Sashe 10
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abin yinta. Kusan ma babu amfanin zamansu ita da Ummi saboda ba abinda ake sanyasu ciki, Hajiya da Hajiya Zahida ke yanke hukunci. Hakanan dai suke zaune, kiran wayar Mamin da akai ne ya sa ta mikewa ta bar musu falon ganin yayarta ce Hajiya Bara'atu. Kirif ta kafeta da idanu har ta fice daga falon. Can kuma ta ta6e baki tana jinjina kai, shakka babu ciki ne da matarnan. "Ji, muna lissafi kin yi shiru." Cewar Hajiya Zahida, ta dai numfasa gami da jan guntun tsaki kafin ta dora. "Uhum, ina jinki." Bayan sun kammala kowa ya watse banda Hajiya Zahida, Hajiya ke fesamata abinda ta gani jikin Mami. "Oh, ciki kuma? Yanzu zamu ga kinibibi iri-iri." Hajiya ta ja tsaki. "Can dai su yiwa wanda sukai wa. Ai ni har gobe ina bakin cikin shigowarta gidannan wallahi, kuma sai ta kasance ita daya wajen miji." Hajiya Zahida ta yi kwafa. "Bari kawai Hajiya babba, wannan abu na min ciwo, barin ma yanda shi mijin ke wani rawar kafa a kanta kamar tunda Allah Ya haliccesa bai ta6a ganin mace ba sai a kanta." "Allah Yasa idan Ya tashi ya auromata biyu lokaci daya." Hajiya Babba ta fadi. Hajiya Zahida ta amsa tana dariyar keta. *** Sosai aka shiga gyaran gidajennasu gaba daya, fenti mai kyau aka yi. Yan uwa na nesa sun soma zuwa yayinda gidan ya soma cika. Adda Maijidda da iyalinta duk suma sun hallara a gidan. Ana saura kwanaki uku a soma biki, Baba Hamza ya kira yan matan kaf inda ya bisu da kyautar dubu goma-goma su rike domin yin abinda ba'a rasa ba. Dadi kuwa sun ji, su ka yi ta godiya. Kai tsaye ta nufi sashen da murnarta. "Kakus!" Ta shiga rangada kira tun daga kofa, dake tare da yaranta mata suna hira ta dago ta dubeta. Ta karaso ciki da murnarta ta fada jikinta. "Yanzu Baba Hamza yay mana kyauta mai tsoka." "Da ya ba ku me?" Ta fiddo ta nunamata, gaba daya suka hau sanya albarka da mishi addua ta gari. "Ni kuwa yarannan suma sai kara girma su ke. Ji dai Laila, kamar yau aka haifeta amma naga ta girma." Fadin Adda Maijidda tana karemata kallo, Kurfi sai kunya ma ta kamata. Murmushi kawai ta yi, Adda Fatima ta amsa. "Ai kamar wadanda ake ja wallahi. Suma dai kan nan da wata shekarar mun aurar da su in sha Allahu." Jin maganar aure ta mike za ta fice, daidai lokacin da ya sanyo kai falon shima, hakanan daidai sadda Adda Salamatu ke fadin. "Wallahi ina matukar son naga an hada Laila da Khalid ko don rashin jituwar da ke tsakanin iyayensu." Gabansu ya buga a tare, ita dai sauri take ta cimma kofa, yayinda shi kuma ya ji tamkar ya juya ya koma. Ba tare da saninta ba, ta ci karo da shi, goshinta ya daki kirjinsa, sassanyan kamshin turarensa ya daki hancinta. Ta ja baya da saurinta, kusan tare suka dubi juna, murya na rawa ra furta. "Sorry." Daga haka ta fice. Shi kuwa ya maze ya karasa jiki a sanyaye. Durkusawa ya yi ya gaishesu. Gaba daya suka amsa suna murmushi. A karon kansu sun hango dacewarsu matsayin mata da miji, hakanan sun so su fahimci hange mai kyau da Salamatu ta yi wanda basu yi wannan tsinkayen ba. Hajja dai bata zurfafa da tunani ba saboda bata auki abin mai yiwuwa ba sam. Sai ma ha e gira da ta yi bayan fitar Khalid ta nuna bata aunar zancen. *** Kurfi ta kasa nutsuwa tun bayan shigarta bangarensu. Sanin da tayi dakinsu cike yake da yan uwa ana hira ya sanya ta wucewa dakin Mami. Zaune ta hangota tana waya. Maganar da take fadi ya mantar da ita batun Adda Salamatu. Washe baki ta soma tana ci gaba da sauraronta, ita Mamin ma bata san da shigowarta ba. Wayarta take hankali kwance da Dr Arfat inda take fadamata Baby ya soma motsi kadan-kadan hakanan babu wata matsala da take ji banda yawan bacci. Ji tayi an buga ihu an rukunkumeta ta baya ana dariya. A farko ta tsorata sai dai a hankali ta soma samun nutsuwa jin muryar diyarta. Kurfi ta zagaya gami da zama a gefenta baki ya k'i rufuwa. Mami ta katse wayar ba tare da sun yi sallama ba ta harareta. "Wato la6e ki kaimin ko?" Ta rungumeta tana dariya sannan ta saki. "Allah kuwa aa, na dai manta ban yi sallama ba. Ni yanzu Mami dagaske Baby za ki kawomin?" Ta tambaya cikin zak'uwar son jin amsar. Mami ta murmusa. "Kada dai naji bakinki kin fadawa wani ko wata." Ai batasan sadda ta mike ta buga tsalle ba gami da yin watsi da dubu goman hannunta wanda take ya barbazu a tsakar dakin tana mai hamdala. Mami ta hangame baki tana duban kudin kafin ta dubeta tana dariya. "Ke, duk murnar ce wai? Wa kuma ya ba ki wannan kud'in?" Tana dariya ta amsa. "Yanzu fa Baba Hamza ya bamu. Allah kuwa Mami naji dadi sosai, kimin addua Allah Ya rufemin bakina kada na fadawa kowa. Ni dai gaskiya ba zan iya celebrating ni kadai ba." Dariya sosai Mamin ta yi don ba karamin farin ciki Laila ta sanyata ba a wannan wautar da take yi. "Maza tafi ku yi da Abbanki." "Lah, ya sani? Bari naje." Daga haka ta juya a guje ta bar dakin. Mami ta kara kyakyatawa can kuma girgiza kai gami da jan guntun tsaki. "Allah Ya shiryamin ke Laila, ban san yaushe za ki girma ba." Daga haka ta shiga tattara kudaden. Ita kuwa tana zuwa sashen Abbanta ta hau kwalamishi kira tun daga kofa. Tana shiga ya bar abinda yake a Laptop dinsa gami da cire gilashin idonsa. "Lafiya dai?" Ta karasa ta zauna gami da tankwashe kafafu, har wata kwalla ta taho mata don tsabar murna. Hannunta ta rike. "Nayi fushi, ashe Mamina za ta kawomin baby ba ka fadamin ba ko?" Ya yi murmushi har hakoransa suka bayyana, gami da dafe kanta. "I'm sorry my Angel, ai gashinan da lokaci ya yi kin sani ko?" Ta hau gyada kai tana dariya har batasan sadda ruwan hawayen ya zuba ba. Sai hannun Abba ta ji yana gogemata. "Yauwa, yanzu mu ci gaba da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya, da bata kulawar da ta dace. Wannan ta fi bukata a yanzu." Suka yi dariya a tare. Tun daga wannan rana ta shiga nan nan da Maminta, ko kicin za ta shiga aiki sai ta shiga itama, a baya ba abinda ta tsana kamar girki don bata iya komai ba a wannan fannin. Amma yanzun za ta shiga Mamin ta sanyata motsa wancan, kuma ki tace wannan. Abin kam har mamaki yake ba Zeenat. Ana gobe biki ne, bata samu zama ba, suka fice zuwa kunshi. Kurfi ba kitso tayi ba, retouching ta je akai mata ta hada gashinta ta tufke a tsakiya. Sun yi gyaran jiki kadan a iyaka kwanakin da ake yiwa amare, hakan yasa suma fatansu ya yi kyau da shek'i. Sai kusan Magrib suka dawo daga wajen kunshi. Kowaccensu ta kama hanyar sashensu. A gajiye likis suke. Amma fa kwalliya ta biya kudin sabulu don kuwa ba karamin kyau kunshinsu ya yi ba. Kowa ya gani sai ya yaba. Su Rahila gaba daya tare suke kwana a sashen su Kurfi. Don haka dakin ya koma a cike har su biyar a maimakon su biyu da suka saba kwana. Wannan ya sa wasu har a katifa. Washegari aka soma biki da kamu wanda zaa gabatar a Marnaf Event's Center da ke a can unguwar yan gayu don haka sai yamma. Komai ya tafi lafiya lau. Washegari lalle da lakca kawai akai, karfe takwas kuwa aka hau shirin zuwa Dinner. Kurfi sai faman fente fuska take da kwalliya gaban madubi. French lace mai kalar sea green suka sanya da head bak'i, gaba dayansu dinkin doguwar riga akai musu. Sun fito sosai a yanmatansu. Kurfi kuwa duk inda ta sanya kafa a bangarensu, zaa shiga yabawa da nuna irin kyawun da tayi. Gaba daya suka fito daga gidan zuwa harabar gidan inda motoci su ka yi parking. Motoci ne rantsastsu na gani na fada. Abokan angwaye na tsaitsaye yayinda wasu suka soma shiga gami da jan motar . Sai wulka idanu suke don ganin wacce ya dace da su shiga. "Ku nifa wallahi ba zan hau motar marar tsada ba, sai na ga wanda ya dace a samarinnan." Dariya suka kwashe. Hindu diyar Adda Salamatu ta ce. "Wallahi ban ga laifinki ba." Tasleem ta cafe. "Atoh, nima ina bayanki." "Adon gari." Suka tsinci murya a gefensu. Gaba daya suka waiga, ganin mai shi ya sa Kurfi wani kyakkyawan murmushi. "Lah Dost, kwana biyu? Saukar yaushe?" Ya shafi sajensa yana dariya kasa-kasa. "Dost, jiya na dawo. Ya garin? Irin wannan kwalliya ai sai ace ke ce Amaryar." Dariya tayi gami da yin wani farr da ido, ko ba komai mace ce ita mai son yabo. "Na gode Dost, nasan dama kai kadai za ka gani ka yaba." Ya yi murmushi. "Toh ya na ganku tsaye?" Ta marairaice fuska. "Mai zafi nake hawa, ba motar kowane kazami nake son shiga ba." Wata dariya ya kyalkyale da ita har ya sanyata itama, ya riga da ya san halinta shiyasa ma suke shiri don kuwa shima mutum ne mai son harka ta wayewa da barkwanci. "Allah Ya shiryeki Dost, toh yanzu tsaya, za ki iya hawa motata? Wannan an kazamin." Ta yi dariya, yana tayata. "Kai don Allah, ai ka wuce ajinnan." Ya dan age gira kadan da murmushi. "Really? Oya muje toh, amma fa kun min yawa kin sani. Ko a musulunce ba zan iya aurenku duka ba, hudu kawai sun isa." Dariya sukai. Ta dubi su Tasleem, ba musu ta za6i mutum uku. Da Tasleem, Rahila da kuma Hindu. Saura su na ya haka? Gwalo kawai tayi musu suka bi bayan Dawud. "Kee, yayanku fa yana wurin ba matsala?" Fadin Tasleem tana matse hannun Kurfi cikin nata. Ita ta ma manta da zaman Yaya Khalid, sai san nan ta hangeshi jingine jikin motarsa kusa da ta Dawud su na hira da Zahraddeen d'a ga Adda Fatima. Kallo daya za ka yi musu ka fahimci ba sa'anninsu bane, don