Sashe 38
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau fa jin ranar su urfi jinta su ke tamkar sallah. Har nafila sukai su ka ara godiya ga Allah. Habiba da Lauratu su kansu sun yi murna, Faruk da Jawad da na sani duk ya addabi zu atansu tun bayan da aka raba Hajiya da gidan aurenta. Ya yanke shawarar Aliyu a waya ganin ya kira Yaya Hassan da Hussain sun nuna basu ga aibun haka ba. *SLADE PARK, OXFORD, UK.* Yana zaune ya saka system a gaba yana kallon film in Game Of Thrones, hankali kwance ya ke faman busa tabar sigari bayan kammala yin kalacin safe. Yana jinsa fayau babu wata damuwa. Wayarsa ce ta soma ringing, har ta katse bai da niyyar kalla ballantana kuma ya auka. Sai a karo na uku ne ya ja wayar a zafafe yana dubawa. Zuciyarsa ta anyi sanyi ganin wanda ke kiran. Faruk ne. "Hey Sadaukin Hajiya, what's wrong?" Daga can Faruk ya amsa. "Hajiya, Daddy ya saki Hajiya." Ya lailayo wata uban ashariya ya kunduma. Ya ara da fa "Akan uwar uban me?!!!" Faruk ya zayyane mishi komai da komai. Slowly slowly ya ji jikinsa na sanyi, dama yasan wataran hakan zai iya kasancewa. Ko ba komai yana jin labarai kuma ya na ganin abubuwa a zahiri yanda aikin asiri ke juyewa. "Ok." Shi ne abinda ya ji zai iya furtawa kafin ya katse kiran gaba aya. Ba zai iya tantance yanayin da ya tsinci kansa ba, kai tsaye ya shiga laluben wayar an uwannasa. Yaya Hassan ya soma kira. "Bro, ka ji abinda ke faruwa a babban gida?" Yaya Hassan ya amsa da "Me ya faru?" "Mutuwar auren Hajiya." Nan da nan Hassan ya shiga fa a da tambayar wanda ya fa amasa don kuwa Daddy ya ce daga shi har Aliyu ya hau gya a kai kamar adangare. "Ok, ok." "Ok da me? Hajiyarmu ba ta kyauta mana ba, sam ba ta au hanya mai illewa ba. Kaima da ka ke biyemata ba abinda ban sani ba. So tun yanzu zai fi maka sau i ka tuba ka nemi gafarar yarinyar da ka untatawa ba gaira ba dalili." Aliyu bai yi karambanin neman wayar Hussain ba don ya san duk bakinsu aya. Tabar ya murje acikin ash tray sannan ya mi e tsaye. "Laila! Laila!!" Ya furta sau biyu ransa na tafarfasa, mene dalilin ma tsanarta tun farko? Ya watsawa zuciyarsa tambayar da nan take ya samu amsar. Ta saba da Daddy insu fiye da yanda su suka saba da shi. Basu wani sakewa da Daddy su sha hira, wannan sai Yayansu Khalid, ga shi kuwa, kullum kallon mai laifi Daddy ke mishi. 'Amman ita fa Laila, me ne matsalarta da hakan? Mami ko kallonsa da mai ata musu ba ta ta a yi ba, murmushi koyaushe bai gujewa saman fuskarta. Ya tuno sadda ya yiwa iyarya dukan kawo wu a, maimakon Mamin ta fusata sai ma murmushi ta yi gami da ba Hajiya ha uri duk kuwa da cewar iyarta ce mai gaskiya. A hankali ya ji wani irin sanyi, sanyin da bai ta a jin irinsa a zuciya ba. Can ya tuna mahaifiyarsa mafi soyuwa a ransa. Ransa ya aci, zai so kiran Daddy ya ba shi ha uri, sai dai sanin da ya yi ba sauraronsa zai yi ba yanzu ya kyale zuwa anjima. Ya yanke shawarar kiran Hajiyarsa. Yana kira kuwa ta auka tana kuka mai cin rai. "Hajiyata, ki yi ha uri na ji komai. Zan yiwa Daddy magana." Hajiya ta soma magana a raunane. "Kyaleshi Aliyu, ba zai saurareka ba. Alhajinku ya ci min mutunci ga ban mutanen da basu auke ni komai ba. Rabu da shi, ina nan inda nake zai kawo kansa." Aliyu ya girgiza kai kamar tana ganinsa. "No Hajiya, wannan ba magana bace. Yanzu lokaci ya yi da ya ci ace kin girmi zubewa gaban wasu attai kina arin i don a yi miki asiri. Ya isa hakanan. Yanzu kawai ki kwantar da hankalinki ki ba Daddy damar ya huce sai ki ro i gafara tunda kin ga dai kin riga ki yi abinda ki kai. Dama fa wa annan duk wasan yara ne kema kin sani, kamar yanda ki ka sani watarana zai karye. Zancen ma ki ara an wuce wajen. Be a good woman for now, ki nemi gafararsa da na su Hajja." "Dalla can rufen baki! Ba dai ni Saudatu ba, wallahi na wuce wannan matakin. Hajjar banza da wofi! Ko Alhaji zai mutu, ko zan yi yawo asa zuwa asa sai na koma gidana kuma sai na ga bayan Laila. Ita ce ta dunga rushemin aikina da karatun Al ur'ani, ita ta hana afkuwar komai! Na tsaneta na tsani kaf dangin Badia'atu!" Daga nan ta katse kiran a fusace. Aliyu ya yi shiru, gaba ayansu Allah aya suke bautawa, sun san girma da daraja na Al ur'ani, kenan da shi Laila ta yi amfani wajen karya sammun da Hajiyarsa ta yi? Zuciyarsa ta shiga wani irin tunani, ya kasa gane komai, ya kasa tantance tsakanin ruwa mai sanyi da na zafi alhalin abin a bayyane ya ke. Ganin ya kasa tuna komai kawai ya mi e ya kashe na'urar kwamfutar ya fa a wanka. *** Ba jimawa sai ga Yaya Hussain da Yaya Hassan. Matansu ba zasu je ba don kuwa ita Rahma laulayi ta ke fama da shi, ita kuwa Aisha aramin ciki ne har na watanni hu A yau ne ta ji tana son yin kwalliya, ko ba komai yau kam burinta ya cika. Mafarkinsu ya tabbata. Ta bu e sif insu ta ciro wata atamfarta red mai sirkin brown a jiki. inki ne na doguwar riga wanda ya yi kyau sosai, shi ta sanya ta gyara fuskarta da hoda da kwalli. Ta sanya man le e ka an. Ta tsaya kallon kanta a madubi, sosai ta ke ganin ramar da ta yi gami da an duhu. Turare mai sanyi ta feshe jikinta da shi. Daidai sadda Batul ta shigo domin kiranta. Ta tsaya tana dubanta da dariya. "Kai Kurfi, wallahi kin yi tsaf." Kurfi ta dara. "Taho mu tafi su Daddy har sun fito, ga Yaya Hassan ma sun zo." Suka fito, a farfajiyar suka ris i mutan gidan ana arin shiga mota. Daddy ya dubi Baba Mudassir. "Ina shi Kamal da Usman?" Ya aga kafa a rai a jagule. "Laifi su kai, Abdullatif su ka kira su ka fa i mishi wai na saki uwarsu. Shi ne yaron nan ya kirani da kuka hankali a tashe. Sun riga sun san matsalar yaron nan da ciwon irji. Yanzu idan suka jaza mishi wani ciwon fa alhalin yana can wata uwa duniya ya zamu yi?" Daddy ya gya a kai. "Gaskiya ne, shiyasa nima na hana yarannan fa a wa yayansu da Aliyu. Na fi aunar komai ya lafa kafin nan." Yaya Hassan ya jefawa Faruk wani kallo, Faruk ya sadda kai asa yana kunkuni don yana zuwa shi ya soma tunkara ya bu ewa wuta. "Wannan fa ban ma kar eta hujjar da za ka hana yara zuwa ba, dukkanmu masu laifi ne. Dole mu je wa Hajja kanmu da kwarkwatarmu." Kai tsaye ya sa Faruk kiran Kamal da Usman, ba jimawa su ka fito kowa ya shiga mota. Kurfi na tare da yayanta mafi soyuwa gareta a gaban mota, su Munira ne a baya. Motoci uku su kai. Yaya Hussain, ha uri sosai ya ke ba Kurfi ta nuna komai fa ya wuce. "Ba ku da laifi, ban ri e ku da komai ba a raina." Yana murmushi ya ara fa "To ina fatan dai har Yayan namu an yafemasa?" Anan ne ta yi if, ta kauda kai tana duban titi. Sau biyu yana maimaitawa ya ji ba amsa. arshe ma ta dubeshi. "Yayana ya Anti Rahma da jiki? Batul ke fa amin ba ta ji da i ba." Ya fahimci maganar ce ba ta so, ya numfasa. "Jiki da sau i, ta warware sai rashin warin jikin." Kurfi ta gya a kai ta kauda fuska. Tambayar da ya yi ke cin ranta, tana ji sadda ya kunna ira'ar Sudais cikin Suratul Ba arah. Ta yi shiru ta na tunani, shima bai ara magana ba sakamakon tunanin Hajiyarsa da damuwa da kalar rayuwar da ta za a wa kanta. Abu aya ke sanyayar da jikin Kurfi akan Khalid. Ta tuna fa tun ma kafin zuwan ranar hakan ba ya sonta, bai auketa a komai in ba. Da ace ya auka to fa ba zai biyewa al awari ko fa in mahaifiyarsa ba tunda ba fa a ce inda ba daidai ba don sa a umarnin Ubangiji. Zuciyarta ta ara gaskata cewar eh haka in ne ba makawa Khalid shi kansa ba son ta ya ke ba. Za kuma ta ja jikinta, za ta kama mutunci da imarta ta mace har zuwa sadda za ta san matsayinta. *** Tana tsaye jikin tagar akin tana kallon waje, can kuma ta juyo a fusace ta nemi wuri ta zauna. Hajiya Hadiza iyar anwar mahaifiyarta wacce suka fi kira da Gwaggo kallo ta ke bibiyarta da shi tun som wayarta da Aliyu har ta kammala. "Yanzu mene abin yi?" Cewar Gwaggon tana dubanta cikin kulawa don ko ba komai Saudatu na ba ta girma da kulawar da sauran an marigayiya Hansatu uwarta basu ba ta matsayinsu na an uwanta ko kuwa dai kwa ayi da son abin duniya ya sa ba ta ga nasun ba oho. Hakan kuma saboda hali ne da ya zo aya. Dukkan wasu tuggu da makirci tare suke ulla- ullarsu. Hajiya Saudatu tana maida numfashi da fidda hucin bakin ciki da acin rai. Ta dubi Gwaggo da jajayen idanunta. "Maganar banza Aliyu ke kawomin, ba zan lamunci hakan ba don ba shawara ba ce. Gwaggo ba zan uya ha uri na kyale yarinyar da ta raba ni da gidan mijina ba. Na tsaneta, na tsani zuri'arsu. Ban ga amfanin sanin da na yiwa Bara'atu ba a rayuwa." Gwaggo ta gya a kai. "Ki haukatar da ita, ki tashi tsaye kyan da afarki. Kar ki yiwa kowa ragi, kinga dai wancan tsohon gurgun uban naki ba kyaleki zai yi ki zauna gidansa ba, kalar cin mutuncin da zai dunga shimfi a miki ma ya isheki. Su Zuwaire ma kinsan ba