← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 41

Sashe 30

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da hakan. Wannan yasa ta ha ura har sai ta samu ke ewa. Ta maida wayar jaka ta killace ta. Sai a lokacin ta shiga kallon akin. Babu komai ciki sai katifu biyu da shimfi en kafet arami a saman tiles in. Gaba aya ya sha dau a domin kuwa da alamu dai azamai ne mazauna akin ha ka nan abin ya ha u da rashin kula daga ita uwar akin nasu. Hawaye sababbi suka shiga kwararo mata. Ta sani, ba don ganin daraja ta aure ba, za ta iya ficewa daga nan ta koma can wajen Hajja ko kuma ta nufi wurin an uwan Maminta, amman ta za i ta zauna. Ta za i ta yi ha urin ta ga iya gudun ruwan Hajiyar. Har shekaru nawa za'a yi su na fuskantar matsala daga gareta su na kaucewa? Ya ci ace sun tunkareshi, ko ba komai ta na son ganin ta cika al awarin da ta aukarwa Maminta na cewar wataran komai zai wuce da arfin addu'a da kuma ikon Ubangiji. Sai dai kuma aninta da Hajja? Ba za ta zuba ido a salwantar da rayuwarsu ba. Ta mi e ta shiga ban akin bayan fitowar Lauratu wacce ke mata kallon antacciya, wannan abu ya fi komai ona ranta, ar aikin gidansu ce yau ke da damar yi mata kallo haka? Dama ba wani mutunci ta ke da duk wani wanda ke angaren Hajiyar ba, don haka ta san za'a rina. Ban akin ta shiga, sai dai shigar ta, fitowar ta, don kuwa wani zarni ne da arni- arni ya buso ofofin hancinta. Ta daure ta shiga. Omon da ta gani da Hypo ta auka ta zazzaga a ko'ina, sai da ta wan e ban akin yanda amshin ya saitu da yanda za ta iya sha a kuma ta yi amfani da shi, sannan ta samu nutsuwar kama ruwa gami da ora alwala. Fitowarta ba Habiba sai Lauratu da ke sallah. Itama ta fiddo hijab in ta ta shimfi ankwali ta tayar da sallah. Addu'a sosai ta yi bayan idarwa, ta nemi tsari daga shai anu, aljanu da ma mutane jinsinta. Ta ri i addu'a, ta kuma san cewa Allah Mai amsawa ne. Kafin ta idar itama Lauratun ta fice. Wannan ne ya bata damar aukar waya ta lalubo lambar Adda Maijidda, ta kuwa sameta. Bayan sun gaisa ta sanar mata cewar ita ce Laila, nan aka ara gaisawa tana tambayarta Khalid. Cikin kuka ta hau labarta mata komai da ke faruwa a gidan. Salati Adda Maijidda ke yi tana arawa, jin cewar Hajja ba lafiya hankalinta ya ara tashi. Ta kuwa ce gobe-goben nan za ta taho daga Kaduna. Bayan sun yi sallama nan ma ta kira sauran Aunties in nata. Ba wanda ba ta fa a mishi yanda ake ciki ba, kowannensu hankali ya tashi. Adda Salamatu ma cewa ta yi a daren za ta shigo. Da wannan Kurfi ta an samu nutsuwa, ta na ganin kiran Zeenat sai dai ba ta iya ta amsa ba, arshe kashe wayar ta yi gaba aya ta maida jaka ta oye don ta samu ta huta. Kanta ke ciwo sosai, ta yi kwanciyarta a wurin ta ci gaba da ambaton Allah tana hawaye. Mi ewa ta yi ta fita da nufin zuwa angaren Hajja, sai su ka yi kici us da Hajiya wacce ta fito don yiwa anta rakiya Airport. Ta watsamata kallon banza. "Ina ki ke shirin zuwa?" Ta daure. "Wajen Hajja." Harara ta dankara mata. "Ke ba fa na son yawo, bari ma na fa amaki don ki sani. Aikatau na auke ki, ba ki da maraba da Habiba da Lauratu yanzu a wurina. Babu kuma wanda ya isa ya hana ni aiwatar da abinda na udurta a kanki wallahi. Nan duniya dai ban gan shi ba, saboda na tsaneki, na tsani dangin uwarki kaf in ku. Su kansu ba su isa su ara tako gidan nan ba balle har su ra u da arzi in cikinsa. Kar na ara kama ki za ki sashin kowace mata a gidan nan idan kuwa kin i ji..." Ta katse maganar gami da yin wani shu'umin murmushi. "Za ki ji a jikinki. Mayya dangin mayu." Daga haka ta wuce Jawad da Faruk tafe a bayanta. Ko kallo Kurfin ba ta ishe su ba. Ta juya gwuiwa a sake ta koma, maimakon ta arasa ciki sai ta zauna anan an barandar gaban akin. Ta riga da ta gama gas atawa cewar muddin kana raye toh fa dole sai ka bi addararka daki-daki. Cikakken musulmi kuwa shi ne wanda zai yi imani da mai kyau da marar kyau. Ta yarda cewa Allah Ke jarabtarsu, ta yarda da hakan. Khalid, wanda a kwanakin da suka wuce ta ke jinsa a ranta, wanda ya bar mata sa onni da dama da ba za ta mancesu ba, a yau ya sauya mata cikin lokaci ani wanda ba ta tsammata ba. Ba ma shi aya ba, har da wanda a tunaninta ko duk mutan duniya sun juya baya gareta, to fa shi ba zai juyamata ba saboda cewar shi in mahaifi ne gareta mai matu ar nuna so da auna a gareta. A hankali ta ji hawayenta na zuba, Maminta ta tuna. Ta jima a wannan yanayin kafin ta ha ura ta koma aki domin jiran zuwan Adda Salamatu. Sai dai har aka ci awa babu ita ba labari, wannan yasa ta kunna waya ta kira ta, nan ta soma kuka ta ke fa a mata ta zo amman Masu gadi sun hana ta shiga, kusan ci nata mutunci suka so yi. Koda ta kira Daddy a waya, fa a ya yi wai akan me za ta zo gidan war haka. Ko menene ta koma sai da safe. Kurfi maganar ta mata zafi, amman ta san fin haka za'a gani tunda har suka yiwa Hajja to fa kowa ma zasu yiwa. "Abu aya na sani Adda, su Daddy ba'a hayyacinsu suke ba wallahi. Abinda suka fi bu ata daga garemu bai wuce addu'a ba. Mu dage wajen gayawa Allah." Cewar Kurfi cikin tausasawa. "Shakka babu hakane Laila, tun farko farkon auren shi da Saadatu da irin haka ta faru, bai ara kasancewa ba sai a yanzun. Wannan kam ya fi na baya zafafawa. Amman kamar yanda ki ka ce mu tashi da addu'a hakan za'a yi. Sai dai ki sani daga ke har su Hajja barin gidan za ku yi." Murmushi mai ciwo Kurfi ta yi don kuwa babu inda za ta je, ta gwammace ta zauna ta ga iya gudun ruwan matar. Addu'a ba fashi, ta san a kwana a tashi, zai tabbatu. Jin shiru Adda ta mata sallama daga nan ta ara kashe wayar ta maida jaka. Bacci wannan, Kurfi ba ta samu ta yi ba sakamakon cizon sauro da kuma sauyin makwanci. Duk kuwa da fankar da ke wulwulawa a tsakar akin, hakan bai sa ta samu bacci ba. arshe ganin baccin ya i zuwa, kawai sai ta mi e ta auro alwala ta hau nafila da addu'o'i. Ta jima har aka kira sallar farko wannan ya sa ta jira, ta tashi mutan akin domin sallah. Tana gabatar da Sallar Asubahi a nan inda ta ke bacci ya soma fisgarta, tun tana gyangya awa har dai ta sheme a wurin. Ji tayi an daki gefen cikinta, da sauri ta bu e idanu tana mai ri e wajen da ambaton Allah a baki. Abin ya ara ona ran Hajiya, dama gama wayarsu da Malam kenan ya tabbatar mata aiki ba zai ci Kurfin ba saboda tana da arin kiran Allah a baki a duk sadda ta gani ko ta ji wani abu da ya tsoratar da ita. Ita kuwa agowa tayi don kallon mai mata wannan aika-aika, ta rantse idan Lauratu ce yau sai ta daka ta a gidan. Sai dai wacce ta gani ya sa ta sunkuyar da kai tsabar ba in ciki. "Mayya, kurwata kurr! Kin wani jefamin kallo da wannan idanun naki na mayu. Don ubanki ai ba bacci na nemi ki zo yi sashina ba. Bana bukatar hutunki, wato su sun fita sun kama aiki ke kina nan isassa kin sheme kina baccin mutuwa. Tashi ni ki je ki gyaran akuna!" Ta arashe a tsawance. Dole Kurfi ta mi e ta bi umarninta. Komai na angaren Hajiyar ita ta gyara tas, ta goge na gogewa. Tana gamawa, Hajiya ta ha a ta da gyaran angaren Daddy. Iyakar gajiya ta gaji, hakanan ta daure ta hau gyara, tana yi yana hawaye, ga inta ba inda ba ya ciwo. Nan ma tana kammalawa ta rufe, ta kama hanyar aki ta tsinci muryar Hajiya. "Ina za ki?" Ta juyoa galabaice, Hajiyar na zaune tare da Mama Zahida, gefe guda kuwa, Aliyu ne ke danne-dannensa a waya. Ta arasa ta gaida Mama Zahida, ta amsa fuska a sake tsabar farin cikin yanayin da ta ganta. Hajiya ta kai duba ga Aliyu. "Me za ka ci?" Ya yamutse fuska ba tare da ya kalli kowa ba ya amsa. "Ta soyamin chips da kwai, sai ruwan tea." Ta dubeta. "Sai ki shiga kicin ki kama aiki." Ran Kurfi ya aci, ta daure ta mi e ta nufi hanyar kicin in. Tun kafin ta shige ta ji dariyar Hajiya da Mama Zahida. Tana aikin tana hawaye, a kicin in ta iske Lauratu na goge gas cooker. Ko kallonta ba ta yi ba ta maida hankali ga Habiba da ke gyaran kayan miya. "Ina ku ke ajiyar dankali?" Habiba ta yi mata nuni da wu a, ta arasa ta ebi wanda ta san zai ishi Aliyun. Cikin mintuna ashirin ta kammala komai ta ha a. Koda ta kai Aliyun ne ka ai zaune a falon. Ta ajiye saman centre table, za ta fice ya amsa. "Ke." Ko juyowa ba ta yi ba balle ta amsa. "Ba kya ji ne?" Ta juyo tana dubansa fuska a aure. Ya watsamata harara. "Kwashe na oshi." Wani ululun bakin ciki ya tokare mata a kahon zuci, ta ga rainin wayon ma ya yi yawa, sai dai ba ta ce uffan ba ta kwashe ta kai kicin ta ajiye. akin ta fa a, nan kuwa ta dur ushe sai kuka. Ta yarda dagaske ita in marainiya ce yanzu wacce ta rasa gata a dole.
Chapter 30 · 0% Book details