Sashe 26
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ban akin. Bayan fitar ta ya kai duba ga hoton da ta juya, hannu ya kai ya auka yana dubawa, a hankali ya dubi ayan gefen inda sauran hotunansa da ya ke shi ka ai su ke a jere har uku, babu wanda aka juya sai wannan in dai. Mamaki ya kama shi sai dai kuma ya basar da tunanin. Ita kuwa a gurguje ta kammala da falon, ta wanke ban akin ta fita. Tana komawa sashinta ta fidda kayan jikinta ganin sun ji e ta zura doguwar riga ta material ja mai sirkin ba i ta rufe kanta da ba ankwali. Kayan ta nufi an barandar da ke a wajen falo idan ka bu e wata ofa ta shanya su kan arfen shanya kafin ta koma ciki. Tana nan zaune a falon ya shigo da sallama. Ta dubeshi, ya fa soma takura mata har ga Allah, sai ya yi ta shige da fice a angarenta alhalin ga na shi can ( arfi hali). Zama ya yi kafin ya dubeta. "Abinci fa?" Kamar ta ce me ya hana ya ci a asa kamar yanda ya soma, sai kawai ta share gami da mi ewa ta sauka. Komai ta ha a ta kawo ta ajiye, ta arta ta zuba masa a filet ta ajiye lemu da ruwa san nan ta koma ta ci gaba da kallon series inta. Ya na ci a hankali ya na bibiyarta da kallo, kamar ta nutsu kamar ba ta nutsu ba, wannan shi ne tunaninsa. _ "Yarinya ce fa, kar ka manta, yanzu ne ka ke da damar sarrafa ta yanda ka so ka kuma ora ta kan tsarin da ka ke so. Amman idan ka ji shawarata."_ Ya tuno kalaman Dawud a sadda su ke tare azu. Yamutsa fuska ya yi kafin ya maida hankali ga abinda ta ke kallo. Ba da zato ba aka nuno jarumin film in ya tarbo ugun jarumar yayin da za ta fa o daga saman tebur. A hankali aka soma ki an taushi da rera wa a mai da i. Hannunta har rawa ya ke wurin aukar remote da zummar chanja tasha. "Gulma, da ba haka ki ke kallo ba? Ko kin manta har kuka ki ke yi?" Maganar ta bata mamaki a farko don kuwa karkace kai ta yi ta na dubansa, shi in ma idon ya tsura mata, kunya ta kamata ta sunkuyar da kai. Ya kauda zancen. "Me ya kai ki ta a min hoto da har ki ka juya?" Ji ta yi irjinta ya buga. Ta ma rasa bakin magana sai le anta da ke motsi. Dakyar ta ce "A saman gado na gani sadda zan gyara, sai na maida saman dirowa." "Sai ki ka juya?" Ta girgiza kai kamar ta yi kuka don kunya da takaicin kanta. To me ya yi mata zafi ma da ta aikata hakan? Ta auka zai ara tankawa sai dai ko magana bai ara yi ba ya ci gaba da cin abincinsa. Bayan ya kammala ya mi "Idan kin kwashe ki zo." Ta gya a kai. "Toh." Ya juya ya bar mata falon, sai kuma a san nan ta samu nutsuwa, ta tattara kwanukan ta sauka. Nan in ma sai da ta tabbatar ta gyara komai kafin ta koma. Tana taka steps in tana tunanin dalilin kiran, sai yanzu ta ji abin wani banbarakwai, Yaya Khalid na kiranta to ta yi mishi me? Sai dai koda ta tuna da zancen hoto duk sai ta tsorata, to yanzun ma bugunta zai yi ne ko kuwa tsawar zai mata? Da yin wannan tunanin ta hau hura hanci, idan ta tuna hoton ji ta ke komai ma iya yi mishi za ta yi tunda har bai ji nauyin abinda ya yi mata ba. Shi kuwa yana shiga akin ya nufi ma'ajiyar hoton, auka ya yi gami da sanya shi a wata akwati da bai cika amfani da ita ba. Ya auko aya a cikin hotunansa da ke a jere a gefe ya ajiye madadin wancan. Ha ka nan ya ji kamar bai kyauta mata ba. *** Da sallama ta tura kai falon, ya amsa asa- asa. Zaune ta sameshi saman kujera ya maida hankali ga Laptop da ke gabanshi ya na dannawa. Ganin ba ya kallonta ya sa ta ke satar kallonsa wanda ta rasa dalili har dai ta kai ga ta yiwa kanta mazauni a can gefensa a asa tunawa da ta yi ko a gida ba sa hawa kujerunsa. Basu ma isa ba. "Tashi ki zauna." Ya yi mata nuni da kujerar da yatsa, ta mi e ta zauna. Bai ara koda kallonta ba har sai da ya kammala abinda zai yi ya rufe system in. Leda ta ga ya jawo a gefensa ya mi a mata. Tasowa ta yi cikin ba shi girma kamar yanda suka saba ta an russuna ta mi a hannun. Lallen ya burgeshi har ya an murmusa, Laila ko iriniya, ta an sauya ka an. "Ga shi nan, waya ce. Ban yarda da hawa social media ba. Nasan kin san aure da muhimmancinsa, don haka kar ki yarda na tsinci lambar wani aton. Idan kin koma ki kawomin waccan wayar." "Na gode Yaya, Allah Ya ara bu i, Ya ara rufa asiri." Murmushi ya yi mata, karo na farko kenan da ya kalleta sosai ya murmusa har ga inta suka shaida tabbas da ita ya ke, ba ta san me ya sanya ta jin yarr a jiki ba. "Ameen. Thanks." Ya amsa cikin wani irin sanyin murya da ta ara ji har tsakar kanta. Ta juya ta soma tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, me hakan ke nufi? Meyasa ta ke jin sauyin yanayi a jikinta idan su na tare da shi wuri guda? Ta kasa fahintar komai har ta shiga falonta, sai da ta zauna ta ciro wayar. Iphone XR ce. Ta burgeta ainun musamman kalar da ta gani wato (Yellow). Ganin a cike take taf da chaji ha ka nan an saita komai ya sa ta gane ba wai ranar ya siyo ba, bai dai ba ta bane har sai da ya mula don kansa. "To amma ai ban ganta ba da nake gyara?" Can kuma ta tuna da wata ofa da ta gani amman Allah bai bata ikon bu ewa ba, ajiyar zuciya ta saki. Tunawa da ta yi cewar yana jira ya sa ta mi e da azama ta au wayar ta cire sim da memory card, kusan lambobinta kaf a kan account in ta na google ta ke adana su ha ka nan hotunanta wannan yasa ba ta tsaya wahalar komai ba ta au wayar ba tare da ta yi resetting ba gudun samun matsala da shi. Tana zuwa daidai ofar ta mur a da sallama ciki-ciki sai dai ya ba ofar baya hakan yasa bai ji ba kamar yanda bai fasa wayarsa ba. _"Ki yi ha uri Hajiya, ba wai ina shaidarta bane, amman ni dai nasan na barta tana kallo, wata ila dai sautin tv ne ya hana ta ji bugun."_ Ba ta san me Hajiyar ta ara cewa ba ya amsa. _"Allah Ya ba ki ha uri, sam ba haka nake nufi ba."_ ara da fa _"Al awarin da na yi miki ba zan ta a karyawa ba, ba zan tafi da ita ba ha ka nan ba zan ta a ba ta matsayin matata ba."_ Maganar ta daki kirjinta, ta ji shi har on ranta, ba ta san ya akai ba ta soma zubar hawaye. Wato har wani al awari ya auka a kanta cewar babu inda zai je da ita? Kenan ma tafiya ce zai yi? Har yana ikrarin ba zai yarda da ita a matarsa ba? Khalid wane irin mutum ne da ya ke abu kamar bai zauna a aji an koyar da shi wajibcin imani da addara ba? Ta ji wani jiri na kwasarta, maimakon ta shiga sai ta rufe ofar ta koma angarenta da sauri. Ba ta tsaya a falon ba ta wuce har aki ta kwanta saman gado ta shiga kuka. Ga irin abinda ta ke gudu, kalmar ba zai ta a yarda da ita a matarsa ba ya fi komai ba anta ranta, a iyakar saninta ko ba ka son mutum to bai fa kamata ka yi mishi wannan cin fuskar a inda ka san ba'a sonsa ba. Ta ji ya bata haushi sosai, ji ta yi an dafa kafa arta, a firgice ta ago don ba ta ji shigowar kowa ba, shi ne zaune yana dubanta, sanyin da ta hango a kwayar idanunsa ya sanya ta kauda kai tare da mi ewa tana goge fuska. A hankali ta janye afafunta da ke a gefensa. Kanta na asa ba ta ce uffan ba. "I'm so sorry." Ya furta tamkar mai ra a, ta ci gaba da wasa da yatsunta hawaye na bin karan hancinta yana iga saman yatsun, ba ta ko damu da sharesu ba. "Ba da son raina ba hakan ta kasance sai dai ki sani komai na yi ina da dalilaina, ki kuma sa a ranki ni Khalid ba zan cutar da rayuwarki ba, ko babu aure akwai an uwantaka." Ya yi shiru don yana neman hanyar faranta ranta, haka kurum bai ji da i da ta ji wayarsa da Hajiya ba, ya gane ne a sadda ya ji ta tura ofar ta rufe, sanin da ya yi su biyun ne a gidan sannan za ta zo kawo mishi tsohuwar wayar da ke hannunta ne ya ankarar da shi cewar ita in ce. "Tafiya ce ta tasomin zuwa Dubai a ashin ma'aikatarmu inda zan je domin yin wani course akan wani aikin ya shafi Kamfani har na tsawo shekaru biyu. A wannan dalilin su Daddy suka yanke cewar kema ki koma gida ki ora da karatunki kafin na dawo a maimakon ki yi ta zaman jira babu wani ci gaba." Ya arasa maganar ciki-ciki tamkar wanda bai so yin ta ba. A ranta ta ce. _'To dama ko kana nan wane ci gaba ne a auren nan? Ba ka so ba na..'_ Ta yi shiru don ta kasa gane komai. "Kin yi shiru?" Maganarsa ta fargar da ita. "Allah Ya kaika lafiya, Ya bada sa'a. Hakan ya yi ba ni da za Ya dubeta sosai, ya