← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 41

Sashe 3

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jimin wani son kai, au don 'yar gidanku ce? Ke ba ki ji me ta cemin ba? Wai har ni za'a kalla a kirani banza? Lallai, wallahi bata isa ba." Daga haka ta kara sauri ta barsu anan ta nufi sashen kakarta. Sallama ta rangada kafin ta shiga. "Ina tsohuwar nan ta shige wai?" Hajja da ke zaune saman three-sitter tana taunan goro ta dubeta. "Ja'ira, sai yanzu kika ga damar zuwa?" Kurfi na dariya ta cire hijabinta tayi wurgi gefe da shi san nan ta kwanta a saman cinyarta. "Kai ke kam ba kya yiwa mutum uzuri ne? Yau wancan Maigidannaki ne ya sanyani a gaba, shi kullum idan yana gida ba shi da aikin da ya wuce ya bak'antamin rai." Kyakkyawan mintsili ta bata a gadon baya wanda ya sanyata gantsarewa gami da saurin d'agata. "Kai don Allah ? Za ki k'aramin zafi akan zafi." "An k'ara din, kul, kada na kara jin kin ta6amin Maigida, ke yanzu ba don shi ba, ai da ba'a san irin k'iriniyar da zaku yi ba, su iyayennaku sun sakarmaku komai ma yi ku ke yi, su wai rik'akkun yan boko ko? Toh ba zan lamunta ba, Allah Ya karawa Maigida lafiya ya kara sanyamaku ido." Kurfi ta ta6e baki. "Ni so nake ma a turashi can wata jahar wallahi, ya yi nesa da mu ko ma samu mu..." Sallamarsa ya sa ta kasa karasawa, cikinta ya duru ruwa, da gudu ta runtuma dakin ta sanya muk'ulli. Ya bi bayanta da kallo kawai, tsaf ya ji abinda ta fada. Karasawa ya yi ga ya zauna gefenta. Dariya kawai ke yi tana karawa. "Kai Laila, Allah Ya shiryamana ke." Abinda ta fadi kenan, shi kam bai tanka ba, gaisheta ya shiga yi. Ta amsa tana kallonsa. "Maigida ran gida na ." Murmushi ya yi mai 'kara fiddo kyawunsa musamman da gefen kumatunsa ya lotsa. Ya cire bakar hular da ke kansa ya shafi sumar da akai wa kyakkyawan aski. "Wadannan jikokinnaki zan 6allasu wataran." ta kara darawa. "Atoh, su zasu ja ka 6allasun, ni ba ruwana. Dole dai matarka na cikinsu idan ma ka tara duka ka 6alla, haka za ka kwashi daya." Ya murtuke fuska kamar ba yanzun ya gama murmushi ba. "Za ki soma ko? Abar wannan maganar, sallama na zo muyi, zan wuce Abuja gobe da sassafe in sha Allahu muna da meeting." ta girgiza kai. "Yaushe ka ke da lokaci, ina son muyi magana." Yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, son ganin da Abba ke mishi nan ma kan batun aure ne. Yasan kuma Daddy ne yasa a yi mishi, yanzun ma maganar za'a kara. Mikewa tsaye ya yi. "Ki bari during weekend ina jin akwai damarta." Ta amsa da toh kafin ta mishi adduar fatan alheri san nan ya maida hularsa yasa kai ya fita. Ta bishi da kallon tausayi, tasan abinda yasa yake gujewa duk wata magana da zasu yi, fatan alheri ta yiwa Marigayiya Sumayya da nemamata rahmar Allah. Yana tafiya itama Kurfi ta fito ta kara gaba bata ko saurari maganar ba, babu abinda ya sanyata fargaba sai jin da tayi na maganar aura masa daya acikinsu, adduarta bai wuce ya kasance Zeenat ba, ita a duniya bata kaunar auren mai kyau, ba zata iya da kwandon yanmatansa ba. *** ALHAJI KHALID KHALIL KURFI Hamsha an kasuwa ne wanda ya yi yawo asashe da dama a duniya domin neman ku Mazaunin garin Kano ne sai dai asalinsa Kurfi dake a jahar Katsina. Matarsa daya a duniya, Maryam Gidado. Ita 'yar asalin kasar Nijar ce, kanwa a wajen aminin Alhaji Khalid, Marigayi Alhaji Nura Mamman. Ta haifamasa yara tara cif a duniya. Maijidda itace diyarsu ta farko, tana auren wani tsohon dan siyasa a Kaduna, sai Hamza, Mudassir, Abdulhamidu Balarabe, Fatima, Badi'atu, Salamatu da autarsu Basira. Idan ka cire matan, kaf mazan suna zaune a Babban gida da iyalinsu. Bayan rasuwar mahaifinsu akai rabon gado, a arshe bisa shawarar mahaifinsu su kai ha in gwuiwa tsakaninsu mazan suka soma safarar kayan kitchen da na tufafi daga waje su na shigowa da shi. A hankali abin nasu ya yi arfi har ta kai sun kai matsayin bu e kamfani mai zaman kansa. Su na da shaguna manya a kasuwa wanda Baba Mudassir ke kula da wannan angare sai gidan gona da ke ashin Baba Hamza yayinda Abba ke kula da harkokin kamfanin domin kuwa duk cikinsu ya fi su kaifin basira da ilimin boko mai zurfi. To daidai gwargwado dai zuri'arsu su na da rufin asiri da kyakkyawar tarbiyya wanda ya sanya ku insu bai rufe idanunsu ba hakanan basu ata iyalinsu da kashe-kashen ku i ba. Komai su na yinsa ne bisa a'ida. SASHIN BABA HAMZA Matansa biyu, Hajiya Saudatu da Hajiya Raliya. Akwai wacce ya so matuka kafin Hajiya Saudatu sai dai bai sameta ba, karshe ya auri aminiyarta Hajiya Saudatun duk domin huce haushin rashi. Matansa kowaccanta na da yara. Saudatu kaf yaranta maza ne, Khalid Kurfi shi ne babban dansu wanda ya kasance Electrical Engineer, yayi aure sai dai basu fi shekara tare ba Allah Ya dauki ran matarsa Sumayya, Hassan da Hussain sune masu binsa (su ake shirin aurarwa a kwanakinnan, Yaya Hassan zai auri Rahma diya ga Gwaggo Fatima, yayinda Yaya Hussain zai auri Aisha diyar Adda Salamatu), Aliyu ke bi wa tagwaye sai Faruk da autanta wanda yanzu yake aji na hu u a sakandire, Jawad. Hajiya Raliya ita kuwa yaranta hudu, Rashida itace babbar diyarta san nan Batul, Munira da Abdullah. Zama suke kadahan-kadahan domin Baba Hamza bai yi sa'ar uwargida ba, tana da zafin kishi hakanan mace ce mai son yaranta kamar ta hadiyesu. Duk wani abu da zai takurasu bata kaunarsa. Hajiya Raliya kuwa mace ce mai kauda kai da hakuri, tana binta sau da kafa hakan yasa sai a jima ba'a yi rikici ba a gidan. SASHIN BABA MUDASSIR Matarsa daya, Hajiya Zahida. Ta haifamasa yara biyar a duniya. Abdullatif shi ne babban dansu, sai Hafsat, Rukayya, Kamal da autanta Usman. Hajiya Zahida aminiya ce ga Hajiya Saudatu, kusan halinsu guda na kishi. Wannan yasa tasu ta zo daya. Suka dora burin duniya akan yaransu, fatan Hajiya Zahida bai wuce ta ga daya a cikin yaranta ta auri Khalid Kurfi ba. Abinda ta lura kuwa, shi babu daya a gabansa. Ita ta lasawa surukarsu zumar yin auren zumunta a zuri'ar gami da kafamata hujja kan irin artabun da aka sha akan auren Khalid na farko, ta nunamata hakan ba karamin zumunci zai k'ara tsakankani ba. Kasancewar Hajiya Zahida mace mai shegen kissa da wayo, hakan yasa itama ke kaunarta kwarai don ba za ka ta6a zama da ita ka hango aibunta ba. Ta fi Hajiya Saudatu wayo da dabara nesa ba kusa ba. SASHIN BABA ABDULHAMID BALARABE Matarsa daya Hajiya Sadiya. Wacce take k'anwa ga Bara'atu tsohuwar zumar Baba Hamza. A sanadin rakiyar da Baba Abdulhamidu kan yiwa Baba Hamza ga Bara'atu ne suka soma soyayya har ta kaisu ga aure. Mami ta san Hajiya Saudatu sosai kasancewarta aminiya bata wasa ba ga Bara'atu kafin su rabu. Diyarsu daya a duniya, ita dinma sai da suka shafe shekaru biyu da aure kafin su haifeta. Gori kuwa Hajiya Sadiya ta sha shi a wajen facalolinta biyu, Hajiya Saudatu da Hajiya Zahida. Tunda ta zo gidan take fuskantar matsala daga su biyunnan, har sukan ce asiri ne tayi ta auri jinin Alhaji Khalid don basu da arzikin aure a zuri'ar, tun abin na sosa ranta, har ta soma sabawa. Duk da cewar ita Zahida cikin wasa da dariya ta ke nata habaicin ba irin na Saudatu ba. Saukin Mami guda, bata samu matsi daga mijinta ko surukarta ba. Cikin ikon Allah aka wayi gari ta samu ciki ta haifo diyarta mai kama da kakanta sak. Wato Laila Kurfi. na daga yarinyar ta rungumeta tana dariya, ita ta lak'abamata Kurfi. Bangaren Baba Hamza, bata da wata matsala sai ma dora kaunar duniya da ya yi akan diyarsu da suka haifa, wato Laila. Duk irin kumburi da nuna bacin rai na Hajiya Saudatu bai fasa ba. Wannan ya janyo Aliyu tsanar Laila ganin yanda ta saba da mahaifinsu irin sabon da su bai yi da su ba kasancewarsa mutum marar daukar waigi da tsare gida akan d'an kowa idan an dauke Laila sai kuma Khalid hasken zuciyarsa. Haka sunan ya bita kuwa har a makaranta. Daga ita sai Khalid ake ambata da hakan duk fadin gidan. Shi a wajen abokansa na makaranta da aiki, wasu su kirashi da Khalid Kurfi, wasu su ce Khalid KK. Itama a makaranta aka fi ambatonta da Kurfin sai kuma cikin sa'anninta na gida. Ganin cewar ita daya ce ya sanya Adda Maijidda daukar Zeenat autarta ta kyautar ga Abba. Acewarta ya hada ya rikesu da Laila. Mami har kukan dadi tayi. Haka suka taso kamar kawaye. Yayyun Zeenat din har uku a hannun aka yayesu, nan suka zauna har zuwa sadda aka aurar da su cikin garin Kano. Anti Nafisa, Anti Fahima da Anti Zaituna. Aliyu, Hafsat da Rashida sa'annin juna ne, sune masu shirin yin Candy a shekarar. Yayinda Faruk, Batul, Rukayya, Laila Kurfi da Zeenat suma suke sa'anni. Munira ba sa'arsu bace sai dai ta kasance mai girman jiki, hakanan tana da sanyi da hakuri da fadin gaskiya. Wannan yasa kaf cikinsu ta fi jin dadin zama da Yaya Khalid. *** Ranar wata juma'a da yammaci, matasan gidan kasancewar duk suna gida, sun taru a garden, kowannensu harkarsa yake yi. Kurfi ta duk'ufa wajen shan kankanan da ta yankawa Yayansu Hussain, ta tankwashe kafa tana kallo a Laptop dinsa. Kunnuwanta rufe ruf da headphone. Riga da wando ne a jikinta wadanda basu kama jikinta ba, rigar iyakar gwuiwa yellow in colour, bak'in zanen fuskar mace ne a jikin rigar wacce gashinta ya barbazu. Ta shagala kallo har batasan sadda rufin da ta yiwa gashinta da bakin dankwalin abaya ba ya zame ya fadi, dan guntun jelarta ta bayyana a karashen kitson shuku. Shi kuwa Hussain yana kishingide jikin kilishi yana waya da Aisharsa. Hafsat da su Aliyu, game din Scramble suke yi. Sauran sun zagayesu suna kallo ana ihu da dariya. A gefe daya Yaya Hassan ne da Zeenat suke hira, daman ita bata da abokin shawara da gayawa damuwa face
Chapter 3 · 0% Book details