← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 41

Sashe 19

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anti Rumaisa yana bacci hankalinsa kwance. Ya sha kayan sanyi milk, da showel. Sai ka rantse ita ince (Kurfi) tana arama tsabar kammaninsu. Ta shagala wurin kallonsa ta ji an mi omata shi. A hankali ta aga kai ta dubeta, Anti Rumaisa ce, itama duk idanu a kumbure. i ki ri eshi Laila, ba shi da laifi ko ka an. Rai da mutuwa duk MU ADDARI ne daga Allah, idan sa'i ya yi, dole a tafi." Sai ta ji kwalla sun kara cikamata idanu, tana yiwa yaron kallo na silar da ta yi rashin Maminta. Ta tsaya dai tana kallonsa tana hawaye sai dai bata ko yi yun urin ta aukeshi ba. Ganin ana matsamata dai ta auka kawai ta hau girgiza kai ta mi e kamar wacce aka tsikara tana kuka, jikinta har rawa yake ta fice a guje zuwa angaren Mami. Dun ulewa tayi saman gadon tana kuka sosai, akin ta ke kallo tana ara aremasa kallo. Shikenan wannan sabuwar duniyar da ta shiga babu Mami a ciki, babu ita. Ashe haka wa anda suka rasa mahaifiyarsu suke ji? Ciwo da ba zai ta a warkewa ba. (Ina jajantawa duk wata iya ko a da sukai rashin mahaifiya, Allah Ya jaddada rahma a agaresu. Ameen) Babu abinda ta ke so, ba abinda ke burgeta, babu kuma abinda ke mata da i yanzun. Ba ta ji sallamar mahaifinnata ba, sai ganinsa ta yi ya shigo. Ya araso ya zauna a gefenta. "Laila." Jin ya ambaci sunanta ya sanya ta mi ewa da sauri ta ru umeshi tana sheshshe "Abbana ba Mami, ya zan yi? Da wa zan dunga shawara? Na rasa uwa, na rasa awa, na rasa abokiyar shawara. Mamina ta hanani awance, bansan kowa ba sai ita, ita ka ai ta zamemin komai. Abbana ya zan yi Mami ta bar duniya ta barni da kewa." Ta arashe gami da sakin kuma sosai tana ambaton innalilahi. Duk wani mai imani ya ga yanda Kurfi ta chanja ta ko e sai ta ba shi tausayi. Abba a yanzu dai kuka ya are sai na zuci, ya dakewa zuciyarsa kwarai. Ta ya ya ma zai yi kuka alhalin yana da iyalin da zai rarrasa ya basu ha uri kuma? "Laila, ke kika halacci Maminki?" Ta girgiza kai tana goge fuska da ankwalinta. "Good, ba ke kika halicceta ba, Allah Mai kowa da komai Shi ya halicceta, Ya kuma bamu aronta. Meyasa zamu zama masu son kai alokacin da Ya kar eta mu kasa tawakkali mu yarda taSa ce dama, kuma ya kar i ranta a lokacin da Ya so? Kar ki manta fa arSa ce a Al ur'ani Mai Tsarki cewa, dukkan mai rai mamaci ne. Inda Maminki ta tafi mu inma wataran duk can zamu tattara mu tafi aya bayan aya. To akan me zamu kasa ha uri da irin jarabtar da Ya ora mana?" Abba bai gushe ba yana mata nasiha har sai da zuciyarta ta russuna, ta nemi kukan ta rasa sai zubar hawaye ka an-ka an. Ta ara fahimtar jahilcin da ta tafka na orawa jaririn da bai ji ba bai gani ba laifin da bai zamto laifi ba ga duk mai ilimi da tunani. Tun daga ranar ta sanyawa zuciyarta dangana, ta kuma ha ura da ci gaba da yiwa Maminta kyakkyawar addu'a. Ta rungumi jaririn Maminta da hannu bibbiyu, ya zamana shi ne madadin Mami a idanunta, kullum yana hannunta, ita ke rainonsa. Wanka ne kawai da shiri bata yi mishi. Har dai aka kwana bakwai, aka ra amasa suna Mu'azzam kamar yanda Mami ta ci buri. Ba sunan kowa bane a zuri'arsu, kawai sunan ke burge Mamin tun ba yanzu ba. Bayan bakwai Kurfi, Zeenat suka tattara suka koma angaren Hajja tare da mai rainon Mu'azzam don kuwa sam Abba ya i yarda da ba Anti Rumaisa ko wani Mu'azzam. A cewarsa ba ya aunar su yi nesa da shi. *** Islamiyya kawai ke raba Kurfi da Mu'azzam, amman da zarar ta dawo to fa komai nata yana a wurinsa. Babu mai ganin dariyarta sosai idan ba Mu'azzam ba duk kuwa da kasancewarsa jariri, idan kana magana da Kurfi to fa sai dai ta murmusa maka ka an. Wataran kuwa takan auki Mu'azzam su je can cikin garden ta sha kukanta na rashin uwa ta share hawaye san nan ta aukeshi su koma ciki. Yau inma hakan ce ta faru, su na tare da Mu'azzam a garden, ta shige can wajen wata aramar orama ta ruwa, (Waterfall). Kuka take sosai tana ara ru ume Mu'azzam da ke lullu e sosai cikin shawul. Ba ta ji motsin mutum ba, sai handkerchief fari sol ta ga an mi o mata. Ta dubi handkerchief in kafin ta kai duba gefenta. Farar riga sai ta sama ba a da wando ya sanya, sai kuwa ba in gilas wanda ya rufe wayar idanunsa. Ya fito a Engineer KK insa sak. Kallonsa ta ci gaba da yi na an sakanni kafin ta kauda kanta. Ba zata so share hawayenta ba sai dai ganin bai gaji da mi omata farin yallen ba kamar yanda bai ce uffan ba ya santa ta kar a gami da magana ciki-ciki. "Thanks." Ta kuwa yi amfani da shi wajen goge fuska. Hannu ya mi amata. "Mi omin shi." Ba musu ta karkata ta mi amasa Mu'azzam. Ya kar a yana murmushi, can kuma ya dubeta. "Kinsan me? Da ace kuka yana dawo da mamaci, da tuni da yawa sun dawo. Sai dai babu ta yanda za'ayi wanda ya mutu ya dawo. Mami ba za ta ta a farin cikin zubar hawayenmu ba, za ta fi gane cewar mu in masoyanta ne idan muka zama masu dagewa da ro omata gafara da rahmar Allah. Mutuwa da ciwo, tana da zafi, sai dai kuma Allah Ya sanyawa an adam ha uri da dangana. Saboda Ya riga da yay al awarin dukkan wani rai zai aneta." Ya an yi shiru, ita dai kallonsa ta ke yi cike da mamakin yanda ya ke maganar da ta haura sakanni goma saboda a nutse ya ke fitarwa hakazalika ba da gaggawa ba sai dai sosai maganganunsa sun shigeta. "Ki yi ha uri, ki ara akan wanda ki ke yi. Mami ba ke ka ai kika yi rashinta ba, mu ma mun yi." Ya arashe hankalinsa na ga Mu'azzam. Itama ta kai duba gareshi ta ji wani hawayen sun ara tahomata, ta aukesu a hankali. "Tashi ki koma ciki, Hajja na can kin bar ta da tunani." Jin abinda ya ce yasa ta gane cewar Hajjar ce ta turoshi. Ta mi e ba musu suka jera har sashen Hajja. Karaf kuwa akan idanun Aliyu, shi kam ya riga da ya tsaneta, mutuwar Maminta bai chanja daga tsanar da ya yi mata ba. Koda suka ha a idanu, fakar idanun Yayansa ya yi ya narkamata uban harara. Ta kauda kai, ko karta bai yi ga zuciyarta ba don kuwa yanzu ba ta ga abinda zai ta a zuciyarta ba har ya dameta irin mutuwar Mami. *** BAYAN WATANNI SHIDA Komai ya sauya, cikin hukuncin Ubangiji, Kurfi sosai ta rage damuwa, takan shiga cikin sa'anninta ayi wasa da dariya. Hakanan takan zauna su sha hira da Hajja, sai ya zamana a sannan ta du ufa da duk wani abu da ta san cewar Maminta na so ta yi a sadda ta ke raye, kamar aikace-aikace musamman girki da ba wani iyawa ta yi ba. Koyaushe idan har tana gidan to da ita ake shiga kicin wasa-wasa kuwa sai ga Kurfin ta sauya zuwa wata mai haza a a fannin girki musamman na gargajiya domin kuwa ar aikin Hajja kusan abincin gargajiya ta iya ba na zamani ba. A wajen Zeenat ta iya na zamani daidai gwargwado. A lokacin kuma aka tara Meeting na family inda aka tsaida zancen auren Zeenat da Zahraddeen sai kuwa Ru ayya da ta gaji da jiran Yaya Khalid ta fidda wani an kasuwa mai suna Jamil, acikin manemanta. Kurfi dai ta nuna tana son ta soma karatu kafin ta samu tsayayyen miji, ta ro i wannan alfarmar su ka bi ta da hakan, ita kuwa Hafsa jin har da Yaya Khalid wa anda zasu yi auren kuma ba'a fa i matarsa ba yasa ta ke zargin lallai ita in ce za'a aura masa. Wannan duk tsarin Baba Mudassir ne da su Baba Hamza. Bayan kowa ya watse a akin Hajja ta fito ta zauna ta hau gugan kayan Mu'azzam. Hajja na kallonta ta soma magana. "Ke kam kin shiga uku, yanzu kin dai dage sai kinga arshen biro da takarda. To ai sai mu gani idan tusar za ta hura wuta." Dariya tayi, ba tare da ta juyo ba ta bata amsa. "Me zai hana to? In sha Allahu kina nan zauna za'a kawoki har ofishina na zan a maki allura." "Allah Yay min tsari, yo ko ba likitoci a duniya zan yarda a kawo ni inda ki ke ne? Ai ke bai fi ki arasani ba ko don ki hana ni aure mijin. To kuwa ta Allah ba taki ba, ehe." Dariya sosai Kurfi ta yi. "Amma fa ki shirya shekaru ari a duniya, inaga lokacin ne zan yi aure." "Au, haka kuma kike nufi?" Dariya Kurfi ta yi. "Wasa nake maki toh." Itama Hajja dariyar ta yi. "Ja'ira, a yi dai mu gani Daga nan ba ta ora komai akai ba. Shiri sosai na aure suka soma don alokacin bai fi wata aya ya rage a soma biki ba. Su ne kasuwa, su ne shagon inki da sauransu. A wannan lokacin ba irin bugar ciki da tambayar duniya da Hajiya ba ta yi ga Hajja da Daddy ba don kawai ta ji wacce za'a aurawa anta amman ba amsa. Hakanan a gefen Hafsat hankalinta tashe ya ke don kuwa ita a ganinta kawai auren dole ne za'ayi mata, ga babanta ba wanda za ta kaiwa maganar banza ba ne ya saurara. Tsoronsa ma su ke yi saboda Baba Mudassir ya fi kowannensu zafi. Mama Zahida itama babu wani labari daga wurinta, wannan y a tayar da hankalinsu har suka bazama neman sani daga bokaye don a atan basira irin nasu, ba abinda ba zasu iya binciko musu ba. A bangaren Yaya Khalid shi kansa ba shi da
Chapter 19 · 0% Book details