Sashe 25
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan sadda za ta yiwa ba i rakiya. Abinci kuwa kullum Hajiya ke aikensa, ba ta ci sai dai shi ya ci abinsa. Ko a gidan Hajiya ba basu abincin sallah ba ta ke, bata jin ta ta a cin girkinta, akan me yanzu ta e mata aiken girki? Ganin abin bai kwanta a ranta ba ya sa sam ba ta ci, shi kam da yake ba kuka ya ke ba yasa bai fahimtar ta ci ko ba ta ci ba Yau kawai ta ji zaman ya isheta don haka ta kunna tv, tun zuwanta ko kallo basu isheta ba sai yau ta ji tana son kallon don haka sai ta mi e ta kunna. Bayan gama searching sai ga channels kala-kala, murna ta cikata ganin tashar da ta ke kalla wato Starlife. A rayuwarta tana son Indian series, sam, bata gajiya da kallonsu. Duk kuwa da irin zagin da suke sha wataran a wajenta idan sun kai ta bango da kayan haushinsu. Zama ta yi ta tan washe afafuwa tana kallo, ta shagala sosai ta yanda har ya shigo ya yi mata sallama ba ta san ya yi ba sai da ta ji an sanya hannu an zare remote in daga hannunta, a firgice ta buga tsalle ta tashi gami da sakin ihu. Sai kuma ta ha a ido da shi, ajiyar zuciya ta saki sannan ta koma ta zauna. Ya aga gira. "Ki dunga rage sauti ya na yawa, sai a shigo a sace ki ma ba ki sani ba, san nan ki dunga rufe ofar asa idan za ki yi zaman kallonki." Ta kuwa kalle shi tana murmushi a asan ranta, ya maida ita ma wata ar yarinya. "Ni zan an fita, Aliyu zai zo kawo maki abinci. Ga wannan ki ba shi idan ya zo." Hannu yasa a aljihun gaban rigar shaddarsa fara al ya ciro an dubu har biyar ya mi amata. Ta sa hannu ta kar a bisa kuskure ta gogi hannunsa. Lokaci guda suka dubi juna kan ta yi azamar gyarawa. "Toh, a dawo lafiya." "Allah Yasa." Ya bata amsa sadda ya ke ficewa. Maganganunsa ta shiga tariyowa, Aliyu zai kawomata abinci kuma inji Hajiya? Anya kuwa ta ji daidai? Sai dai ta share maganar ta ci gaba da kallonta amman daga ta tuna Aliyu na hanyar gidan sai gabanta ya fa i. Tunda aka yi bikin ma ba ta sanya shi a idanunta ba. "Ya dai kamata na soma girkina tunda dai ni ban au kaina a Amaryar ba hakanan Yaya Khalid bai aukeni wata Amaryarsa ba." Tana nan zaune ta ji ana wasawa da arfi kamar za'a alla ofar, tun dai bata yarda bugun ake yi ba har dai ta mi e ta nufi asan. Sai da ta dafe irji don razana don ta san shi ka ai zai yi wannan banzan bugun. Bu ewa ta yi su kai kici us kuwa, ya wani tamke fuska yana harare-harare. "Kin bar mutane na ta buga ofa don wula anci." Ba ta ce komai ba, ta an matsa don ya shigo amman ya dire abincin a ofar. "Ke a su wa? Haba Malama ai ba gidanki bane, da na so shiga zan shiga ne kaina tsaye babu wani jiran iso. Niyyar ce ban yi ba shiyasa ma na wasa." Kamar ta ce me ya hana shi ba Maigadi ya mi o, sai kawai ta ga ata lokaci ne biye mishi don haka ta ja baki ta yi shiru tana murmushin tura haushi. Ya kuwa ulu da murmushin, wato ita ga matar Yaya. Aikuwa ya kudurce turamata haushi da zantukansa. "Da in abin ma auren cushe ne, Yayanmu ba so ya ke ba. Mu kam ba za mu bar kewar Anti Sumayya ba, daga kanta mace ta are kuma inada ya inin har a idanun Yaya." Daga haka ya yi wani murmushi duk da itama bata bar nata ba, asalima sunkuya wa ta yi ta auki kwandon kayan abincin. Murmushinsa bai wuce na sanin da ya yi ya sha a mata ba ne koda ba ta nuna in ba kuwa, bai saurareta ba ya juya ya fice abinsa cike da nisha i yana feeto da baki. Ta rufe ofar ta sanya mu ulli, ba ta yi gigin zubda hawaye ba saboda ta san dama yanzu ne aka fara wasan, fatan ta Allah Ya sa komai ya zo mata da sau Koda ta duba, tuwon masara da miyar agushi ne da ya ji nama da kifi. A haka dai kamar ka sa hannu ka ci, murmushi kawai ta yi domin kuwa ta gode Allah ma tuwo ba cimarta bace, sam ba ta so. Idan kuwa shi ake yi a ranar to tukunyarta daban. Sauke ajiyar zuciya ta yi ta jerawa Yaya Khalid saman tebur a nan asan ganin nan ya ke zama ya ci yanzun, ta ajiye kwandon gefe. Kai tsaye kicin ta fa a, a jikin kicin in akwai ofar store don haka ta bu e ta shiga, komai na kayan abinci ba wanda babu a ciki, ta auki Indomie ta dawo ta bu e firij ta au kwai sanin da ta yi shi ka ai ne zai mata saurin kammalawa. Cikin mintuna biyar kuwa ta kammala ta ci abinta. Tana komawa sama ta tadda missedcalls in Tasleem, da sauri kuwa ta bi bayan kiran tana jin wani sanyi a ranta. Bayan an aga Tasleem ta ce, "Ran Amarya ya da e, da alama kina turakar Oga." Yamutse fuska ta yi. "Ke meye haka?" Dariya ta yi. "Afuwan matar babban Yaya kada ki sa idan na zo ya sa a min korar kare na ta a ki, ya kike toh?" "Ban sani ba tunda abin ya zama tsokana." Dariyar dai ta ara yi. "To Allah Ya ba ki ha uri. Amman dai Allah Yasa yanzu kin saki jiki kin rungumi wannan auren hannu bibbiyu." "Hum, hannu aya ba ya aukar jinka. Koda zai auka ma na gwammace na ha ura da na wahala." "Sannu, ayi dai mu gani toh. Ya zaman shiru? Ai na shiga gidanku jiya ganin Mu'azzam." Jin haka ta okantu ta ji labarinsa. "Dagaske? Fatan kowa lafiya?" "Sumul Alhamdulillah, ba ki gan shi ba sai ara mulmulewa ya ke. Na mishi hoto ma zan aiko maki." "Kai amman kin kyauta ar uwa. Don dai Hajja ta i bari na auke shi ne wallahi, amman shirun nan ma ai aiki ne." Tasleem na dariya ta amsa. "Ibadar ce dai duka, fatan kin gyara sashin Yayan naki?" Oho, ita ko a ka ba ta kawo ta yi hakan ba. Cikin rashin kula ta ba ta amsa. "Ko hanyar sashin nasa ban sani ba Tasleem." Jin haka duk sai Tasleem abin ya yi mata ba da i. Nan ta hau fa a irin yanda ya kyautu a matsayinsu na tsararrakin juna. Ta nuna mata illar da ke tattare da rashin kyautata mishi don kuwa ko da ace aure bai ha a ba yayanta ne ballantana kuma auren ya riga da ya ha Jikinta duk ya bi ya mutu, kuma fa haka ne. Wannan ta sa bayan sun yi sallama ta mi e gami da zura silifas in ta. Tana fita ta nufi wata ofa da ke gefen nata daga an hawo steps wanda ba ta ta a shigar ta ba sai a ranar. Jikinta ne ya ba ta cewar nan ne angarensa. Ta tura a hankali da shiga da sallama. amshi dadda a na turarukansa ya shiga ofofin hancinta. "Wow." Shi ne abinda ta furta ganin kayan da aka zuba a falon. Kwalliyar fari da ruwan toka akai ga aya, ba wani tarkace aka zuba ba amman dai tsarin ya yi kyau. Gyaran ba wani mai yawa ba ne da alama yakan arta tattarawa sai dai akwai ura da shar ka an. Ta arasa akin, shima ya yi kyau sosai da adon ja da ba i, ya ha u sosai ya yi tsari kuma. Kayansa da ya cire duk ya ajiyesu jikin hanger sai wasu a asa. Ta numfasa, a nutse ta hau gyara. Ta kakka e gadon kenan, ta ji fa uwar abu, dubawan da za ta yi ta ga hoto ne, ta kai hannu ta auka tana duba. Maganganun Aliyu ne ya dawomata tsaf a kwakwalwa. Kyakkyawa ce ta in karawa, ta sa alo hannayenta saman irjinsa yayinda ya wani antar da idanun yana murmushi wanda har dimple insa ya fito. Itama murmushin ne saman nata idanun. Ba ta son shi, amman sai da ta ji ranta ya sosu. Wato dai Sumayya ta mutu amman ba ta mutu ba a zuciyarsa, tausayin kanta ya kama ta, ta san ba zai ta a kallonta da sunan matarsa ta sunnah ba, ta san wahala kawai za ta ci a hannunsa. Ba ta san ta na hawaye ba sai da ta ji saukarsu saman hoton. "Allah Yay muku rahma." Ta furta a fili kafin ta ci gaba da gyara. Bini-bini hankalinta na ga hoton da ta ora saman gefen durowar gadon, ba ta san meyasa ta ke jin ba da i ba. Har ta kammala gyaran, sai kawai ta a ta juya hoton don ba ta son gani, ta saka a ranta watakil fuskar Sumayyar ke ba ta tsoro. Sai da ta kammala da aki san nan ta fa a ban akin ta soma wankewa. Kafin ta gama kuwa ta an ji e, tana fitowa ta ga mutum daga shi sai singilet da dogon wando na shaddarsa, yana zaune gefen gadon yana arin cire agogon da ke aure a tsintsiyar hannunsa. Sai da irjinta ya buga domin har ga Allah ta tsorata, tunaninta ta ina ya shigo alhalin ta rufe ofar kuma mu ullin na jiki. Ya ago fararen idanunsa ya zubamata, ta yi saurin auke nata don ba za ta juri ganinsa ba sutura ba kasancewar irarsa sosai ta fito. Ya kauda kansa ya ci gaba da abinda ya ke, a asan ransa kuwa ya yaba da abinda ta yi, bai san tana da hankali har haka ba, yanda ta lailaye gadon ba aramin burgeshi ya yi ba. "Yaya sannu da dawowa." Ta fa i bayan ta an russuna, ya amsa a tausashe san nan ta mi e ta fice ri e da bokitin da ta sanya towel in da ta goge tiles asan