← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 41

Sashe 13

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fasuwa, ta zauna tana dariya. "Kyau nayi miki kenan, kin manta inkiyar Abbana balarabe?." Ta gyada kai. "Ah sosaima, na kuwa manta." Sai san nan ta gaisheta, ta amsa gami da tambayar Mami da jiki. Kurfi ta zaro ido a tsorace. "Lah bata da lafiya ne?" "Yo mai juna biyu ai lalla6awa yake, yau lafiya gobe da sauki." "Wa ya fadamaki Mami nada ciki? Nidai kinga ba ni na fada ba kar ki ja min fadan Abba." uwa ta yi mata. "Ubanki ne ya fadamin, jimin ja'irar yarinya. Wato nima sai a barni a duhu?" Dariya sosai Kurfi tayi, ta mike. "Ni kinga na tafi zan zo mu yi hirar anjima." Murmushi tayi. "Ina jiranki, shi dai ciki ba'a oyensa." Bata ce komai ba ta fice. Karfe goma aka daura auren Yaya Hassan da Aisha shi kuma Yaya Hussain da Rahma. Nan fa aka yi ta gu a da fatan alheri. Ba jimawa sai ga tawagar angwaye da abokansu. Yanmatan gaba daya su na bangaren Hajja tare da Amare. Hotuna suke tayi, koda suka ji tahowar angwaye, nan da nan suka rufewa Amaren fuska, bayan shigowarsu ma suka rantse ba zasu ga fuskar ba sai an biya. Aka yita dariya da zolaya. Kurfi da su Tasleem sun fi kowa za ewa, wani abokin su Yaya Hussain wanda tun farawarsu bai magana sai kallo da murmushi ya zura hannu a aljihu ya fiddo yan dari biyar biyar ba tare da ya kirga ba ta damkawa Kurfi. Nan suka yi ihu har da masu gu a sannan aka bari Angwaye suka isa ga Amarensu, ba karamin kyau sukai ba. Sai dai Amaren duk sun so su 6ata kwalliyar da ruwan hawaye. An dai yi hotuna sosai kafin su soma fita zuwa sashen sauran matan gidan domin mika gaisuwa. Su kuwa su na biye da su a baya banda Amare. "Ba mu yi hoto ba, Hajiyar kau Ta kai duba ga mai maganar, shi ne dai wanda ya fiddo kudi ya basu, nan da nan ta saki fuska. "Ai ni bana hoto sosai." "Karya take wallahi." Tasleem tayi caraf ta amshe. Harara Kurfi ta kai mata shi dai murmushi yake. "Kyaleta a bata yin, yanzu dai a ban lambar waya." Kamar tace bata da waya sai kuma ta ga ba zata cuci kanta ba, aikuwa ta karanto mishi tsaf ya adana, zai maida wayar ya ce. "Ko ba daidai aka ban ba, zan kama kafa da Sis Fahima." Dariya kawai tayi suka wuce, sai a sannan ta fahimci ko waye, kanin mijin Anti Fahima ne, yayar Zeenat. Wannan karon har falon Hajiya itama ta shiga, tana kallonsu su na hotuna tsaye daga gefe, ba shiri ta ji an hankadeta, a fusace ta dubi mai shi, Hafsat ce, su na hada ido ta bankamata harara, har tayi gaba ta dawo saitinta. "Ai fa, sai dai ki are a ire-iren su Kamal din wadanda fuska ba fasali, ki kyale babban goro don kuwa shi sai magogin karfe. Banza kawai da batasan abinda ya dace da ita ba." Daga haka ta ja tsaki tayi gaba, ranta ya 6aci sai dai ba sosai ba, ya ci kuma ta soma sabawa da wannan cin kashin nasu, ta dorawa kanta laifi da ta shigo bangaren, banda haka, ashe ma Hafsar ta lura da sadda sukai magana da mutumin da yanzu ta ke jin sunansa, wato Kamal. Juyawa tayi ta fice abinta, a hanya suka yi kici6us da shi tare da Dawud. Yau dinma ankon farar shadda su kai abinsu tsaf. Ta sha aikin blue, karshen haduwa sun hadu. Da yake ranta ba dadi, gaishesu tayi sama-sama, koda Dawud ya ja ta da wasa kawai murmushi tayi ta kara gaba. Bata da masaniyar ya biyo bayanta sai muryarsa ta ji dab da za ta shiga bangarensu. "Yau kuma me ya faru?" Ta saki fuska da murmushi. "Ba komai." Ya daure fuska. "Ni za ki yiwa karya? Jiya ma haka kikaimin saboda na gani da idona duk abinda kuke da Aliyu, yanzun ma haka kike so?" Kawai sai ya bata dariya kuma hakikanin gaskiya yau ta ji ya burgeta, ashe akwai wani bangare na halayyarsa mai kyau? Kodayake, dama ba'a rasa nono a ruga, ba yanda zaayi ace gaba daya halayyar mutum munana ne. "Dariya?" Abinda ya furta ne ya maidota hayyacinta, ta yi saurin gimtse fuska gami da rufe bakin. "Aa, yi hakuri. Amman ni banda wata damuwa." Ya gyada kai. "Ok, a condition na Mami bai kamata ki dunga kai mata maganganun tashin hankali bane. Ba don ita ba ba ki isa na damu da damuwarki ba." Yana fadin haka ya juya ya wuce abinsa, ta bishi da kallon harara gami da murguda baki, mai hali dai ba ya fasa halinsa. Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, ita ai ya gama yi mata komai tunda har ya damu da Maminta. Karfe bakwai na yamma aka kai amare gidajensu. Kwana uku da biki kowa ya watse zuwa muhallinsa gidan ya koma kamar yanda yake, daga su sai su. Daga nan kuma su Kurfi suka shiga shirin jarrabawarsu ta karshen zangon karatu na fita daga sakandire. Wannan yasa bata da hutu, su na dawowa gida kuma ga Islamiyya, da zarar ta dawo za ta kusan wuni tare da Mami tana tayata ayyuka ita da Zeenat. Sai lokacin kwanciya su ke karatu don sai su jima basu kwanta ba. Wannan yasa sam basu da lokacin komai, daidai da wayarta ta kashe ta ajiye. Zeenat ta fahimci abin na yi ne, koda dai tsaurin makarantar yasa dole ba abinda zai taimakesu din sai Addu'a da kuma karatun. Domin sam ba'a yarda da satar jarrabawa ba, ko wadanda suka kammala suka fita basu yi. Sadda mai makarantar ya ta6a kama wani, har gobe bai ba shi certificate na kammala makarantar ba sai hakanan aka hakura ya chanja jarrabawa. Wannan ne dalilin da yasa suke ba karatu himma kwarai don kuwa kwakwalwarsu ce za ta yi aiki. Satinsu daya suka soma jarrabawar Waec, nan fa kai ya kara daukar zafi don ma dai da tazara (intervals) tsakanin papers din. Islamiyya kuwa sai alfarma suka rok'a suka bar zuwa duk ranar da zasu yi jarrabawa, sai dai sukan yi kokarin tilawa a gida don ko kusa iyayen basu kaunar wasa da karatun islamiyya, shiyasa duk sadda aka samu tazara to kuwa zasu je. . *** Kwanci tashi asarar mai rai, har anyi watanni biyu, lokacin kammala jarrabawarsu Kurfi ya zo, sun kammala cike da nasara, ranar dai an sha murna. Lokacin sati daya ya rage a soma azumi. Yan matan gidan masoya Yaya Khalid kuwa, tun su na jira su ji maganar wacce ya za6a har dai su ka gaji suka share batun ganin ita kanta Hajja bata kuma tayarwa ba. Wannan bai ba Kurfi mamaki ba sai ma dariya da ta yi musu, ganin Zeenat har da su kuka da shiga damuwa ya sanya jikinta kuma ya yi sanyi ta bari. Karshe dai batasan ya akai ba sai gani tayi Zeenat sun dinke da cousin dinsu Zahraddeen, yakan kira a wayar Mami su sha hira abinsu, ba karamin dadi kamarin ya yiwa Kurfi ba, ko ba komai shima ba baya ba wurin kyan fuska da kuma hali. Ana jibi za'a soma azumi gaba daya gidan aka hau gyara. Kowane angare idan ka shiga kakka e-kakka e kawai ake yi da cire yana. Kurfi ta yi jifa da tsumma a gefen bokiti san nan ta zube a asa. Zeenat da ke goge fankar falon ta dubeta. "Lafiya?" Ta tankwashe afa gami da buga tagumi da hannu biyu. "Ke azumi fa za'a shiga ko kin manta ne?" Dariya sosai Zeenat ta sanya. "To sai akai me? Kefa ba ki da hakuri akan abinda zai ta a cikinki." "Kuma dole ta yi ba, kul na sake jin kina jimamin azumi, idan ya taho murna ake yi saboda za'a shiga watan bautawa Ubangiji, watan da ya fi kowanne rahma da aukaka. Wataran duk sonmu da mu yi, ba zamu samu ba sakamakon mun mutu, babu mu a duniyar. Don haka ki ji tsoron Allah, kada na kara jin kin yi orafi akan abinda ya shafi bautar Allah." Mami ke wannan bayanin tana daga tsaye jikin kujera, sam basu da masaniyar fitowarta daga kicin. Cikinta an watanni shida da satittika ya fito sosai hakanan gaba aya ta rame ta ara haske sosai. Tuni jikinsu ya yi sanyi. "In sha Allah ba zan ara ba Mami. Astagfirullah." Mamin ta gya a kai gami da murmusawa. "Yauwa ko kefa." Ta yi murmushi itama san nan suka ci gaba da aikin. Sun shiga azumi da kwanaki goma, Zeenat ta wuce Kaduna gidan mahaifiyarta hutu. Sai ya kasance daga Kurfi sai Maminta da Abba a angarensu. Wannan ya ara sanyawa Kurfi buri da son ganin Maminta ta haihu. Ranar wata juma'a tun karfe biyun rana azumi ya soma ko a Kurfi, dukkanin wa anda ta yi bai bata wuyar wannan ba. Ga dai hadari a garin amman hakan bai hana zafi ba sosai a garin. Ana yin la'asar kuwa garin ya ara turni ewa sai kuma lokacin ne iska ta soma gudana cikin ikon Ubangiji. Mi ewa tayi daga hanyar shiga kicin inda ta yi rashe-rashe sai dai ta yanka abinda za ta yanka ko kuma ta are tafarnuwa daga nan zaune, bayan ta gaji ne tayi kwanciyarta. Ganin ta na okarin zura takalmin fatarta mai laushi ya sanya Baba Asma'u tambayarta. "Sai ina kuma?" Tayi dariya don tana jin kamar ta buga tsalle don murnar ganin yanda garin ya kacame da hadari ga iska mai da "Kinsan fa wannan season din namu ne." Dariya Baba Asma'u tayi. Mami ta amshe. "Love season ko? Ai ke har yau ba ki kawowa Babartaki suruki ba." Ta turo baki ta wuce da gudunta don gujewa maganar. Bata tsaya ko'ina ba sai garden insu, ba ta kai ga arasawa ciki ba ta soma jin tashin karatun Alkur'ani mai girma cikin wata zazza ar murya mai taushi na fitowa ta cikin garden in. A hankali ta ke tafiya har ta arasa sai dai bata shiga sosai ba. Sanye yake da bakar jallabiya. Ya dora tafin afa aya daman kujerar lilon yayinda guda aya ke ajiye a asa. Kansa na jingine jikin kujerar ya wani lumshe idanu yana
Chapter 13 · 0% Book details