← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 41

Sashe 20

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani sukuni, lamarin ya zo mishi a bazata don bai ta a tsammanin Hajja za ta mishi wannan shigo-shigo ba zurfin ba. Sai gashinan lokaci guda ta shayar da shi mamaki. Ba ya fatan ya kasance cikin yan uwansa, bai ra'ayin kowaccensu hakan yasa har zuwa ya yi ya samu Hajja ya ro eta alfarmar zai fiddo matar aure nan da kwanaki uku, shi dai babbar bu atarsa su janye udirin yi mishi auren da ya kira na dole. *** Ranar wata laraba da daddare Kurfi na kwance su na lissafa wa anda ya dace a gayyata Dinner, ta nisa ta hau dariya. "Lafiya?" Zeenat ta nemi ba'asi. "Kinsan wallahi ina tausayawa Hafsat kuma dai tana ban dariya. Ta ya ya za'ayi ayi mata aure ga wanda ba ta sani ba don Allah? Nikam na gode Allah da Abbana bai da tsaurin Babanta. Wai! Da ace ma za in ranta za'a auramata ai da sau i. Ko ba komai zai koyamata hankali." Zeenat ta kai mata bugu a cinya, suka sa dariya. "Allah Sarki, kema fa kin so Yaya Khalid innan, yanzu ji dai kamar ba'ayi ba. Kuma fa yanzu da zai ce zai aureki zan yi murna. Wallahi sai yanzu na ke an fahimtarsa, yana da tausayi ko ba komai tausayin ba zai bari ya zalunci mace ba." Zeenat ta hangame baki tana dubanta har ta tsargu ta harareta. "Me akai kuma?" "Na auka mafarki nake ai, yau kece ke yabon mugu?" Murmushi kawai Kurfi ta yi. "Ai har yanzu akwai sauran gyararraki a halayyarsa, ya fiye miskilanci da aure- auren fuska." Dariya kawai Zeenat ta yi, mai ha i dai ba ya fasa halinsa, wayar da aka kirata ya katse hirarsu hakan yasa itama Kurfin mi ewa ta bar mata akin tana mitar Yaya Zahraddeen ya matsa da yawa. *** Ya kur i lemun ba don da i ba sai kawai don kar ya kunyata matar amininnasa wacce ta kawo mishi cike da kulawa. Dawud ya dubeshi a nutse. "To wai ma menene abin tada hankali anan? Bana ji a jikina su Daddy zasu yi maka za in tumun dare." Guntun tsaki ya ja yana dubansa. "Ba wannan bane ka ai aure, aure na nufin kauna, zaman amana, yarda da komai ma. Don me za'a yimin auren dole da girmana?" Dariya ta kama Dawud, ya kuwa shiga yatawa, hakan yasa Khalid dubansa kamar wani ta e. Dawud ya aga mishi hannu sadda ya ke arin controlling kansa. "I'm sorry, kai ne ka ke ban dariya idan kana cewa auren dole. Sai na ke maka kallon irin garadan nan kuma na hangi dolen da ka ke i rari. Bai dace da kai ba. Look." Ya nutsu sosai. "Ka bar danganta hakan da auren dole, sau nawa su na ba ka damar kawo wacce ta dace? Nifa ban ga laifinsu ba, ina ji a jikina za ka yi farin ciki da aurennan. Inama ace Laila za'a auramaka, wallahi da ka fi kowa sa'a." Ha e girar sama da ta asa ya yi lokaci guda ya na mai girgiza kai cikin sauyawar yanayi, idanunsa a lumshe. "No, ita wannan amanar Mami ce a gareni, na bata kulawa tamkar anwata. Banda haka, gwara kowa ma a kanta ita, bar maganar kar raina ya aci." Murmushi Dawud ya yi mai tarin fassarori sai dai bai ce komai in ba har suka sauya akalar hirar inda suka hau batun shirin bikin dole . Daddy ya riga da ya auke mishi lefe, don ya ce wannan ma iyarsa ce, shi ne mai ha awa. A farko ya zargi ko Laila in ce sai kuma jin ita karatu aka bata damar yi yasa ya kauda batun. Idan kuwa Hafsa ce to ranar da ta sake ta shigo gidansa allata kawai zai yi a huta. *** Cikin hukuncin Allah aka shiga satin biki gadan-gadan, Amare sun sha gyara na musamman. Duk wani gyara kuwa har Kurfi ake yi domin kuwa daga an zo gyarawa Zeenat fata, Hajja za ta zugata ta ce ya kamata itama ta yi tunda ita ce anwa kuma kusan awa ga Zeenat. Ba musu kuwa za ta bada kai, duk da yanayin Kurfin ya sauya ba kamar da ba, ta rage rawar kai. Hatta da lalle kusan iri aya akai musu, sai dai duk wannan bai sanya tunanin komai a zuciyar Laila ba har sai da aka zo ga ar shan magani da cin kaza. Anan ne jikinta ya yi sanyi, sai ta ji su Anti Fahima na cewa itama ta ci don zai mata aiki. Har dai ta gaji ta tambaya. "Wai ko nima dai Amaryar nan ce oyemin ku ke yi?" Anti Fahimta sai dai su yi murmushi. Wannan inma amsa ce gareta, tambayar duniya ta yi ga Zeenat amma mursisi ta nuna ita ba abinda ta sani. Safiyar talata inda a ranar ne za'a yi Kamu, Abba ya kira Kurfi zuwa angarensa, itama ba jinkiri, kamar yanda ta saba duk sadda za ta je bayan mutuwar Mami, wannan karon da azamarta ta tafi don shi ka ai ya rage da zata tambaya ya fa i mata gaskiya. Hajja ta ce bata da labarin komai wanda kawai kallonsu take ba tare da ta yarda ba. Yana zaune yana kallon labaran safe, ganinta yasa ya rage karar talabijin in. Fuska a sake ya ke dubanta. "A'a kaga Amarya. Kinga yanda ki ke wani kyalli kuwa?" Gabanta ya fa i, ta tabbata ita Amaryar ce kenan. Ta karasa a sanyaye ta zaune gefensa. "Abba nima Amarya ce kenan?" Murmushi ya yi kafin ya an gyara zama ya maida nutsuwarsa gareta. "Mafarkin Maminki kenan Laila. Burinta a aurar da ke, bata da burin ki ora karatu daga sakandire kina zaune a gida. Kin fi kowa sanin wannan." Ta gya a kai, tasan da hakan, ba shi ta ke bu atar ji ba. Ta dubeshi fuska a raunane. "To amma Abba wa za ku auramin?" Gani ta yi ya an juya ya zura hannu arkashin pillow na kujera ya auko wani hoto. arshe ya mi amata. Hannu na rawa ta kar a, wanda ta gani ne ya sanyata jifa da hoton tana mai furta No da iyakar karfinta. Kawai kuma sai ta yi zaman dirshan a asa ta sanya ihun kuka. Abba ya zuba hannu a ha a yana kallonta a sanyaye, shi bai hanata kukan ba, shi kuma bai rarrasheta ba. Sai da ta yi iya yinta tana sambatun wai ya bar sonta saboda Mami ta bar duniya. Kowa yanzu ya tsaneta, maganganun na shigarsa amman bai ce komai ba, can da ya ga ta gaji ta dawo ro onsa akan a janye da batun aurenta da *YAYA KHALID* a bata damar za ar miji, sai ya dakatar da ita gami da rike hannunta ya mi ar da ita tsaye. arshe ya zaunar da ita gefensa. "Laila." Kanta a asa ta amsa. "Naam." "Kin yarda Allah aya ne?" Ta gya a kai. "Na yarda." "Kin yarda ni AbdulHamid, ba zan ta a yin abinda nasan zai cutar da rayuwarki ko kuma zai ba anta ran Maminki idan da ace tana duniya ba?" Cikin muryar kuka, can asa- asa ta amsa cike da fatan ya ce an fasa tunda bata so. "Eh." "To wallahi Maminki ta jima tana son aurenki da Khalid, sai dai tsoronta aya, iyayyar Hajiyarsa a gareta, tasan shi zai ba ki matsala. Ta sha fa amin tana da ya inin Khalid zai ri e ki amana, ba zai bari wani abu ya cutarmata da ke ba. Hakazalika ta sha mafarke-mafarke akan lamarinki da shi sai dai takan sare idan ta tuna kamar ba zai yiwu ba hakan yasa bata ta a yi miki zancen ba, arshe kuma ta koma fatan ya ri e ki tamkar ri on ya da anwa don takan karaya ta ga kamar ba lallai fatanta ba ya cika, tunda kuma Allah Ya cika yanzu, to hakan ya fi mana komai da i. Abinda nake so ki fahimta shi ne, aure *MUKADDARI* ne daga Allah, babu ta yanda za'ayi bawa ya auri wanda Allah bai yi shi ne abokin rayuwarsa ba. Babban abinda ya sanya muka ha aki da Khalid bai wuce don ganin an arfafa zumunci da kuma son ganin Hajiya ta sauya ta bar wannan zazzafar iyayyar da ta ke nuna maki ba. Mun san abu ne mai wuya, amman kuma mu munsan wa anda muka za a, ba za ku kunyatar da mu ba." Abba ya ci gaba da yi mata nasiha da bata misali irin ha uri da juriya na matan Annabawa da Sahabbai da ma sauransu. Tun urfi na hangen tsanarta akai aka ha ata da mutum irin Yaya Khalid wanda zuciyarsa babu gurbin kowace mace sai ta Sumayya, har ta sauko ta rungumi komai matsayin Kaddara. Babu ta yadda za'ayi ta kaucemata kamar yanda Abba ya misalta. Ta rasa Mami, za ta yi ari wajen ganin ta cika burinta na son ta yi aure. Tasan a duk inda ta ke, za ta ji da Ta ago ta dubi Abba da murmushi auke saman fuskarta ga kuma ruwan hawaye lokaci guda. "Shi ke nan Abba, ka ta ya ni addu'a." Don farin ciki sai da ya ji kwalla ta taho mishi. "Allah Yay miki albarka, Ya faranta maki fiye da yanda kika farantamin. Kwana nake na tashi da fargabar yanda zan tunkareki da zancen aurennan Laila, sai dai kuma na manta cewar ke jinin Sadiya ce. Ba za ki ta a ba amin asa a idanu ba. Allah Ya kyautata makwancin Mahaifiyarki, in sha Allah tana Aljanna. Allah Ya sanya albarka a rayuwar aurenki da Khalid." Ta sunkuyar da kai tana goge hawaye, sai ya bata tausayi ganin yanda ya ke faman addu'a ga shi sai washe ha ora ya ke na alamun yana cike da farin cikin biyayyar da ta yi musu. A haka suka rabu ta koma angaren Hajja. Nan ma Hajja ta zaunar da ita ta kara da nata nasihar, har ta gama ba ta ce uffan ba. Duk wani abu da za'a ce ta aikata ta bar musu, yi kawai ta ke. Zeenat ta bata ha uri bisa rashin sanar da ita ko waye mijin sanin da ta yi ba ta aunarsa. Nan ma dai murmushin ya e ta
Chapter 20 · 0% Book details