Sashe 11
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuwa aji da kyau da kudi duk sun kere musu, sun sha adonsu, Yaya Khalid blue shadda ya sanya tirarriya, ya yi karin hularsa mai kyau, farar fatarsa sai kara shek'i ta ke yi a hasken fitilun farfajiyar gidan. Shi kuwa Zahraddeen maroon shadda ya sanya. Shima dai farin ne amma bai kai Yaya Khalid fari ba. Ya yi kyau tsaf sai dai siriri ne shi a kan Yaya Khalid da yake da ingarman jiki. Toh shi ma Dawud din ba wani haske ne da shi ba, za'a iya kiransa da black beauty, shima anko sukai da Yaya Khalid hatta da hular kansu iri daya ne kasancewarsu AMINAN JUNA. "Wai ba za ki magantu bane!" Tasleem ta katsemata tunani. Numfasawa tayi ba tare da ta ce komai ba sai yamutse fuska da tayi. "Ashe dai Yaya Khalid ya an ha u ba laifi. Yanayinsa ma kamar wani aljani." Wani irin dariya su Tasleem suka sanya, itama tana tayasu. Suna tunkararsu, su dinma idanunsu yana kansu, ganin haka ta ci magani ta dauke kai kamar bata ganshi ba. Dawud ya cire lock na motar ta hanyar amfani da mukullin. "Dost, ku shiga ko?" Ta gyada kai kawai, gaba daya suka shiga ita kuwa ta nemawa kanta mazauni a gaban motar. Sai san nan ta samu nutsuwar kallon gefen Yayannasu. Ya maida hankali ga danna waya bai ce komai ba. Kusan a tare su Tasleem suka saki dariya asa- asa. "Kai, wallahi na dauka zai dakamana tsawar don me za mu bi abokinsa." Fadin Rahila kenan. "Wallahi nifa tun da muka tunkarosu kar ki so ki ji yanda cikina ke mur awa, wai! Yaya Khalid ko masifa!" Tasleem ke maganar tana rike ciki. Dariya su ka sanya. Kurfi tuni ta maida hankali wajen danna waya. "Yar duniya, kin mana shiru muna jimami ko?" Ta ja guntun tsaki kawai. "Ku ku ke wani tsoron mutum kamar wani mala'ikan mutuwa, nifa ina tsoronsa ne kawai idan nasan nayi laifin da zai iya kai min bugu ko ya budemin wuta. Amma haka kawai don shi sarkin mafa ata ne sai ya yi mana fa an da ba dalili?" "Hakane kuma fa, ba wannan ba, Allah kuwa yau ya yi bala'in kyau. Ke su duka ma." Fadin Rahila. "Ashe ba ni kadai na yaba ba, kwalliyarsu daban wallahi. Nima sun burgeni don tun dazu idon yana kansu. Yanzu Kurfi idan wannan Dost din naki ya ce yana sonki ai kakarki ta yanke sak'a." Hindu ke wannan sambatun. "Ku kam ai tunda o'o ta kirashi da aljani ku fahimci cewar bala'in ha uwa ya yi." Fa in Hindu a karo na biyu. Kurfi dai guntun tsaki ta ja ta maida kai ga kallon motocin da suke ficewa daga gidan cike da yan biki take, amma dariyarsu a kunnenta. "Kuma fa hakane, yo wannan wani abin arziki ta sani, yabon ma ai na iskanci ne. Ai ita wai a duniya ba zata auri mai kyau ba saboda kishinta. Nasan maganganunnan naku ba burgeta zasu yi ba." Murmushi tayi anan jin abinda Tasleem ke fadi, sai lokacin ta magantu. "Yauwa 'yar kirki fadamusu kam. Wai mu yaushe zamu bar wurinnan, Dost ya barmu sai hira suke abinsu." Ta share wancan maganar. Basu dau kuwa lokaci ba sai gashinan gaba daya sun nufo wurinsu. Dawud ya shigo. Ya tashi motar suka fice inda shima Yaya Khalid ya shiga ya tashi tasa, ya ja Zahraddeen a gefensa. Suka bi bayansu. Wuri ya cika tam! Koda isarsu hatta da Angwayen sun halarta. Dawud ya dubi Kurfi ganin ta fiddo waya daga purse din hannunta za ta nufi Angwaye. "Kai, Dost, yaushe kikai abar zamanin ba labari?" Sai fa a sannan ta tuna kuskurenta na zuwa da waya. Ta diririce, Tasleem da sauri ta tare yayinda ta ce ai nata ne ta bata ajiya. Da wannan suka rufe bakinsa gudun kada maganar ta je gun Yaya Khalid duk kuwa da cewar sun san ba halinsa bane. Selfie sosai ta yi da Twin cousins dinta musamman mutuminta Yaya Hussain. A garin hoton ne ba ta sani ba ta ja baya ta take kafar Aliyu, ai kuwa ya sakarmata kara gami da hankadata tayi taga-taga kamar za ta fadi. Wayar kuwa tuni ta bugu da k'asa. "Dalla can banza jaka kawai!" Ya fadi yana mai rije yatsar kafarsa. Idan ranta ya yi dubu ya 6aci, batasan sadda ta daga murya cike da rashin kunya ta amsa ba. "Kai ne dai banza jakin ba.." Ya kuwa kwasheta da mari, ta rike ha6a idanunta cike da kwalla. Ga gayu a wurin duk ana kallo saboda kowa ya karkata hankalinsa ga Angwaye da Amarensu ana hoto kafin su shiga. Hussain ya juya a fusace ya haushi da fada kamar zai ari baki, Aliyu ya bar wurin yana kananun maganganu. Ta dauki wayarta za ta bar wurin Hussain ya rike hannunta don yasan aikin bai wuce ta je ta sha kuka. To anan dinma hawayen ta shiga sharewa, yana bata hakuri. Karshe ganin camera na yawo kansu, ta zame hannunta ta bar wurin tare da Tasleem. Tasleem na mitar wulakanci irin na Aliyu haka suka nufi bathroom, a gaban madubi ta gyara fuskarta, sai dai fa shatin yatsun Aliyu ya kwanta a samansu. Ba ma wani abun ta shafa ba hakanan suka shiga ciki ranta kuwa gaba daya a jagule don ko digon fara'a babu, ba kamar yanda ta shigo taron ba. Kujerun zaman maza biyu ne da mata biyu, abin a lissafe yake dai na yan boko. Ta nemi wuri kawai daga can lungu daga baya ta zauna, Tasleem ba nan ta ke son zama ba sai dai ganin haka itama kawai ta bita su ka zauna tana bata hakuri. Suna nan zaune Angwaye da Amaren suka shigo. Tuni aka chanja kid'a mai taushi. Fitilun dakin taron kuwa sai chanjawa suke daga ja, blue, green da kuma fari. Kusan kowa ya tashi ya nufi wajensu suna tafe ana musu hotuna, Tasleem itama mikewar tayi ta nufesu don hoto. Ita dai tana zaune tana danne-dannen waya don komai ya fita a ranta. "Ke." Jin muryar Aliyu ya sa ta dago kai ta dubeshi fuska a daure. Kujera ya ja ya zauna, tare suke da wani abokinsa wanda ya sha wani shegen aski sai taunar cingam yake yana mata kallon yan bana bakwai. Da yatsa ya soma nunata. "Ke don ubanki har akanki za'a disgani a gaban jama'a? Ko uwarki bata isa ta yimin abinda akaimin yanzu ba na kyale ban dau fansa ba. Wallahi kin ji na rantse, sai na koyamaki hankali yanda sai kin yi kuka da idanunki. Na kuma kara fada, ke banza ce! jaka ce!!" Shiru ya yi don burinsa ta tanka, sai dai ga mamakinsa bata ce komai ba, abokinsa ne ya hau ta6a shi. "Kai ga fa wannan Brother naka yana kallonmu." Yana waigawa kuwa ya hada ido da Yaya Khalid da ke zaune a bangaren hagu tare da su Dawud, sai kuwa ya wayance da murmushi da daukar lemu gami da kur6a. Ita gaba daya ma sai ta mike ta bar musu kujerar zuciyarta na tuk'uk'i. Don me za ta zo taron da za'a dunga zagin iyayenta ba ta da abin yi kuma? Alkawari ta daukarwa Maminta ba zata kara sa'in'sa da Aliyu ba, dazun ma zuciya ce ta ciyo ta. Yanzu kuwa ko don lafiyar Maminta da gudun 6acin ranta ba za ta tanka mishi ba. Don haka sai ta nufi hanyar fita, bata tsaya ko'ina ba sai harabar wurin inda tsilli-tsillin an biki ke harkokinsu, bayan wata mota ta samu inda akwai kujeru tayi zamanta ta hada kai da gwuiwa. Kuka ta shiga rerawa abinta, motsin da ta ji a gefenta ne ya sa ta dago kai. Yaya Khalid ne, cikin yanayi na son sani ya ce. "Me akai miki?" Ta hau share fuska gami da girgiza kai. "Tambayarki nayi fa. Aliyu ne?" Kamar ta tambayi yanda akai ya sani sai dai tayi shiru. Nan ma kan ta kara girgizawa. "Aa." Ya yi shiru, can kuma ya jinjina kai. "Ok kada ki fada din, amman ki gaggauta goge fuskarki ki shiga ciki, idan kin san ba za ki zauna a bikin ba me ya kaiki zuwa?" Nan ma ba ta ce komai ba ta share fuskar sosai ta mike ta nufi ciki. Ganin dai da gaske ba fadamasa za ta yi ba ya sanyashi dakatar da ita. "Kinga." Ta juyo tana kallonsa, shi dai kullum ba walwala a fuskar. "Gida za ki koma ne?" Da saurinta kuwa ta amsa da eh don bata ga amfanin kara koda second a wurin ba. Ya juya ya soma tafiya kafin ya bata umarnin biyoshi. Bata ko damu da yiwa kowa sallama ba ta bi bayanshi, wannan duk ya faru akan idanun Hafsat wacce tun daga fitowarsa itama ta fito don ta riga da kanta ya gama fasuwa ganin shi ke zaune a kusa da ita. To shi dinma dalilin zaman saboda Dawud ya riga da ya zauna ba yanda ya iya. Amman ita nan duniya gani tayi Yaya Khalid kyau tayi mishi shiyasa bai k'i suka zauna a wurin ba. Dalilinsa ne ta za6i zaman bayan kujera fiye da gaba. Ganinsu tare da Kurfi ba karamin tadamata hankali ya yi ba, yanda ya dunga tambayar abinda akai mata har zuwa sadda ta shiga gaban motarsa duk ba abinda bata gani ba. Nan da nan zuciyarta ta darsamata lallai akwai wata alaka da ke gudana tsakaninsu. *** Shi kuwa waya kawai ya yiwa Dawud ya sanarmasa tafiyarsa, bata san me Dawud ke fadi ba ta ji dai ya ambaci kalmar Sorry kafin kuma ya katse kiran. Ya dubeta, har lokacin fuskar a daure tamau. Rashin jin ma ya yau babu damar yi tunda ba walwala. Har zai nufi gida sai ya chanja shawara. Kai tsaye ya dauki hanyar zuwa MARHABA MALL. Hankalinta gaba daya ma yana wajen tunani na daban, ta dai lura ba gidan ya nufa ba, a hankali kuma ta ji ya kunna karatun Al kur'ani. Nan ne ta ji wani sanyi ya soma ratsata, a dan sace ta dubeshi. Ashe dai yana da audio na ira'a. A farko ta dauka shi boko da boko kawai ya fi ba muhimmanci, sai kuma sannan ta tuna yanda yake musu idan su kai fashin makaranta.