← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 41

Sashe 41

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

hararar inda Kurfi ke zaune tana karanta wani lovestory book da ta auka a studyroom in Khalid kafin ta ce "Daga asibiti nake." "Too, ba ki da lafiya?" "Eh, sun ce wai juna biyu ne." Ta fa i ciki-ciki tana yamutse fuska. Hajja ta shiga hamdala da murna. "Allah Ya inganta, Ya raba lafiya." Kurfi ta fa i da zuciya aya yayinda farin cikinta ya gaza uya ko a fuska. Rukayya ta watsa mata wani kallo kafin ta auke kai tana wani murmushi ta dubi Hajja. "Hajja nikam ban son wannan jikar taki tana shiga sabgata. Wato dai shi mutum idan ya rasa uwa a gida sai ya yi fatan kowa ma ya rasa. To dai ta Allah ba ta mutum ba." Maganar ta soke ta sosai, Hajja da ba ta gama farfa owa ba daga mamakin kalamin ya sa Kurfi samun damar maida martani. "Na gode Allah da Ya ha ani da uwa ta gari. Kinsan wannan ya fi komai abin alfahari. Har uwata ta rasu ba'a ta a jin kansu da mijinta ba balle abin ya kai ga saki adalilin bin bokaye." "Kan uban can! Ni kike zagar wa uwa?! Wallahi yau sai kin san ta haifa." Daga haka Rukayya ta nufeta gadan-gadan. "Ke! Ke!! Bana son hauka." Hajja ke furucin kafin ta hau kwala wa Balaraba kira. Kurfi kuwa tamau ta ri e hannuwanta ita kuwa bori ta ke tana yun urin kai mata duka tana zage-zage. Tsawar da Daddy ya daka ita ta yi sanadin da gaba aya suka nutsu. Rukayya ta ara fashewa da kuka tana fa in sai ta daki Kurfi tunda har ta iya ta zagi uwarta. Daddy ya dubi Kurfi. "Laila ya haka wai?" "Kaga Hamza, kyale wannan shashashar yarinyar. Don tsabagen rashin kunya a gabana ta bu i baki tana zagin Marigayiya Sadiya ba ta ji ba ta gani. Amsar da Laila ta bata shi ya fi cancanta gareta. Ba don juna biyun da ke tattare da ita ba yau sai na sa kun koyamata hankali!" Daddy ya gama sauraron Hajja kafin ya dubi Rukayya fuska a aure. "Ke ashe ba ki da hankali? Kar na ara jin wannan anyen aikin daga wurinki idan kuwa ba haka ba wallahi matakin da zan auka kanki sai kin gane kurenki. Ku yara ba ku san kaddara ba, duk yadda ta zo ba ku san ku ri e da hannu bibbiyu ba? Me ar uwarku ta taba yi maku da ku ka bi ku ka tsaneta? Ko an fa amaki duk ba mu da labarin abinda ku ke mata ke da an uwanki? Ku ji tsoron Allah tun kafin ha inta ya kama ku. Maza ba ta ha uri." Ranta na tu i ta ba Kurfi ha uri. Kurfi ta gya a kai. "Ya wuce." Ta furta da rawar murya. A arshe Daddy ya karasa ga Hajja don dama gaisheta ya shigo yi kafin ya wuce aiki. Ita kuwa Kurfi ta tattara waya da littafinta ta wuce aki. Zama kawai ta yi saman gado tana huci da ambaton Allah a ranta kawai don ta samu zuciyarta ta yi sanyi. Zuwa yanzu zuciyarta ta bar kuka akan ire-iren wannan abu. Fatanta aya bai wucw ganin ta soma karatu ba, wannan ka ai zai auke mata dukkanin kewa da ka aici. *** A rana ta biyu Mama Zahida ta koma wajen Malam Badaru. Kamar wancan zuwan, haka ya juyata son rai, wannan karon maimakon ra i sai ta ji madadinsa. Sai ya zamana daga aikin kwanaki uku an koma sati. Cikar sati ya ba ta wasu layu wanda ya ce da najasarsu ya ha a akan ta je ma abarta ta binne. Misalin arfe sha biyu da rabi na dare, ta faka motarta a can wani loko wanda wurin daji-daji ne kusa da wata ma abarta. A hankali ta fito auke da damin ku i a leda wanda ta ke niyyar ba maigadin ma abarta sai layun da ta ulle a gefen zani sai kuwa mu ullin motar da ta jefa cikin rigar mama. Sa af-sa af ta ke tafiya kamar arauniya, tana arasawa ta ara rage sautin takunta. Allah Ya taimaketa ma Maigadin ba ya kusa, don haka ta shige ma abartar tana mai jin tsananin fa uwar gaba. Yanda ta ji irjinta na bugu sai da ta ji kamar ta juya ta koma, sai dai kuma ita keda riba idan komai ya kammala. Ta karasa tana jin ta wata fayau, tana taka shukokin bishiyar tunfafiya har ba ta sani ba ta taka wata ma abarta. A firgice ta daka tsalle ta yi baya tana fidda numfashi. "Waye?!" Ta ji an fa i da arfan sauti. Ta yi saurin kwanciya a bakin hanya, har mutumin ya gama zagayensa ya koma mazauni. Da wannan damar ta samu ta mi e ta hau ha a rami da sauri-sauri. Ta ciro layun kenan za ta sanya ta ga fitila ta hasketa gaba ayanta. Nan da nan mutumin ya yi ihun da ya tara wasu cikin samarin unguwa da dattawa. Ganin asirinta ya tonu ta tattare zani za ta gudu su ka kuwa yi rubdugu suka cafketa. Wani wawan mari aka samu wani ingarma a cikinsu ya auketa da shi. "Munafuka! Uwar ina za ki je kuma? Yau Allah Ya tona asirinki, dama mun jima muna fakon ki. Kece mai zuwa binne layu ma abarta!" "Na shiga uku, wallahi yau ne far.." Wani marin hagu da dama ya ara mata, arshe suka yanke kai ta Police station. Daga haka aka kwashi layun da ba ar ledar da sauran tarkacenta da ta ke ha a aka fice da ita tana ihun kuka. *** Ranar ta kama Juma'a, an tashi da wani irin zafi. Hakan yasa koda ta yi wanka riga da skirt an kanti ta sanya wa anda suka zauna daram a jikinta. Pink colour din ya dace sosai a fatar jikinta. Ko ankwali ba ta aura ba ta fito zuwa falon ta zauna. Farin handkerchief ta shimfi a a asa kafin ta soma yanke faratan hannun. Tana yi tana sauraron wa ar da ta kunna a wayarta ta Ali Jita mai suna I love you baby. "Yaya oyoyo! Yaya oyoyo!!" Tashin muryar yaran gidan ta ji su na ihun murnar da ba ta gana fahimtar ta me ce ce ba. Can ta tuna da dawowar Abdullatif cikin wannan satin, hakan yasa da murnarta itama ta mi e ta fito. "Kar na ara jin zancen banza! Yau nake so ki aiwatar. Ki tabbatar ta ci abincin. Yau nake son ganinta a mace." Hajiya ke maganar ta waya. Daga aya angaren aka amsa. "Ranki ya da e an gama. Yau zan cikamaki burinki kamar yanda ki kai al awarin aukaka rayuwata." Murmushin nasara Hajiya ta yi kafin ta katse kiran. Ta tsaya duban wayar sannan ta saki dariya. "Sai anjima Laila, yau za ki bi uwarki." Ya juya baya, ya russuna ya na gaida Ummi tana amsawa fuskarnan cike da fara'a. Kurfi ta araso da saurinta. "Yaya Abdullatif san.." Sauran maganar ta ma ale a ma ogwaronta sakamakon wanda sukai ido hu u da shi. Kallonta ya ke da gaske kamar yanda itama take dubansa. Ya sauya gaba ayansa, ya yi wani mugun kyau fatarsa har she i ta ke yi kamar yanda ba in gashinsa ya ara duhu da cika. Kyakkyawar sumarsa ta ara taimakawa wajen fiddo zahirin KHALID HAMZA KURFI. Juyawa ta yi da sauri bayan ta jefamasa wani kallo na tsana ta wuce sashinta. Ummi na magana amman ina! Tana isa ta rufe gam da mu ulli zuciyarta na tu i. Ta na jin takaicin fitar ta, da ace ta san shi ne to fa ko za'a mutu ba za ta fito ba ballantana su ara ha uwa. Ba ta kaunar ta ganshi. *** Ya maida dubansa ga Ummi jiki a sanyaye, Ummin ma shi ta kalla a son ta fahimci yanayinsa

h j l r t v x
j l v
Times New Roman
Times New Roman
Symbol
Symbol
Arial
Arial
Calibri
Calibri
SimSun
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
Bookmark1
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO F3
TECNO LD7
WPS Office
8232f21a020749ef8aafc9427c0babdd
Chapter 41 · 0% Book details