← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 41

Sashe 12

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk kuwa da ta san yanda sukai wahala a karatun Arabi, su basu yin rabinsa a yanzu. Ganinsu a MARHABA MALL ya sanya ta washe baki, ba fa ta ta a zuwa ba. Haka kawai sai ta tsinci kanta da murmushi. Yana ankare da hakan, shima bai san sadda ya murmusa din ba. Har suka shiga tana kallon duniya, an awata wurin kamar ba'a kasar Hausa ba. Yana parking ya dubeta. "Ina zuwa." Ai ji tayi kamar ta kurma ihu, ta nemi shakkarsa ta rasa har bata san sadda ta karya harshe ba. "Yaya na zo na raka ka?" Sai ta so ba shi dariya ma, ya maze. "No, ki dai jira yanzu zan zo." Yana shirin rufe motar ta kara daga murya. "Yaya don Allah fa." Ta furta tamkar tayi kuka. "Fito." Ba batun jira tuni ta fito ta gyara zaman karamin mayafinta. Nan da nan ta koma Kurfinta ta ainahi mai fara'a da rawar kai da kuma yanga. A can asan zuciyarta kawai hangota take yi tana hurawa su Tasleem da Zeenat hancin ta rigasu zuwa Marhaba Mall, banda wannan ma kuma, ta jera da wanda suke mishi kallon tsadadde mai wuyar samu. Tare suka jera su na tafiya har zuwa ciki, kamanninsu a zahiri yake don kuwa Yaya Khalid tsawo ne zai fi ta da shi sai kuma dimple da kuma hasken fata. Ita fatarta bai kai nashi haske ba. Kamar an ce ga adadin takun da zasu yi su shiga Marhaba Mall din, haka suke taku daya-daya kusan ma a tare. Kurfi ganin gayu sosai a wurin ya sanya ta kara chanja taku gami da sakin fuska sai dai ba sosai ba gudun kada a kirata 'yar kauye farin shiga. Su na shiga ya nufi bangaren kayan zak'i. Nan ya bata umarnin daukar abinda ta ke so. Basket ta dauka ta soma jefa duk wani kayan kwalam da ta ga ya yi mata har ma da wadanda bata sani ba ko zata iya ci ko aa, a kasan ranta kuwa har murna take ta samu na dorawa a Instagram, san nan za ta yanki su Hindu da shi. Kamar an ce ta daga kai, ta hangi daya cikin samarinta wadanda ta ta a yi musu aryar suna da lambar waya. Duk da ba za ta iya tuna sunansa ba, amma ta san tare da Zeenat da Tasleem ne alokacin da suka hadu da shi. Da saurinta ta juya baya ganin ya tunkarota, a juyawar da tayi ta hada ido da Yaya Khalid shi dinma wajenta ya nufo. Gaba daya ta diririce, Allah Ya taimaketa ashe saurayin bai ganta ba, sai dai ta sha mamaki da ta ga ya mikawa Yaya Khalid hannu sun gaisa a mutunce, ganin haka ita kuma tayi saurin shan corner zuwa daya bangaren na kayan cima. Ba abinda ta dauka sai kalle-kallen da ta ke yi. "Bani fa da kudin siyan duka shagon, idan za ki taho mu tafi ki taho." Muryarsa kawai ta ji, ta kuma hangi fitar saurayin, sai san nan ta sauke ajiyar zuciya har da wani murmushinta. Ai ko me zai ce ya gama yi mata komai tunda ya fiddata a layin sauran yan uwanta da basu ta6a taka shagon Marhaba ba. Ya daga gira kawai yana kallonta ganin yanda take ta wani murmushi da kwarkwasa idanu kamar wacce ke gaban saurayinta, sai dai bai ce uffan ba. Ta yi gaba ya bi bayanta har zuwa wajen cashier. Aka yi lissafi ya biya, maimakon ya bata ledar sai ya rike har suka karasa gaban mota. Yana zama ya dauki wayarsa da ya barta a mota tana chaji. Missedcalls din Hajiyarsa ne sai kuwa na Mama Zahida sai na Mamin Kurfi. Mamaki ya sanyashi furta maganarsa a fili. "To lafiya kuma wannan kira?" Kurfi da ke kallon wasu ma'aurata larabawa wadanda ke kokarin shiga mota, ta dubeshi da sauri yayinda gabanta ya buga dam! Maminta kawai ta tuna, kada dai itace ba lafiya. "Mamina ce?" Ta tambaya ba da zato ba, uffan bai ce ba har sai da wayar Mamin ta shiga san nan ya amsa. Tambayarsa tayi ko Laila na tare da shi, ya tabbatar da hakan gami da ce mata yanzu za su taho. Ta yi musu fatan isowa lafiya daga nan ya share bai kira Hajiyarsa ba ya tashi motar. Har suka isa gida ba wanda ya kara magana, ita dai har a sannan jikinta a sanyaye don bata san meke faruwa ba, ta dai fahimci da Maminta ya yi magana yanzun a dalilin sunanta (Mami) da ya ambata. A kofar gidan sun iske da yawa sun dawo daga wurin Dinner, yayinda wasu kuwa yanzun ake kawosu. Bai tsaya anan ba ya yi horn maigadi ya bude gate. Bayan shigarsu nan Kurfi ta hango tashin hankali don kuwa Hajiya da kanta ta hango zaune saman daya a cikin fararen kujerun karkashin bishiyar mangwaro. Yan korenta su Hajiya Zahida na tsaye tare da wasu cikin yan uwanta ciki kuwa har da Hafsat da su Aliyu. Gabanta kawai ke bugu da sauri-sauri, ba ta yi dana sanin shiga motar Yayan Aliyu ba sai yanzun, ta manta da duk wata gaba da ke tsakaninta da su. Tana shirin fita ya dafe hannunta da tattausan tafin hannunsa wanda sanyin Ac na mota ya gama ratsawa. "Ban son shirme, mene duk kika wani rude? Ba ruwanki da su, ki wuce ni zan yi magana da su." Kai ta gyada tana kallonsa a hankali kuma ta zame hannunta, shima kan ta karasa ya cire. Budewa tayi ko ta kan ledojin ba ta bi ba, sai da ya dakatar da ita ya mik'amata. Hannu na rawa ta kar6a ta wuce. "Ke!" Tsawa Hajiya ta dakamata wanda ya sanya ta sakin ledar ta juyo a firgice. Hafsat da Aliyu wadanda tun tahowarta hankalinsu ke kan tambari da kuma sunan jikin ledar wato Marhaba, su ka ji wani malolon bakin ciki da takaici ya mamaye zukatans u, ba domin Yaya Khalid da ke tunkarowa ba, ba abinda zai hana su dauke ledar su hanata. Ba ta kai ga karasawa ga Hajiya ba, Yaya Khalid ya kira sunanta gami da bata umarnin tayi ciki kawai. Ba musu ta juya ta dauki ledarta kuwa ta nufi bangarensu da sauri, tana jin tashin muryar wata yar uwar Hajiya tana fadin Khalid bai da kunya ya zama shanyayye. Ita dai tunda ta lalla6a ta ji ta a sashensu hankalinta ya kwanta. To nan ma dai a falo ta iske Mami tare da su Anti Rumaisa da Anti Bara'atu. Anti Rumaisa ta soma tambayar inda suka je? Bata bar komai ba dangane da abinda ya faru, sai dai ba ta yi kuka ba ta daure saboda kada ta kara tayarwa Mami hankali. Gwara dai su ji abinda ya tsayar da su kada wani abun daban. Nan suka shiga salati, Anti Rumaisa ta ce. "Wallahi ban san meke damun Saudatu ba, kullum cikin jaye-jayen magana, ita da abu ba ya wucewa a wajenmu an fadamata za ta sha ruwa a gidannan?" Dariya Anti Bara'atu tayi, hankalin Kurfi yana kansu, burinta su dora don ta matsu dama tasan dalilin tsanar duk da dama takan yawaita jin Hajiya ta sanyo har Anti Bara'atu a cikin masifarta idan tana yi domin su. Mami ta katse komai ta hanyar fadin. "Laila wuce dakinku." Ba musu ta mike, sai kuma ta koma ta budemusu kayan kwalam da zummar su d'iba, Anti Rumaisa ce kawai ta dibarwa yara alawa tana yi tana ikrarin Yayannan na ji da ita. Ita dai baki ta ta6e tasan yau din ma wata sa'a ce ta ci a kansa har hakan ta kasance. Tana shiga gaba daya suka shiga kallonta da ledar hannunta. Ai gaba daya suka saki wani ihu har da masu tsalle, ta kuwa tuntsire da dariya. Nan fa ta hau basu labarin yanda aka yi suka fito tare har da dawowarsu. "Cabd'i, amma fa wallahi kin jawo ruwa, ke kinga yanda Hajiya ta zo har nan ta hau Mami da fada?" Zaro ido Kurfi tayi, cike da faduwar gaba take duban Tasleem. "Don Allah dagaske?" "Wallahi, ai Hafsat ce dama ta ce mata wai Yaya Khalid ya daukeki a mota kun bar wajen party kuma batasan inda za ku je ba. Wai har hannu ya rik'emaki." Jin wannan kazafin ya sanya idanunta cika da kwalla, ba ma wannan ba, ta yi sanadin da aka ta6a mahaifiyarta. "Ke kar fa ki damu kanki, Mami a take ta bata shaidarki, ta kuma kara da fadin ba wannan tarbiyyar ta yi miki ba. Ke dakyar dai ta fice daga dakin, ba wanda ya tankamata." Sauke nannauyar ajiyar zuciya Kurfi tayi kafin ta furta Allah Ya kyauta. Zeenat dai na kallonsa sai dai jikinta duk ba kwari musamman da ta ji Yaya Khalid ne ya kai Kurfi Marhaba Mall, haka kawai. Kurfi ce ta lura da ita ta kai mata duka a cinya. "To Majnuniyar Yaya Khalid, kema kishin kike?" Sai a san nan suma hankalinsu ya kai gareta, ta ja guntun tsaki gami da yin yak'e, cikin harara ta ce. "Aa kin manta, bakin ciki." Dariya kawai Kurfi tayi ta share don tasan tatsuniyar gizo bai wuce na 'koki. Ita batasan ma Yaya Khalid din bata hangenshi a mijin aure ba. *** Suka wayi gari ranar lahadi da shirye-shiryen daurin aure. Gaba daya iyayen sun hadu a can bangaren bayan gidan inda suke aikin manyan tukwane na abinci. Yan matan kaf dinsu yau farar shadda suka sanya sai dai kowacce da kalar dinkinta. Kurfi riga da siket akai mata, aka jera stones a gaban rigar. Ta cakare kwalliya, batu na kyau da haduwa kuwa, sai ka rantse daga jinsin larabawa ta fito. Sai dai gadon kyau daga suka yi shi ita kuwa za ta iya cewa mahaifnta. Saboda bafulatana ce ta gaske, mai yalwar gashi da hasken fata da kuma tsawon karan hanci. Gaba daya suka fito suka shiga bangaren sauran iyayen da su gaishesu, dama ba ta yi karambanin zuwa bangarrn Hajiya Zahids da Hajiyar Khalid ba, tasan yanzu sai a kashemata annashuwarta. Ganin sun nufi nan ita kuwa kawai ta yi sashen Raliya, sun dan ta6a hira sannan ta fito ta yada zango a wajen Hajja. "A'a, yau wa nake gani haka kamar balarabiya?" Jin furucin sai kanta ya ara
Chapter 12 · 0% Book details