← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 41

Sashe 40

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kasan ya zamu yi? Mu sauya hanya, ka bi inda akwai yawaitar mutane, sannan mu gani." "Hakan nake tunani dama, bari na bi ta cikin gari." Daga haka Yakubu ya ara gudun motar bayan ya sauya hanya. Kamar kuwa daga sama motar ta wucesu a guje ta yi gaba. Sai a sannan Kurfi ta sauke ajiyar zuciya. "Kinga ta tabbata dai mu ake bi, Allah Ya fi su ko ma su waye." Gya a kai kawai ta yi tana ci gaba da godiya ga Allah da Ya karesu da kuma addu'ar neman tsari. Har aka yi aka kammala gyara mata gashi ba ta da cikakkiyar nutsuwa, zuciyarta ba ta huta da tunanin dalilin bibiyar ba. Ana kammalawa suka wuce mall inda ta yi siyayyar mayukanta na shafawa da sauran tarkacen da ta ke bu ata don ta rantse ba za ta taka gidan Khalid ba har sai ya dawo ta san matsayinta. Hajja ta yi fa an amman a banza. Koda ta koma ba wanda ta sanarwa da abinda ya faru a ranar ganin ba amfanin tada hankalinsu akan abinda ba ta da tabbas. *** Tana kuka ta ke zuba bayani. "Ina mai rantsuwa da Allah duk abinda na mallaka zan iya arar da shi matu ar za ka min aikin da zan koma Khalid Kurfi Estate. Malam na maka al awarin kayan more rayuwa da ciki har da gida da mota duk radda na bu i idanu na ganni a tsakar akina na koma wa aurena." Tun da ta soma magana ya ke are mata kallo, komai ta yi ma shi burgeshi kawai ya ke. Jin irin yanda ta shirya sadaukar da komai don samun biyan bu atanta a ransa ya furta "An zo wajen." Domin yasan wannan ce damarsa da zai tafiyar da ita yanda ya so. arshe ya ha ata aiki mai wuya. "Kar ki damu kanki Hajiya Zahida, tunda har ki ka zo kema kinsan zaa share maki kukanki. Aiki sai dai idan baa zo wajenmu ba, ba ki san irin manyan da ke shigowa gidannan ba sa'ilin da duniya ke bacci. Mun yi musu aikin da ya shafe naki kuma sun ga biyan bu ata don haka kada wannan ya dameki. Za ki yi yanda ki ke so a gidannan, lamarinki zai bun asa har ya fi yanda ki ka tafiyar da shi a baya." Wani da i ya ratsa Mama Zahida nan da nan ta share fuska tana dariyar jin da "To amman fa aiki ne babba, fatan za ki iya?" "Wallahi ko ma menene ni kam bani da damuwa zan yi shi. Ka fa a kawai." "Na farko dai za ki jera kwanaki uku kina zuwa shimfi ata, na biyu kuwa da wannan ruwan da ya gauraya na jikinmu zan yi amfani da shi wajen yi miki aikin da za ki ke ma abarta ke d kanki ki binne. Bayan wannan zan miki kwalli ta yanda wanda za ki sanya kuma ki yi duk yanda za ki yi ku ha u da shi mijinnaki. Daga ranar da ku ka yi ido hu u, to ki tabbatar ni Badaru kakata ta yanke sa a don kuwa duk abinda ki ka lissafo zai tabbata har ma ya wuce tsammaninki." Idanunta sun riga da sun rufe, jinta ta ke yi ko mene za ta iya aikatawa matu ar bu atarta za ta samu biya. Don haka ba wani jinkiri ta amsa. "Zan iya, zan yi. Matu ar zan cimma nasara bani da damuwa." Wani da i ya ziyarci Malam Badaru, nan da nan ya mi e ya fito daga akin. Umarni ya ba yaronsa akan a sallami kowa sai zuwa gobe zai gansu. Nan fa taron jamaar da ke jiransa wa anda mafi yawansu mata ne suka tashi su na uni don abin bai musu da i ba. Mafi yawa a matan satar hanya suka zo. Wasu a dalilin kishiya wasu kuwa mallaka ce sai kuwa anmata masu neman farin jini ta arfi da yaji. Ciki kuwa har da karuwai masu son bun asa kasuwancinsu. Bayan fitar kowa yaron ya rufe ofar gidan gam. Sai a sannan Malam Badaru ya soma aiwatar da nufinsa akan Mama Zahida, ba ta ta a tsammanin neman ta hanyar bayan gidanta ba ne, ihun azaba dai ta yi shi har ta gaji ta ha ura. Bai kyaleta ba sai da ya kusanceta ta hanyar da ta sani sannan ya kyaleta tana kukan azaba. Can sai mi o mata wani ruwan magani bayan ya ibi wanda ya ke bu ata ya sanya a kwalba. Ba musu ta kar a ta sha don ta ji sassauci. Daga nan ya mi e ya fice yana dariyar eta ko ba komai ya fanshe. Kusan wuni curr Mama Zahida ta yi a gidan bokanta har dai ya tabbatar ya mata ha in magungunan da nan da nan ta ji ta sakayau kamar ba ita ke jin azaba ba sannan ta fice. Ba don Allah Ya taimaketa da motarta ta ke tafe ba to da tana da tabbacin sai an ago ta nan take. Koda ta isa gidanta ma wa anda a baya an haya ne a ciki, sai dai ta yi musu korar wula anci kawai don ta rayu ciki don ta rantse ba za ta je gidansu mai yara kusan talatin da oriya ba. Yawanci ma iyayen wasu basu nan. Ruwan zafi ta shiga sosai ta gasa jikinta, ranar ulle ofa ta yi don kuwa ba inda ta taka ta je a yanayin da ta ke jin kanta. Da zarar ta tuno komai zai zo arshe sai zuciyarta ta yi fes. Misalin arfe takwas na dare, Kurfi ce zaune a sashin Abbanta bayan ta gama zagayen kowane aki na sashin Amaryarsa wacce ake shirin aura aure gobe. "Abbana sosai wuri ya yi kyau. Allah Yasa a yi muna raye." Da murmushi ya amsa yana mai wasa da hannun Mu'azzam da suka shigo tare da Kurfi. "Amin My Angel. Ni kuwa ku na waya da mijinki?" Ji ta yi gabanta ya fa i, idan ta ce aa za fa a iya tilastawa Yaya Khalid abinda ba ya so, ta fi aunar a kyaleshi da raayinsa. Tambayar da Abban ya ara a karo na biyu cike da tuhuma ya sa ta gya a kai. "Eh Abbana." Ya yi shiru yana nazarinta, jikinsa bai ba shi cewar su na yin ba, ya na zargin rayuwar da Laila ke gudanarwa a gidanta. Sai dai ba ya son zurfafawa ba tare da kwakkwarar Hujja ba. Don hakan ne ya za i amincewa da Eh da ta furta koda kuwa akwai tarin tambayoyin, ya barsu su fito da kansu wataran. Ta yi nasarar auke mishi hankali daga zancen, ba don kuma ba ya sane ba haka ya kyaleta. Sai dai ya na sane cewar tabbas iyarsa tana da sauran damuwa. "Abbana ya batun karatuna?" Ya gyara zama, nan da nan ya ji sanyi a ransa ko ba komai ga abinda zai saurin auke mata kewa. "Akwai shi My Angel tunda har mijinki ya amince. Ki ha o takardunki ki dam awa Babanki Mudassir. Zai nema maki." Ta ji da in hakan ta yi godiya kafin ta yi mishi sallama ta fita auke da Mu'azzam. Ba wani jinkiri kuwa ta auka ta kai, shi kansa Baba Mudassir ya ji da in hakan, ya tabbata mata zai magana da abokinsa Prof assim. Da wannan murnar itama ta baro wajensa. Kwanaki biyu tsakani Amare suka tare. Baba Mudassir ya samu mace mai shekaru talatin, ba ta ta a aure ba, sai dai kuma ar boko ce hakanan kuma ma'aikaciya. Hajiya Hafsat. Wayayyar mace ce wacce ta amsa sunanta. Tana da kirki kwarai kamar yanda ta san darajar kanta. Baba Mudassir ya ji da in samunta matsayin matarsa ko ba komai yana son harkar wayewa. Ita kuwa Amarya Yasmeen wacce ba wani shekaru mai yawa ta ba Kurfi ba sai dai tana da jiki da tsawo irin na manya wanda ba lallai a fahimci arancin shekarunta ba. Yarinya ce mai biyayya wacce ta taso cikin rayuwa ta maraici. Mahaifiyarta Basira ba abinda ta sa a gaba face kwa ayi na abin duniya. Ta sha yin aiki a gidajen masu ku i tana tura su wataran ta yi aryar rashin lafiya kawai don ta samu wani a yaran gidan ya ce yana son su saboda kaf yaranta babansu suka auko. Kyau irin na fulani, Yasmeen ce kawai ta auka ba in fatarta ta bahaushiyar sak ba sirki. Wannan sai ya zame mata wani abin ado na daban, ya kasance ta fita zakka cikinsu wajen kyau da kuma kyawun hali duk kuwa da cewar ga aya yayyunta sun yi aure. Sosai Abba ya yaba da binciken da akai game da ita da kuma ita kanta yanda ta nuna mishi tarbiyya. Kurfi ta yi murna da auren Abbanta sai dai kuma ranar ta sha kuka sosai da Yasmeen ta tare a sashin Maminta a baya. Hajja ce ar rarrashi gami da nasiha. *** Washegari tun misalin arfe takwas na safe ta kammala girka abin kari ta ajiye na Hajja ta wuce sashin Abbanta ri e da kwando. Koda ta kwankwasa ba jimawa aka bu e. Sai a sannan ta yi tozali da matar Abbanta. Fuska auke da murmushi ta tarbeta, ganin haka itama sai ta saki fuskar sosai ta shiga da sallama. Ta gaisheta a ladabce ba tare da la'akari da komai ba, Yasmeen ta amsa. "Momi ga breakfast." Kunya ta an kama Yasmeen. Ita kuwa Kurfi tuni ta ajiye saman centre table, Yasmeen na godiya ta amsa da fara'a ta fice. Tana tafe da zummar komawa sashinsu ta ci karo da Rukayya. Banzan kallota watsamata, Kurfi ta saki fuska sosai. "Sannu da zuwa, yanzu kike tafe?" Tsaki kawai Rukayya ta ja ta ara gaba. Kurfi ta ha iye dariyarta ta bi bayanta ganin dai itama sashin Hajjar ta shiga. Kuka ta sameta tana yiwa Hajja gami da ro on ta sanya Baba Mudassir ya dawo da Mamanta. Hajja ta dubeta. "Ki raba ni da wannan mai zafin zuciyar. Ba zan iya tunkararsa da wannan zance ba." Rukayya ta fusata. "Haba Hajja, ke fa kika haifeshi ba shi ya haifeki ba." Hajja ta aure fuska. "Wai ma me ya kawo ki da safiyarnan?" Rukayya na uni tana
Chapter 40 · 0% Book details