyawawan da ke sonki ba kya sonsu sai wani mai hanci salansa na aiki." Dariya Tasleem ta sanya, ita kuwa Kurfi ta hau masifa. "Zan zageki wallahi, banza mai halin mahassada. Ina ruwanki da shirgina? Dadinta dai ya fi mai son mai soyayya bayan rai." Jin haka Zeenat tayi gum, tasan da ita take. Wato tana son Yaya Khalid, shi kuwa har yanzu bai ga abar so kamar marigayiyar matarsa Sumayya ba. Daga haka Kurfi ta fice ta kyalesu bata ko amsa adawowa lafiyar da Tasleem ke mata ba. Falon ba kowa tsit, wannan yana kara sanyamata kaunar gidan Anti, rayuwa ce ita da iyalinta suke yi kamar a Turai ba ruwan kowa da kowa. Tana fita ta iskeshi zaune a saman kujera yana jiranta. Ta karasa ta zauna tana kasheshi da murmushi. Sai yanzun take kara kallonsa sosai, abinda Zeenat ta fadi kan hancinsa ta hanga karara, dariya ta su6ucemata, dagaske Zeenat bata da kirki. Itama fa don tana son hirar ya sanya ta ke kulashi, ko ba komai tana son ta ganta tana zance. "Ranki ya dade, yau kuma dariya na baki?" Ta dake ta gimtse ta hanyar mayarwa murmushi. "Ko kadan, wani abu na tuno." Ya yi dariyar shima. "Shikenan a bani labari." Dole haka ta kirkiro labarin karya ta bashi a ranta tana istigfari, suka hau darawa, ita tana dariyar hancinsa yayinda shi kuwa yake dariyar labarin. Dakyar ta samu ta hai istigfari a kasan ranta. Mintuna biyar kacal ta yi a wajensa san nan suka yi sallama bayan ya jajantamata rashin waya har da alkawarin zai kawomata kafin ta koma gidansu. Ta ji ta kasa cewa aa saboda gaskiya tana da bukatarsa. Da tsallenta kuwa ta koma ciki ta labartamusu, Zeenat ta zaro ido. "Kan uban can! Wai ba Yaya Khalid ya tsawatar kan waya ba?" "Aa kin manta Kawu Khalid! Ke dilla kyalemin batunsa kar raina ya 6aci, shi baisan zamani ya sauya bane da zai dunga takuramana?" Tasleem ta girgiza kai. "Um um kedai Kurfi, kinsan ni kaina da ba gidanku nake ba tsoron Yayannan naku nake, mutum sai bakar zuciya kamar bakin kumurci. Anya ba tun mutuwar matarsa ya sauya ba?" Dariya sosai suka yi. "Kema dai kya fada, ki tuna, ai a baya akan ga dariyarsa sosai sosai koda ba da mu yake ba, amman yanzu hum um!" Cewar Kurfi. "Ato, kinsan da haka kuma za ki kara jangwaloshi. Allah Ya ba ki sa'a." Zeenat ta amsa. Share batun Kurfi tayi ta hanyar mikewa ta fada bandaki alwala. Washegari kuwa sai ga Mahmud da dallaleliyar waya kirar Infinix ya kawomata. Ta yi godiya ba adadi ganin har da kyautar sim da katin kira. Nan ta saita komai ta sanyata a vibration ta jefa a kayanta. *** Satinsu uku a gidan Anti suka tattara suka koma Babban gida. Zo kaga murna da ihun ganinsu, dama anyi kewarsu ba kadan ba manya da yara. Sati daya suka kara suka koma makaranta ajin karshe. Kurfi na nan da wayarta tana yadda ta so a 6oye. Har wannan lokacin Allah bai hadasu da Yaya Khalid a gidan ba adalilin tafiyar da ya kara yi zuwa Abuja. *** Mami ce zaune a falo ta yi shiru tana sak'e-sak'en zuci, gaba daya jikinta a sanyaye yake bata da sauran kuzari. A haka Abba ya shigo ya risketa. Sallamar da ya yi ma bata san ya yi din ba. Sai da ya shafi gefen fuskarta kafin ta yi firgigit ta dubeshi. Ajiyar zuciya ta sauke gami da murmushin yake. "Sannu da zuwa Nawan." Cikin yanayin damuwa ya amsa. "Noor, meke damunki haka? Tunanin me kika da har ya daukemaki hankali a komai?" Ta girgiza kai tana kokarin sauke murmushi saman fuskarta. "Ba komai Nawan, kawai kasan wani sa'in sai mutum ya ji komai na duniyar ba burgeshi yake ba." Shiru ya yi yana dubanta, a iyakar zamansu ya san wacece ita. Mace ce mai bala'in zurfin ciki, ko damuwa za ta kasheta ba ta fad'i sai dai idan shi da kansa ya fahimci lamarin. Tana da hakuri kuma sosai ga yawan murmushi da maida komai ba komai ba. "Shikenan, amman ina shawartarki da koma menene ki barshi a hannun Mahaliccinki domin Shi ne zai yayemaki. Ki cire damuwa a zuciyarki, ki yi imani da kaddara mai kyau da kuma akasinta." Ta dan yi mishi kurr da idanu, kamar ya so ya gane damuwarta, sai kuma ta wayance da murmushi gami da dora kai saman kirjinsa. Shima ya bata kyakkyawar runguma. "Lah, bari a yiwa masoya hoto." Suka tsinci muryarta, gaba daya suka dubeta, hannu ta had'a kamar mai daukar hoton gaske. Mami da sauri ta mike zaune, Abba ya mikawa Kurfi hannu yana dariya. " Zo nan ma ki fadamin laifin da kika yiwa dan uwanku." Ta karasa baki a bude ta mikawa Abban hannu tana mai zama a gefensa lokaci guda. "Abba wa kuma ya kawomaka k'arata?" Ta furta a raunane. "Ba k'ara aka kawomin ba, ya dai ce bakya jin magana idan ya zo zai kamaki." Nan da nan ta gane ko waye. Ta zaro idanu. "Abba wai Yaya Khalid? To kuma me nayi mishi yanzu? Ni wallahi kawai tsanata ce ta yi mishi yawa." Ta karashe a shagwa6e kamar mai shirin fashewa da kuka. Murmushi Abba ya yi. "Haba dai tsana, karki kara furta hakan kinji ko? Yayanki ya fi kowa sonki, ki yarda da hakan. K'iriniyarki ya tsana. Can dai kika san laifin da kika yi mishi." Ta turo baki ba ta ce komai ba karshe ma ta mike ta fice tana mitar Yaya Khalid ba zai ta6a bari mutum ya wataya ba. Iyayen suka bita da kallo da murmushi, Mami da ta ji hawaye na son zubomata tayi saurin kauda kai ta sharesu. Abba ya lura da ita, ba ya son takuramata kan sai ta fadi damuwarta, ya tabbata ko zai shekara yana naci ba fadi za ta yi ba sai dai tayi ta ba shi hakuri. Mikar da ita ya yi yana mai yi mata rad'a a kunne. Ta dubeshi cike da tsananin kauna tana murmushi kafin su mike zuwa sashensa. *** Karfe tara da mintuna na dare, ta bar sashensa zuwa dakinta bayan ta tabbatar da ya yi bacci. Tana shiga dakinta ta sanya mukulli. Gaban madubi ta tsaya ta bude rigarta tana kallo. Shafa cikinnata tayi da murmushi dauke saman fuskarta sadda ta ji motsin abinda ke cikinta kadan-kadan. 'Kina da ciki har na watanni hudu Sadiya, sai dai ba zan 6oyemaki ba, rayuwarki na cikin hatsari. Sai dai idan kin bi k'aidarshan magunguna da samawa zuciyarki nutsuwa ta hanyar kauda duk abinda zai bakanta rai komai zai tafi daidai idan kuwa ba haka ba ki hakura a ciremaki cikinnan." Ta tuno maganganun Dr Arfat a gareta alokacin da ta ziyarci asibitinta kwanakin baya. Hawaye ta ji ya soma zuba saman fuskarta, karshe ma sai ta rushe da kuka. Sam ba zata bari a ciremata cikinnan ba, akan wane dalili Allah Zai bata kyauta kuma ta cire duk da cewar larura ce za ta sanya. Ta tuno diyarta Kurfi da ke masifar son ganin anyi mata 'kanwa ko 'kani. Ba zata dakusar da mafarkin mijinta mai son tara iyali da yawa ba amman dan aljannan bai ta6a sauyamata fuska ba ko ya juyamata baya bisa yanayin rashin haihuwarta sosai ba. Ta ci kuka abinta kafin ta wanke fuska ta dora alwala, Shafa'i da wutri ta gabatar ta rufe da addua. *** Tafe take a hanyarta na zuwa sashen Umma mahaifiyar su Khalid, ranta gaba daya a jagule don bata kaunar zuwa bangarensu muddin ba dakin Ummi (Raliya) zata shiga ba. Ta lura a duniya Umma ba ta da abar kushewa da tsana sama da ita, ita kuwa hakan yasa ko kyallinta bata son gani. Taimakonta ma daya, tagwaye na masifar ji
Chapter 6 · 0% Book details