Sashe 31
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** arfe uku da rana su Adda Maijidda suka iso, tare ta ke da mijinta. Ba jimawa su Adda Fatima da Salamatu duk suka shigo. Maigadin bai hana ba ganin dattijo da shigar kamala irin mijin Adda Maijidda. Koda sauran ma suka iso, shiga kawai su ka yi. A sashin Hajja suka yada zango, yaranta sun sha kuka ganin yanayin da ta ke ciki. Nan da nan kuwa Adda Maijidda ta au waya ta kirasu kaf insu an uwan, ba su suka shigo gidan ba sai yamma. Fa a ta shiga yi ba autawa, sai dai ga mamakinta abin ko gezau. Asalima Daddy wanda ya fi dukkansu sha uwa da ita da matu ar girmama ta, shi ne farkon dakatar da ita a tsawance. "Kinga MAIJIDDA, kar ki fa an maganar banza mana! Ai ba fin mu son uwarmu ki kai ba, kuma ki ka san shirim da muke yi ne akan ta? Hajiya ta ce muddin akai cinikin shekara za'ayi amfani da ku en a fitar da ita waje. Amman dai ku ba kwa ganin abinda muke yi, shekarar Hajjar nawa a wajenmu muna hidimta mata? Mun ta a nuna gajiyawa da har za ki wani nemi gayamana magana ki goranta mana? Ai idan baa gode mana ba ba fa za'a zagemu ba." Adda Maijidda if ta yi cikin juyayin maganar. Su kuwa sauran dama sharar kwalla suke. "Haba Alhaji Hamza, kar ka manta uwa uwa ce. Kuma.." "Kai Engineer dakata! Hajja ina ce uwarmu ce ba taku ba? Idan muna magana a matsayinka na bare ka dunga yin shiru. Wannan abu ne da ya shafemu ba ruwanka! Idan abin dagaske me kai ka au nauyinta mana. Ku in fa ba daga sama ake mana ruwansu ba!" in Baba Mudassir kenan cike da sababi. Kowannensu ya fahimci abin ba laifinsu bane, sun san ba haka halinsu yake ba, wannan ce ta sanya Engineer duban Matarsa da annenta bayan fitar mazan. "Ku yi ha uri, ku yarda da cewa wannan abu jarrabawa ce daga Allah babu yanda kuma za'a iya tsallakewa." "Engineer jikina ya na bani abubuwa da dama, ina jin cewar ba alau wa annan mutanen suke ba. Akwai wata a asa." Fa in Adda Maijidda a sa'ilin da ta ke arin goge fuskarta ganin Hajja na hawaye. "Dama ina fa, nida jiyan nan da na zo suka sa akai min korar kare? Hum." Adda Salamatu ke wannan magana ta na shesshe a. Tun da take, ba'a ta a cin mutuncinta irin jiya ba. Nan dai Engineer ya lalla asu gami da yi musu nasiha. Adda Maijidda ta mi "Bari naje na taho da Lailatu, ba zan yarda da zaman ta a hannun wannan matar da ba Allah a ranta ba." Daga haka ta fita zuwa angaren Hajiya. Ta iske ta zaune a falo ta kammala cin abinci ita kuwa Kurfi na aikin tattara kwanukan. Sallamarta ce ta sanya Kurfin dubanta, ai sai ta ajiye tiren ta arasa a guje ta rungumeta tana kuka mai tsanani itama Adda Maijidda na matsar kwalla. Hajiya ko gezau sai ma ara kishingi a da ta yi tana musu kallon raini. "Yi shirunki Lailatu, in sha Allah ba za ki ara zubar hawaye ba, maza je ki auko kayanki mu tafi." Jin haka Hajiya ta mi e tsaye. "Ke Maijidda, ki ficemin a ido wallahi idan ba haka ba zan miki tozarcin da ba ki ta a tsammata ba! ana take aure kuma ya zame mata dole ta bi umarninsa! Daga ke har yaku bayin da kika ebo ku ka zo ba ku ishi Saadatu kallo ba, don haka cikin mutunci ki ja su ku ficemin anan!" Adda Maijidda ta yi murmushi. "Saadatu kenan, to ko AbdulHamidu bai isa ya sanya na i tafiya da Lailatu ba a yau ballantana kuma ke in banza! Idan kina ta ama da shirka, mu mun yi imani da Allah. Shi ne Mai amsa mana kuma Mai maganin makirai. Sannu-sannu za'a wayi gari wataran asirinki ya tonu. Aron lokaci ki ka samu kinsan duk wanda ya samu wuri sai ya yi shanya. Amman watarana sai labari. Lailatu taho muje." Ta kama hannun Kurfi ta juya, sai dai cak Kurfi ta tsaya ta i tafiya motsi. Ganin haka Adda Maijidda ta juyo tana dubanta. "Taho mu wuce mana." Ba ta ce uffan ba sai kuka kawai da take kanta a asa. Shewa Hajiya ta yi gami da tafa hannu sa'ilin da ta ke tunkaro inda suke. "Haba Maijidda, ke a su wa? Yaushe wuyanki yay tsaikon da zai yi kafa a-kafa a da lamurana? Wallahi ke ba kowa bace a wajena! Don haka tun wuri ki kiyaye ni." Daga haka ta nufi matattakalar bene tana dariya. Adda Maijidda ba magana sai kallon da ta ke bin Kurfi da shi cike da mamaki. Kurfi sai a sannan ta magantu cikin rawar murya da shess hekar kuka. "Adda ba zan iya etare umarnin Mijina ba, ki yi ha uri. Ina tsoron fa awa fushin Mahaliccina. Ki yafemin don Allah." Ta arashe gami da zubewa kan afafunta tana kuka sosai. Adda Maijidda ta gya a kai tana sharar kwalla. "Shi ke nan Laila, ba zan iya cewa komai ba kuma anan, sai dai ina so ki ri i addu'a, kar ki wasa da ibada. Kar ki dunga zama ba alwala. Mu ma ba zamu zauna haka ba, komai zai daidaita in sha Allah. Yanzu zan tafi da Hajja da Mu'azzam don ba zan bar su a wannan rayuwa ba. Ki ci gaba da ha uri da addu'a, in sha Allah mu keda nasara. Allah Yay miki albarka, Ya gyaramana wannan lamari." Kurfi ta yi murmushi gami da amsawa da amin. Adda Maijidda ta ce su je ta yi sallama da Hajja da aninta. Ta ce tana zuwa. Bayan fitar Adda Maijidda, da sauri ta kimtsa wurin da Hajiya ta ci abinci sannan ta bi bayanta. Tana shiga sashin Hajja ta fashe da kuka ganin har sun ha a akwatin kaya sun fiddo. Ta arasa ta fa a jikin Adda Salamatu, sannan Adda Fatima kafin daga bisani ta waiwayi Adda Badi'atu da Basira. Sun sha kukansu sun oshi, sun yi mamaki jin cewar ba za ta bisu ba daga bakin Adda Maijidda. Nan kuma suka hau fa a, Engineer ne ya dakatar da su gami da nuna musu hakan ma daidai ne. Ta fisu gaskiya tunda kuwa biyayya ce ta aure ta ke arin bi. Don haka ba laifi. Ya ara da cewa. "Kuma ku sani, wala ace Laila tana gidannan ko ba ta nan, abinda fa Allah Ya addaro zai faru a kanta babu makawa sai ya afku. Bamu isa mun hana ba, don haka ku kyaleta. Allah Yana tare da ita." Suka ci gaba da kallon Kurfi ganin ta duk ta fa a sai fari. Ba jimawa suka mi e don tafiya don kuwa hatta da su Balaraba gidan zasu bari. Lami daman ba kowa ne da ita a Kano ba, asalinta ar Nijar, hakan yasa da ita zasu wuce Kaduna. Balaraba ce za ta koma gidan yayanta domin ta soma sanar da batun zuwa Kaduna don jinyar Hajja. A haka suka rabu ds Balaraba, Kurfi na ame da aninta tana kuka shi kuwa idanu kawai ya uramata, wani sa'in ya hau dukan fuskar yana dariya yayinda wani lokacin sai ya yi shiru ya ura mata ido. Suna kuka tana kuka haka suka rabu, bayan fitarsu ta shige Garden ta zauna ta sha kuka son ranta. Sai da ta gama kafin ta ara dun ule mu ullin angaren Hajja da suka dam a mata ta oye shi a inda babu mai gani sannan ta koma angaren Hajiya. Kai tsaye akinsu ta shiga ta adana. Daidai da an uwan Mami bayan sun ji labari, sun yi sun yi akan Laila ta bar gidan amman sam ta i. Abin har ya ba su haushi, arshe kuma suka fahimceta. Sau aya Tasleem ta zo duba ta, a na biyu korar kare akai mata arshe ma aka hanata zuwa gaba aya. Toh haka Hajiya ke sanyawa a yi ga duk wanda ya ji anci dangin mazajen ko kuwa Mami. Akwai sadda ta tashi da ciwon kai da zazza i mai zafi, duk da wannan yanayin Hajiya ba ta fasa sanya ta aiki ba har sai da ta ga tana shirin mutuwa sannan ta sanya Habiba mi a ta Kemis. Kwanaki uku ta samu rangwame ta ora aiki daga inda ta tsaya. Ba ta wasa da addu'a, koyaushe idan ba ta komai za ka sameta da Alkur'ani tana tilawa. Wannan ba aramin ara dugunzuma zuciyar Hajiya ya ke ba. Ta sha ta hana ta ta hanyar kiranta ta sanyata aiki daga wannan sai wancan. Akwai ranar da ta dukufa tana gugar tiles a karo na uku don sau biyu kenan Aliyu na maido ta baya ta hanyar zubda lemo da gangan a na farko, a karo na biyu kuwa sai ya hau zazzaga ruwan hypo yana masifar wai arni gugan ya ke bai fita ba. Kallonsa kawai ta yi ta kauda kai, sau inta ma ta ji ana labarin zai wuce asar waje domin yin Degree a can. Ko ba komai za ta samu sau in zuciyarta. Tana cikin yi ta ji tashin muryar Daddy daga sashin Ummi. Fa a yake sosai wai ta kirashi mara adalci har tana mishi batun irin masu haka na tashi da shanyayyen arin jiki. Shi aure ne ba zai yiwa Munira da mutumin banza ba, idan kuwa hakan ne rashin adalcin toh ta yi ta ganin hakan. Ta yi abinda za ta yi. Kurfi ta ji kirjinta ya buga, ba ta so maganar ba sanin da ta yi ba laifinsa bane tunda da ai ba hakan yake ba, sai dai kuma tasan yau da gobe ce ta fusata Ummin ta fa i da zafi. Gani tayi Hajiya ta sauko daga bene ha ora duka a washe, ko lura da ita ba ta yi ba ta fice da sauri zuwa tsakar gidan. Kurfi ta girgiza kai cike da tausayin Ummi don tasan Hajiya ba dai za ta tausa ba sai dai ta ara rura wutar abin. Tana gugan amman hankalinta na can, tana jin Hajiya na fa "Ke kam Raliya ba ki da godiyar Allah, duk irin kyautatawar da Alhaji