Sashe 21
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi ba ta tanka ba. Da yamma tare aka shiryasu cikin atamfa holland mai tsada, aka sanyamusu laffaya mai kyau, fuskar ba kwalliya sosai don kamu ne da unshi, ba wata kwalliya su ke wa amare a irin ranakun ba a gidan. Ita dai ba baka sai kunne. an uwan Mami suka cika a sashen Hajja, Anti Rumaisa suka sanyata a aka su ka yi mata nasiha mai ratsa jiki har ya sanyata zubar hawaye. Aka gabatar da Kamu lafiya kalau, su Hajiya sai aure- auren fuska suke yi. Hafsat kuwa ko mintuna biyar ba ta yi a wurin ba ta yi ficewarta zuwa sashensu. Ganin haka wasu su ka tafi jin waf. *** arfe takwas aka shirya fita Dinnerparty, banda Kurfi cikinsu, ta yi zamanta. Akai-akai ta yi musu rakiya nan ma ta ce babu inda za ta je, da aka matsa ma ta sanya kuka dole aka kyaleta aka tafi. Tana nan zaune a falon Hajja tayi rigingine ta kwantar da Mu'azzam saman cikinta yay filo da irjinta ya na bacci, kusan rabin mutanen gidan sun yi bacci, ita kuwa ba baccin ne a gabanta ba, tunani kala-kala ta ke akan ta yanda za ta soma zaman aure da Yaya Khalid. Ta hanga ta hango babu wata mafita, ita da ko kalaman so basu ta a furtawa junansu ba asalima babu ta yanda za'ayi su soma amman wai shi ne zai zama mijinta. A hankali ta ji saukar ruwan hawaye, tun tana yi a ciki-ciki har dai ta soma sheshshe Hajja da ta soma gyangya i saman kujera ta wartsake ta kai duba gareta. Ta an yi shiru tana nazarinta, tausayinta ya kamata. "Lailatu." Ta share hawayen kafin ta mi e zaune a hankali ta gyara kwanciyar Mu'azzam ya dawo saman afarta ta na duban Hajja. "Lailatu idan akwai cutarwa a lamarin aurennan, ni zan iya cewa a janyeshi. Ki fa amin cikinki, anya za ki iya?" Kamar ta ce aa, sai ta tuna da Abbanta da Mami, ta tuna da irin farin cikin da ta gani saman fuskarsa a lokacin da ta ce ta amince da auren Yaya Khalid. A hankali ta sauya yanayin fuska ta dubi Hajja. "Ni Hajja kawai Mamina na tuna, ba wai auren ke sanyani kuka ba. Da tuni tare da ita za'ayi bikina." Ta arashe gami da fashewa da sabon kuka. Hajja tausayinta ya kara ninkuwa a zuciyarta, gaba aya Laila ta sauya. Da a baya za'a ce yarinyar nada wannan kaifin tunani da hankalin za ta iya musantawa don kuwa wautarta a baya yawa gareta, amman mutuwa ya ladabtar da ita. Ta nutsu fiye da zatonta, tasan ba wai kewar Mamin ce ka ai a ranta ba, har da aurenta da Khalid. A baya ta sha nunamata ba ta son koda inuwarsa ne, a yanzun kuwa sai ta ke arin oye iyayya da damuwarta garesu adalilin ba ta son tayar da nasu hankulan. Murmushi sosai Hajja ta yi, ha a ba su yiwa yarannasu za en tumun dare ba. Ta yi mata nasiha a arshe ta ce ta tashi ta je tayi nafila ta kuma nemi za in Allah ta hanyar istihara. Ba musu kuwa ta mi e ta yi aki. Sai da ta yi kafin ta kwanta bacci kuwa mai da i ya yi awon gaba da ita. *** Ya kasa zaune ya kasa tsaye, yawo yake a tsakiyar falon nasa yana kur ar ruwan kamar wanda ya samu magani mai aci. arshe ya yi jifa da kofin gefe ya tarwatse. Zama ya yi yaraf a saman kujera ya runtse idanu. "Laila ita muka za ar maka a matsayin abokiyar rayuwarka. " Ya tuna maganar Daddy a gareshi, ya bu e idanunsa a hankali. Sun ka a sosai, kamar ya zubda kwalla haka ya ke ji. Hannu ya sanya ya dafe kansa. "Meyasa Laila?" Ya yi furucin a hankali kamar mai ra a. Bai ta a yi mata wannan kallon ba, ba zai iya rayuwar aure da ita ba, ta yaya ma zai iya? Yarinyar da ya ga kashi da fitsarinta, ya sha rainonta da hannunsa? Yau kuma ita ake nufi da ya aura a matsayin matarsa ta sunna? 'Gobe ne ma aurin auren.' Wani angare na zuciyarsa ya yi tuni a gareshi. Ganin hakan duk ba mafita bane a gareshi ya sanyashi mi ewa ya nufi angaren Hajja ba tare da la'akari da cewa dare bane, zai iya samun sun yi bacci. Kafin ya arasa ya hangeta tayi rigingine tana kuka, kaf maganar da su ka yi da Hajja babu aya da ya tsallake bai shiga kunnuwansa ba. A sanyaye ya juya ya koma angarensa ya na ji kamar ya ha iyi zuciya ya mutu. To ma me zai ce? Ita a matsayinta na mace ta ha iye iyayyarsa da damuwarta, don me kuma shi zai zo ya ba iyayensu kunya? Ranar dai bacci arawo ne ya sace shi cike da tunani kala-kala na irin zaman da ya kamata ya yi da Laila a matsayin matar da zai aura. *** *ABINDA AKE GUDU* arfe goma da rabi na safiyar ranar Asabar, aka aura auren Zeenat Mahmud ahiru da Zahraddeen Nuhu Sulaiman. Lailatu AbdulHamid Khalid da Khalid Hamza Khalid. Rashida Hamza Khalid da Mubarak Haruna Muhammad. Ru ayya Mudassir Khalid da Jamil Shu'aibu ofar Soro. Sai na arshe Hafsat Mudassir Khalid da Huzaifa Nazifi AbdulMuminu. aurin auren da ya tara mutane da yawa. Wurin babu masa a tsinke. Fuskar kowane Ango cike da farin ciki don kuwa kowannensu ya dace da za insa. Shi ka ai ne ya ke ya e, shi ka ai ke oye damuwarsa ya na murmushi da washe ha oran da bai kai zuci ba. Dawud ya san komai, shi dai bil ha i ya ji da in kasancewar Dosti insa matar Aminin nasa. Ko ba komai ya jima yana fatan hakan. Yau dai Allah Ya yi. A can wurin matan gidan kuwa abu bai yi kyau ba domin kuwa har angaren Hajja, Hajiya Saudatu ta shigo tana kuka tana zage-zage. Wai ita an cuceta an cuci anta. Zuwan Daddy ne ya kashe wutar rikicin, ganin har Hajja na hawaye ya sanyashi marin Hajiya Saudatu a bainar jama'a. Bai shiryawa hakan ba amman a zafi irin nasa ba zai iya ganin matarsa ta ci mutuncin mahaifiyarsa ya auke kai ba. Wannan ya ara ba anta ran Hajiya ta tattara ta tafi sashenta cike da alwashi kala-kala. Aliyu kuwa da ya ji labari ya ara jin tsanar Kurfi na nu usarsa, ba zai kyale ba, ba ta ci bulus ba. Ita ce sila, wataran zai maganinta. Wannan ne alwashinsa a koyaushe. To haka ma a angaren Mama Zahida, Hafsat ta rikice gaba aya. Ita kuwa Mama Zahida tuni ta watsar da makamanta don kuwa Huzaifa ya ninka Khalid a ku i da komai. an abokin Baba Mudassir ne, to ita kuwa da daman ku in ta ke yiwa me ya rage? Hafsat dai ciwon son Yaya Khalid ne ya dawomata sabo fil a zuciya. Kuka ta ke da bore ita a lallai an cuci rayuwarta, itama sai da Baba Mudassir ya bubbuge ta kafin a samu salama. Duk wannan diramar da ake yi, tana sashen Maminta ta dun ule saman kujera tana kuka kamar ranta zai fita. Ba abinda ba ta ji ba, asalima sai da Hajiya ta soma zage-zagen tana danganta dangin Maminta da mayu san nan ta baro wajen. Kuka sosai ta ke yi domin kuwa ta tsorata da iyayyar da Hajiya ke nunamusu. Kanta ya soma sarawa sosai, daman tun soma bikin ta ke fama da zazza i sai dai ta oye. Abinci kuwa ba ta cin na kirki. A hankali ganinta ya soma dusashewa, tun tana jin hayaniyar maro a masu takewa Angwaye baya, har dai ta ji if! Ta shiga wata duniyar. *** Sadda ta farka, ta ganta ne a saman gadon akinsu. A hankali ta ji hannu saman goshinta, ta kai duba ga mai shi. Anti Bara'atu ce ke aikin matsa ruwa a an bokiti tana gogemata jikin. Bata ma san ta farka ba don hankalinta na can ga ba Ummi (Hajiya Raliya) labarin asalin iyayyar Hajiya gareta. "Aminiyata ce, sai dai ta jima ta na ri e da ni a ranta kasancewar a komai ina mata fintinkau. A islamiyya a an ajinmu ni ke zuwa ta farko, na kuma ri e mu amin Headgirl a makaranta, kazalika na rike monita a islamiyya, samari ma na fi ta. Ina fa amaki ba don alfahari ba, sai don na fahimtar da ke silar iyayyarta gareni. Ya zamana har na ha u da Hamza, kuma a lokacin muna tare da ita sai dai bai nuna ita in ya ke so ba. Duk zuwan da Hamza zai yi in sha Allah Saudatu tana nan. Kullum kuma tana cikin kusheshi da nuna ita fa bata yarda da son da ya ke min ba. Allah Masani, ban san me ya je ya dawo ba kawai dai Hamza ya bar zuwa wurina. Na ha ura na auri wanda Mahaifinmu ya za amin bayan tafiyarsa, sati guda da aurena naji batun aurensa da Saudatu. Da yawa sun sha cemin asiri ne, sai dai kuma abinda Allah Ya so ne Ya afku. Bai addaramin aurensa ba. Hatta da mahaifin Saudatu sai da ya tako har wajen mahaifina ya ba shi ha uri don ya ce wallahi ba zai auramata Hamza ba, ba zai iya kallon mahaifinmu da zuri'armu ba idan ya yi hakan. Sai kuwa yayansa ne ya aura auren. A angaren Hamza ma ba da son ran su Hajja ba, sai da aka kai ruwa rana kafin ayi aurensu don Hamza da aka ce an fasa aurensa da Saudatu aramin mahaukaci ya zamar musu har da kwanciya asibiti shi dagaske idan bai aureta ba to fa mutuwa zai yi. Duk uwa ba zata so ta rasa anta ba, wannan ne babban daliin da yasa Hajja da an uwansa suka yarda da auren. AbdulHamid kullum yana hanyar bani ha uri da nunan ba yanda zasu yi, sai da na nunamasa dagaske komai ya wuce kafin ya ha ura ya bari. To kuma duk wannan cin amanar ni ban mata tsanar da ta yimin ba saboda na yarda komai *MU ADDARI* ne daga Allah. Amman tsanar Sadiya? Wannan kuma abu