← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 41

Sashe 17

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi musu, duka ne kawai basu sha a hannunta ba, to dai itama Tasleem in ta ce muddin mahaifinta ya shigo to fa a kunnensa. Da wannan Kurfi ta bi direbansu suka wuce, rana ta farko kenan da Abba ya kai hannu jikinta bayan Khalid ya fa amasa, fa ar ma ba da niyya ba, Khalid in ya rutsata a farfajiyar gidan ne Abban ya zo wucewa ya shiga tambaya. Anan ne har Abban ya mareta. Sosai ya bu emata wuta, kallo kawai ta bi Khalid da shi cike da acin rai kafin ta ja akwatinta ta ara gaba. Dakyar ta samu iyayen suka bar fushi da ita, a arshe suka yi mata nasiha mai ratsa jiki gami da nusar da ita gangancin da ke cikin bin saurayi a fita yawo, wannan ya sanyayamata jiki musamman da Mami ta bata labarin wata ar makwaftansu da aka lalatawa rayuwa sanadin hakan, nan ta gano cewa ba wayewa bace bin samari a fita yawo, ba kuma hanya ce mai ilewa ba. Daga nan ta aukarwa iyayenta al awarin ba za ta ara ba. Shi kuwa Khalid ta kwan biyu ana fushi da shi kafin ta manta komai ta watsar. Sai bayan sallah da sati biyu san nan Zeenat ta dawo daga Kaduna suka ci gaba da zuwa Islamiyya da kuma zaman jiran result. Alhamdulillah dai sun samu Jamb insu ta yi kyau yanda ya kamata. *** A kwana a tashi, cikin Mami na ara girma, yayinda sha uwa ke ara shiga tsakaninta da iyarta, kusan ma fiye da baya tunda yanzun islamiyya kawai suke zuwa banda boko. Dr Arfat ta ba Mami shawarar yawan motsa jiki hakan yasa duk bayan sallar isha'i su ke an trekking ita da an rakiyarta, wato Zee at da Kurfi, wataran har su Munira sukan bi su idan sun so yawo. Yau dai a an tafiyar daga Mami sai Kurfi, Zeenat na fama da mura hakan yasa Mami ta hanata fita ta ce ta zauna gida ta huta. Sun fito farfajiyar gidan sukai kici us da shi yana tsaye jikin mota sanye da tshirt maroon da wanda dark. Waya yake, don haka Kurfi ta soma ro on Allah a asan ranta don su samu su wuce ba tare da ya tanka musu ba. Addu'arta bata ci ba don kuwa katse kiran ya yi ya nufo inda suke. Bayan ya gaisa da Mami, itama Kurfi ta gaisheshi. Bai ko amsa ba ya e tambayar Mami ina zuwa? Da murmushi ta amsa. "Nan zamu an zagaya na motsa jiki." Ya dubeta, duk ta bi ta rame sai tulun ciki, kawai sai ta ba shi tausayi. "Muje na muku rakiya." "Ai da ka barshi, kada mu katse maka hanzari, ba nisa ma zamu yi ba saboda garin akwai hadari." Murmushi ya yi. "Ba komai, muje kawai." Daga nan suka jera suka fita daga gidan. Kurfi ji take kamar ta juya ta koma, akan me zai bi su? Tasan kawai don ya katsemusu hira ne ya kuma katse nisha inta, don ko ba komai gari ana iska mai da i banda alamun hadari da ya soma bayyana don kuwa ana ta wal iya. Suna ta hira da Mami ita dai nata kunne har suka iso kusa da wani shago. Dama ta ullo an chanjinta don akwai wani biskit da suke siya mai shegen da i. Ta dubi Mami. "Mamina zan siyo abu yanzu zan biyoku." Suka dubeta. "Yi sauri to." Cewar Mami. Ai kuwa da saurinta ta nufi shagon. Mami dake bin ta da ido tayi murmushi. "Khalid." "Naam." "Wata ar alfarma nake son ka yimin." Jin haka ya sanyashi nutsuwa, suna tafe yana dubanta. "Kamar ta me Mami?" "Amanar Laila." Sai da ya ji fa uwar gaba, ya an girgiza kai na rashin fahimta. "Banganeba Mami." Ta ji idanunta sun cika da walla. "Bansani ba, ban san me addara ta oye a lamarina ba, ban kuma san inda zan tsaya ba. Kawai dai ina ji a jikina mafarkin da nake mai yiwuwa shi zai tabbata. Ro ona aya shi ne, ka rikemin amanar Laila, bansan me zai faru da rayuwarta a bayana ba, nidai nasan komai MU ADDARI ne daga Allah. Ka auketa tamkar ciki aya ku ka fito Khalid, ba ni da a namiji, amman kai ina maka kallon ana. Ina kyautata zato a kanka. Na tabbatar koda duniya zasu Laila, kai ba za ka juyamata baya ba. Ka ri emin ita irin ri on da za ka yiwa anwarka Munira da kuma aninka Aliyu. Kana okari wajen tsawatar mata akan duk abinda ka ga ta yi ba daidai ba, nasan ko babu raina ba za ka fasa abinds ka saba yi ba." Idanunsa suka ka a, ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi, mutuwar Sumayya ce ta fa o a ransa, ya ji tamkar maganganun Mami sallama ce ta bankwana ta ke yi gareshi itama. "Mami noo, please ki bar irin wannan maganar, wallahi ji nake kamar kina bankwana da duniyar ne. Ina jin kamar zamu kwanta mu farka babu ke a duniyar. Mami Laila anwata ce, ina aunarta domin Allah kuma na yi al awari gareki ba zan ta a bari wani ya cutar da ita ba." Mami ta share hawayenta sai ta sanya murmushi mai ha e da ar dariyar farin ciki. Hannunsa ta riko. "Na gode sosai ana, Allah Ya yi maka albarka. Kar ka damu, dole ne ga kowane * AN ADAM* ya dunga tunawa da mutuwa. Ta ya zan mutu ban ga aurenka ba, ban kuma ga na Lailata ba? In sha Allah burina zai cika a kan idanuna." Kunyar maganarta ya sanyashi sunkuyar da kai yana murmushi. "Oh ni, Allah Ya shiryamin Laila." in haka ya sanyashi aga kai yana kallon inda Kurfi take. Tana tafe tana irga chanjinta ga ledarta ba a cike da biskit. Ko kallon gabanta ba ta yi sosai. Sai ta ba shi dariya ya murmusa har zuciyarsa. Sai da Mami ta kira sunanta san nan ta ago kanta, ita sam ta mance tare suke da mugun, sai da ta gan shi ta tuna. Ba shiri ta maida chanjin cikin leda ta hau takowa da an saurinta yayinda iska ke okarin yayemata gyalenta. Ai kuwa ba ta yi aune ba gyalen ya yi gefe ga kan babu ko ankwali. Takaici ya kama Yaya Khalid, gefe ga wasu dandazon samari sai karemata kallo suke, ganin aya a cikinsu na shirin tashi ya mi amata gyalen, ya sanyashi saurin zuwa ya kama gyalen. Mi a mata ya yi a fusace. Ta kar a jiki na rawa ta rufe kan. "Ban hanaki yawo ba ankwali ba?" Ya fa asa- asa. Ta dubi wayar idanunsa, ganinsu a rine ya sanyata auke nata da sauri ta rufe kan. Suka jera har inda Mami ke tsaye tana kallonsu, ta kalli wancan da ta kalli wannan haka ta dun ga yi har suka araso. Murmushi tayi. anwartaka ba ta jin magana sai addu'a ai." Sai san nan ya murmusa bai ce uffan ba, a haka har suka isa gida. Hira sai dai tsakanin Mami da Yaya Khalid. Kafin su arasa kuwa an soma yayyafi, Allah Ya taimakesu sai da suka shiga har angarensu san nan aka tsuge. *** Mami na shiga watan haihuwarta ta bar zuwa kowane sabga ta dangi ta bar wa su Hajiya, koyaushe tana gida. Ranar alhamis Mami na saman darduma tana sallah a falo, tare da Kurfi. Kurfin na zaune ta tankwashe afafuwa ri e da wayarta tana kallon wani indian series a youtube da ya wuceta bata samu gani ba a tashar Starlife, a gefenta wani ha en cincin ne da Anti Bara'atu ta aikowa Mamin, tana yi tana ci. Mami har ta gaji da orafin kallon da ta sabarwa kanta da shi tun bayan kammala jarabawarsu. "Tashi Laila ki rakani sashen Hajja." Ba musu kuwa ta mi e ta tsaida kallon. "To Mamina, bari na maida wayarnan kada wancan an gaban goshinnaki ya gani ya wace." Mami ta murmusa maimakon fa an da ta saba yi idan ta kushe Yaya Khalid. "Sai na fa amasa kuwa." Ta zura aramin hijab inta iyaka kafa a a saman doguwar rigar atamfa da ke jikinta, ta arasa ga Mamin tana fa in ta yi ha uri ta bari. "An i ha urin." Ta marairaice gami da kai kunne ga saitin cikin Mami. "Lil, kana jin Maminmu ko? Ka ce ta yi ha uri." Mamin ta tureta tana dariya itama ta shiga tayata. Suka jera Mami na ri e da hannunta su na tafe su na hira tamkar basu son tafiyar. "Laila ta majnun, yanzu ke ba kya fatan ki yi aure sai karatun dai?" Kurfi ta narkar da fuska. "Eh mana Mamina, kinga ai ba wanda ma nake kulawa yanzu, ni ko wancan Kamal in na rage amsar wayarsa, shima abinda yasa muke tare sabods ya cemin zai barni na arasa karatu. Kuma shi yanzu ba gaggawa ba ya ke." Mami ta an ta e baki tana murmushi. "Kuma da yake an ce miki lallai shi ne mijinnaki ko?" Jin haka ta an dubi Mamin sai kuma kunyarta a karon farko ta kamata, dole ta sunkuyar da kai. Murmushi Mamin ta ci gaba da yi kafin ta dungure kanta. "Ja'ira, wata yau kuma ni kike kunya?" Dariya kawai ta yi. Ya yi daidai da tahowar Aliyu, fuska a aure ya araso kamar zai bangaje Mami ya wuce. Cike da acin rai urfi ta ja tsaki. "Banza kawai marar hankali." Mami ta girgizamata kai. "Ban hanaki ba? Karki ara! Aliyu jininki ne babu yanda za ki yi." "Wai Mami meyasa ke komai ki ce ha uri, ha uri, cin kashin da suke ya yi yawa. Daga ke har Abba bansan wani kalar zuciya ba gareku da ba kwa tuna sharri sai alheri." Tana maganar a fusace, Mami ta juya suka sauya hanya zuwa garden ganin Kurfi har ta soma hawayen ba in ciki. Allah Ya taimaka ba kowa, don haka suka zauna saman aya daga kujerun wajen masu zaman mutum bibbiyu har zuwa uku ma. Shiru sukai ita tana hawayen yayin da ita kuwa uwar ta yi shiru kawai tana kallonta tana sa a abubuwa da dama a asan ranta. Can kua sai ta juyar da kanta ta goge kwallar da ta cikamata
Chapter 17 · 0% Book details