← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 41

Sashe 4

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

shi, tasu ta zo daya kwarai. Shi kansa yakan nemi wani shawarar a wajenta duk kuwa da bambancin shekarunsu, amman Zeenat akwai hangen nesa. Wannan baiwarta ce. Kurfi kuwa itace kankat dinsu, ba inda bata ta6a ba, ga kokari a makaranta ga kaifin tunani. Hakanan kuma a gefe daya tana da rashin ji. A wannan yanayin motar Yaya Khalid ta shigo gidan. Bak'ar Camry ce mai maidaidaicin kudi. Ya fakata a gefe, tun kafin ya fito ya ke kallon inda suke. Ita kadai ta tsonemasa idanu a cikinsu ganin babban kuskuren da ta tafka, ransa banda zafi ba abinda yake yi, ita yanzu bata jin kunyar zama haka tsakiyar maza babu kallabi? Baisan sadda ya 6alle murfin motar ba ya fito ya nufi inda suke zaune. Tun daga nesa Batul ta hangoshi ta sulale bayan ta fadamusu cikin rada-rada. Ai har 'yar rige-rigen kimtsa kai aka shiga yi. Yana karasowa suka shiga gaisheshi, ya amsa a dake. Ita sam batasan wainar da ake toyawa ba, sai da ta dago kai tana tuntsire dariya har da kaiwa Yaya Hussain duka, za ta yi magana hankalinta ya kai kan Yaya Khalid. Wani wawan mik'ewa tayi, da sauri Yaya Hussain ya cafke Laptop dinsa ganin za ta janyomasa asara. "Don ubanki ina dankwalinki?!" Ya fada cikin daga murya. Da sauri ta hau shafa kai san nan ta durkusa ta dauka ta sanya. Ya yi mata nuni da jikinta. "Ke bakya girma ne ko bakisan kin girman ba? Shigar da yara zasu yi shi kike yi ko? Ku kuma kuna ganinsu a rasa mai yi musu magana?" Ya karashe da kallon tagwaye yana watsamusu banzan kallo. Yaya Hussain da murmushi ya amsa. "Ayi hakuri babban yaya, bamu dauka hakan laifi bane ganin babu bare." "Shari'ar musuluncin fa?" Hassan ya shafi sumarsa bai ce komai ba. Kallonta da ya kara yi ne ya sanya ta wucewa sum-sum cikin tafiyarta ta yanga. Ya kauda kai daga kallonta har ta fice san nan shima ya nufi sashensu.
Chapter 4 · 0% Book details