Sashe 16
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
girman kai take ji da shi, yaushe rabon da ta zo sashenmu ta gaishemu yanda ta saba?" wafa Hajiya ta yi. "Barni da ar banza, ni wallahi ban i ta mutu a wajen haihuwarnan ba. Ke na tsaneta yanda ba kya tsammani." Dariya Mama Zahida ta sanya. "Ni kuwa bana fatan ta mutu, na fi aunar ba in ciki ya asheta wallahi, so nake itama a yi mata kishiya ta ji yanda ake ji. Idan ta mutu to me akai?" Shiru ya an biyo bayan nazarin da Hajiya ke yi, can kuma ta yi asa- asa da murya. "Kuma fa da gaskiyarki, kishiya ita ce daidai da wannan matar. Ya kike ganin za'ayi? Ga Balarabe an riga da an gama da shi, bana jin zai so ara aure." Mama Zahida ta an yi shiru, can kuma ta saki dariya. "Haba Hajiya, wannan fa mai sau i ne, ki saki aljihu kawai, ni nasan yanda za'ayi, na kuma dan da wacce zamu ha ashi." Hajiya ta murmusa. "Shikenan, bari dai a kammala shagulgulan sallah mu gani." Sukai dariya hankalinsu kwance, Aliyu da ke a bayansu kusan ya fisu murna da abinda su ke ullawa, ko ba komai wannan ma na daga hanyar da zai gasawa Kurfi aya a hannu. Har yanzu bai manta marin da ya sha sanadinta ba, ya kuma rantse sai ya auki fansa. *** Biyu ga sallah suka ci kwalliya sosai suka fita ziyartar an uwan Mami, a gidan su Tasleem sai da Kurfi ta kwana biyu. Da yammaci suka ci kwalliya fiye da wacce su ke a baya. Kurfi ta ha e cikin pink lace mai adon green sai kuwa duwatsu. Ta yi kyau sosai, ta fente fuskarta da kwalliya ta fito tamkar wata Amarya. To hakanan a angaren Tasleem, itama adon kece raini ta yi da lace inta ruwan madara da ratsin dark brown. Itama ta fito as da ita. Suka dubi kwalliyar juna su na murmushi, ko ba'a fa a ba sun san dai sun yi kyau tsaf. Daga haka sukai zaman jiran isowar Mujahid saurayin Tasleem da zai fita da su. Tasleem ta ara ciro waya ta danna mishi kira. Bayan sun kammala wayar ta dubi Kurfi su kai dariya. "Allah Ya shiryemu." "Uhm, ameen ke dai, ya ce ya kusa." Gya a kai Kurfi ta yi ta na mai ci gaba da aukar hotunanta a waya. "Ni kuwa kinsan me ke ban mamaki da an gidanku?" Ba tare da ta maida hankali ba sosai ta bata amsa. "Sai kin fa "Wallahi ba wanda zai ce kakanku ya ta a ri e wani mu ami na shugabancin asa a baya, kinga dai nasan komai ya ja baya sosai ba wai kamar yadda Mami ke an labarta abinda Kakanku ya mallaka a baya ba, amman wallahi rayuwarku so simple na gani, ba ku wani auketa da zafi ba. Ke ni ba ma wannan ba, wallahi kun samu kyakkyawan tarbiyya ta yadda ba'a sangartaku ba da ku i. Ba'a ata ku ba, da wasu ne fa adaidaitar ma ba hawanta zasu yi ba." Kurfi da tuni ta maida hankali kanta, ta yi dariya. "Ba kece farkon fa ar haka ba, kuma ma kina mantawa shugabannin baya basu fiye satar da na yanzu ke yi a gwamnati ba, banda haka ma Hajja fa ta ta a fa amin sai da suka sha gwagwarmayar rayuwa bayan saukar kakanmu daga karagar mulki, shi mutum ne mai kyauta da bai yarda makwaftansa da bayin Allah su kwana da yunwa ba alhalin shi ya na oshe. Daidai gwargwado yana taimako ga wanda ya zo da wanda ma bai zo ba amman ya ke da bu ata. Kamar yanda ya gina masallatai a auyuka da dama hakanan ya gina rijiya da makarantun islamiyya. Hakanan yana da kiyayewa da tsoron cin haram a cikin halal, wannan ya ara sanyawa sam ba ya son cin ku in gwamnati. Kinga da a wannan arnin ne ba abinda za'a duba, ba wanda ya damu da hakan. To kinga kuwa dole komai ya ja baya, san nan ku en da ake biyansa bayan saukarsa nan ma kuma sai ya zama ba wani albarka ya ke mishi ba sosai. Alhamdulilah tunda dai ance ya mutu ba bashin wandala a kansa, hakanan asusunsa na banki bai bar abinda ya haura miliyan ba koda dai ku in da, da kuma na yanzu akwai bambanci. Ke da za ki ji fa i tashin da suka shiga kafin Allah Ya ara aukaka su za ki ara fahimtar rayuwar ba komai bace. Yau kana da shi sai kiga na asan ka ya zo ya fi ka. Sai dai idan an ce don suna toh akwai kam, kuma Alhamdulillah kamar yanda kika ce har da tarbiyyar. Tunda gashinan waya sai an mula ake bamu." Dariya sukai don wannan dai da Yaya Khalid take. Tasleem ta ara girmama zuri'ar Khalid Kurfi. "Banda ma kina koyamin satar hanya ai da ba haka ba, tuni Yaya Khalid zai dunga min kallon ustaziya." Tasleem ta kai mata duka a baya tana dariya. "Dama kina da ra'ayi." Murmushi kawai Kurfi ta yi. Ba jimawa wayar Tasleem ya yi kara, Mujahid ne, sanarmata ya yi cewar yana can bakin ayin kamar yanda ta bu ata, kada ya arasa gidan. Ta amsa da to san nan suka ara gyarawa suka fice. Anti Rumaisa ta fita zuwa gidansu taron dangi, Mamin Kurfi ma na can, suma ance su je amman sun ce zasu an le a wani wuri sannan. HondaCrv ce baka wuluk mai tinted glass. Banda shima Mujahid in da ya sauke gilas da ba ganeshi zasu yi ba. Gaban Kurfi ya fa i, ta dubi Tasleem. "Kai, nikam wallahi bana son shiga mota irin haka na ba on fuska." Tasleem ta sauke ajiyar zuciya. "Ki ke tsoro ko nake yi? Amman karki damu nasan Mujahid farin sani, bai da wannan abi'un banzan na samari. Kuma ke banda ma abinki hakan bai fi ba, kika san da wa za mu iya ha uwa a hanya?" Jin haka sai kuma ta jinjina kai. "Kuma fa hakane." Daga nan suka arasa, Tasleem na gaban mota ita kuwa Kurfi na baya ta ame, bayan sun gaisa ta shiga danne-dannenta a waya, sama-sama ta ke jin hirarsu. Har suka isa shahararren park in da ya yi suna warai a fa in garin ba ta sanya musu baki ba. Wuri ne na an gayu manya da matasa har ma da yara kasancewar akwai angare na kayan wasanni da kuma na kayan walam hakanan wajen wamin wanka, akin taro da sauransu. Suka jera su uku, tafiya suke tamkar ba sa so har suka isa ga wani lambu mai shegen kyau wanda aka awata da furanni kala-kala akaiwa furannin shapes na love da kuma sunan park in a grasscarpet. Wajen sanyi babu hayaniya sam, kasancewar sallah, ya an samu cikowa ka an. anmata da samarinsu a kujeru mabambanta, wani angaren kuwa magidanta ne da iyalansu sun ha a picnic. Sai abun ya ha u da sanyin gari da an hadari-hadari ya bada yanayi mai kyau da da i da ke taimakawa wajen wanke zu atan kowane an adam da ke wurin ciki kuwa har da urfi wacce ke jin kamar yau ne sallarta saboda wata irin nisha i da ta ke ji a ranta. Ko zama ba ta yi ba ta dubesu fuska a sake. "Ina zuwa." Daga haka ta gyara zaman ba in gilashinta ta fice cikin tafiyarta mai salon burgewa. Haka har ta fita gaba aya ta nufi angaren siye da siyarwa. Ya ha e cikin shadda blue black inkin riga iyaka gwuiwa sai kuwa ba ar hula a kansa. Ba in gilashin idanunsa sun taimaka wajen ara haska shi inda ya ana tsaye a tsakiyar park in yana neman Dawud a waya, so ya ke ya ji ta angaren da suke gudanar da taronnasu na tsoffin aliban makaranta (Reunion) sai dai layin ba ya tafiya hakan yasa ya ci gaba da kutsawa ciki rai a ha e ganin irin yanda ake binshi da kallo, abinda ya tsana kenan a rayuwa, wannan ma na daga cikin dalilan da ya ke yiwa matan yanzu kallon basu isa ba. A can kuwa, Kurfi ice-cream ta siyamusu san nan ta fito ri e da ledar don komawa wurin su Tasleem. Kanta na asa tana gyara zaman jakarta, shi kuwa ya taho da zummar shiga domin an ce ta cikin wurin ne ake hawa lift a ulla inda zai sada mutum da hall din. Kasancewar kallo ba ya daga cikin sabgarsa, hakan yasa bai lura da ita ba, ya nufo dab da ita ne wayarsa ta yi ara, a garin ya kai duba ga wayar ya bangaje ta. Itama ba ta lura da tahowarsa ba har sai da hakan ta faru ledar ice cream in ta fa i. Wani guntun tsaki ta ja a daidai lokacin da ya ke furta. "Ya Salam, i'm so..." agowar da ta yi yasa sauran zancen ma alewa a fatar bakinta. Tuni ta cire gilashin fuskarta tana dubansa, sai kuma ta yi saurin dur usawa ta kwashe ta mayar leda. Toh shi inma bai nemi ya tankamata ba a wurin, don haka ya kewayeta ya wuce ransa a ace. Ta an bishi da kallo kafin ta dubi mutanen wurin, duk ido na kansu, sai ita inma ta maze ta hanyar ci gaba da tafiyarta sai dai wannan karon da an sauri-sauri har ta isa ga su Tasleem. Ganinta ta taho a rikice ya sanya Tasleem neman an mintuna wajen Mujahid sannan ta nufota. "Yaya Khalid, wallahi yau zan ci gidanmu, ki rufan asiri ki zo mu bar wajennan." Jin haka kayan hanjin cikin Tasleem suka ka Mujahid bai so tafiyarsu ba haka ya ha ura suka fito ya maidasu. *** Koda suka koma gida hankalinta bai kwanta ba musamman da Mami ta kirata ta wayar Anti Rumaisa ta nemi sanin laifin da ta yiwa Khalid ya ke ta nemanta. arshe dai Mamin ta sanarmata cewar ta shirya ya sanya direbansu ya zo aukarta. Hankalin Kurfi ya tashi, ta tsinewa Tasleem ya fi a irga. Sai a san nan ne ma Anti Rumaisa ke jin abinda ya faru, ai kuwa ta yi salati ta ara da hailala, fa a kuwa tamkar ta ari baki haka ta