← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 41

Sashe 7

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ita, Aliyu ne basu fiye d'asawa ba domin duk abinda uwarsa ke so to fa yana bayanta. Yanzun ma su Aliyu ta je kira don su fito su wuce islamiyya gudun kada su yi latti. Sai da ta soma shiga dakin Ummi ta yiwa su Batuul magana san nan ta nufi dakin Umma. Da sallamarta ta shiga, Umma na ji ta watsamata wani kallon raini kafin ta kauda kai ta amsa. 'Bak'in hali irin na d'anta.' Ta fadi a zuciyarta, a fili kuwa har da dan murmushi saman fuskarta ta karasa ta durkusa gabanta. "Umma ina wuni." Ta na kallonta kasa-kasa ta gyada kai batare da ta amsa ba. Itama bata damu ba ta maida hankali ga Aliyu wanda ke zaune ko shirin makarantar bai yi ba. "Aliyu ka.." "Ke!" Ta ji an dakamata tsawa. Ta dubi Umma da sauri. "Don uwarki da ubanki bai girmeki bane? Ko sa'anki ne da za ki kira sunansa muraran babu girmamawa?" Kurfi ranta ya 6aci, gani take ai ko su Faruk basu kiran Aliyun da Yaya ballantana ita, ta dai hadiye ta ce. "Ki yi hakuri Umma, mantawa nayi." Harara ta narkamata. "Shegen hali irin na uwarki za ki nunamin, munafukan kawai." Kurfi fa an kaita banko, don haka ta dubeta idanu cike da ruwan kwalla. "Kiyi hakuri Umma, amman wallahi Mami ba munafuka bace." Kallon mamaki suka ta watsamata. Saukar marin da Aliyu wa watsawa Kurfi shi ya maido Umma cikin tunaninta. "Da uwar tawa za ki ja har kina kiranta munafuka?!" Bai barta haka ba sai da ya hada da duka karshe ya tunkudata waje. Kurfi bata fasa kiran Maminta ba munafuka bace. Tana yi tana kuka. Haka Raliya ta fito ta riskesu daidai sadda Umma ke fadin. "Yauwa gadanga, yi min raga-raga da 'yar iska. Fasamin bakin shegiya." Ai kuwa ya k'ara k'aimi wajen kaiwa bakin bugu. "Ya Salam, haba Umman Yaya, me ya yi zafi haka?" Wani banzan kallo ta watsamata. "Idon matambayi, ba ruwanki da harkata! Idan ma ku ku ka zugota ta shigo ta yimin rashin kunya toh wallahi daidai nake da ku. Yarinyar da na kusa yin jika da ita ce za ta tsaya gayamin bakar magana. Don ubanta wa take nufi da munafuncin? Dadin ka haifa kenan, ba za'a zageka su kyale ba!" Ta karasa lokacin da Aliyu ke kai mata wani bugun. Cikin karaji ta kara magana. "Bazan daina fadaba, na fada! Na fada." Nan da nan aka taru a sashen. Mami jin ance Laila ake duka ya sanya ta zuwa sashen, kallonsu tayi a sukwane, bata nemi ba'asi ba ta durkusa ta kama hannun diyarta. Duban Aliyu ta yi, kwarjinin matar ya sanya shi jin zuciyarsa tayi wani irin tsinkewa. Ya waske kawai ya ja baya ya koma daki. Muryar Umma ta katse shirun da tambayoyin da wasu ke jifan Laila da shi. "Yau ni Laila za ta kira da munafuka! Dakyau! Abinda ta tsotsa ne daga Safiya take fesarwa yanzu. Dadin ka haifa kenan, an min maganin shegiya." Mami ta dubeta da murmushi. "Kiyi hakuri, in sha Allah zan yi maganin abin." Ta dubi Kurfi wacce jikinta ya yi ru6u-ru6u tsabar buguwa. "Bata hakuri." Ta dubi idanun mahaifiyarta, bata ta6a musamata ba. Dole ta juya ta durkusa ta hau magana ba don taso ba. "Kiyi hakuri Umma." "Ai ni an gama biyana kuma, hakurin a rike bana so." Mami ta jinjina kai ta ja hannun diyarta dake takawa dakyar suka bar sashen, makarantar da bata je ba kenan. Masu tausayinsu nayi, masu farinciki nayi. duk batasan wainar da ake toyawa ba. Suna shiga sashensu Mami ta zaunar da ita, Zeenat kam kukan tausayi ya hanata magana, duk yanda Mami tayi da ita ta wuce su tafi makaranta itama ta ce babu inda za ta je. Tun tasowarsu ba'a ta6a yiwa Kurfi irin wannan dukan ba. Gidan ma ba'a duka sai abin ya ci tura. Kurfi ta dubi Mami wacce ke gogemata inda aka fasa a bakinta, ta rike hannun Mamin. "Wallahil azim ban kirata munafuka ba Mami, bari ki ji abinda ya faru." Nan ta labarta mata komai, iyakar abinda akai kenan. Tausayi ya sanya Mamin jan kafadunta ta rungume. Shiru itama Mamin tayi na mintuna kafin ta dago ta dubeta jin ta yi shiru sai shesshek'a. "Ba ki yi laifi ba, daidai gwargwado nasan tarbiyyar da muka ba ki Laila. Nasan ba za ki ta6a kiran Hajiya Saudatu munafuka ba. Ki yi hakuri, mai hakuri yana tare da Allah." Daga nan ta sanyata ta yi wanka ta shafemata jikin da man zafi, ta bata maganin ciwon kai, ba jimawa bacci mai nauyi ya kwasheta. Mami ta zubamata idanu cike da tausayi, kan ta shiga shafawa tana zubda ruwan hawaye. Dayan hannun a saman cikinta. Tausayi take ji, jikinta na bata abubuwa da yawa game da rayuwarta, gaba daya diyarta shekarunta goma sha shida, batasan mene tanadin rayuwarta ba, Allah kadai Yasan gawar fari amman ba ta kaunar ta mutu ta bar diyarta ba tare da ta aurar da ita ba. Ta shagala da tunani bata ji sallamarsa ba sai da ta ji ya sanya hannun shima saman cikinnata. Kallonta yake cike da tuhuma, itama ta dubeshi kafin tayi hanzarin janye hannunta, duk da haka bai dauke nasa saman cikin ba. Ya gane komai ya fahimci damuwarta tun daga jiya zuwa yau. Ta gane yasan komai, ta gane babu kuma sauran abinda ya rage da zata 6oyemishi. Hakan ne yasa ta zame hannunsa a kasalance ta fita daga dakin. Ya dubi diyarsa cike da tausayin wannan abu da akai mata, daga bayanin da Zeenat tayi mishi ya fahimci sam ba laifinta bane, a halayyarta bata iya jurar a gayawa iyayenta bak'ar magana komai kankatarsa, haka take tun tana k'arama. Ya fice ya rufemata dakin. A dakinta ya risketa tana kokarin jera kayan guga a sif. Ya dakatar da ita ta hanyar juyowa da ita gareshi. Ta dubeshi , zaunar da ita ya yi gefen gado ya dubeta cike da damuwa. "Haba Noor, yanzu a duniya za ki iya 6oyemin cewar kina da ciki? Kin kyautamin kenan? Kin fa sani cikinnan barazana ce ga lafiyarki, har ki yi shiru ki zauna da shi? To ba zan lamunta ba, tashi muje asibiti dole a rabaki da shi a yau." Ya karashe cike da tashin hankali. Girgiza masa kai tayi gami da riko hannunsa tana kuka. "Aa, ka taimaka kada ka rabani da babyna, ina son abina. Domin girman Allah ka barmin d'ana. Ka manta Allah ne Mai kashewa da rayawa? Babu abinda zai sameni da yardar Allah lafiya kalau zan haihu." Abba ya kasa yarda da zancenta, ta ja ya ja, karshe ta hau magiya da rok'onsa Allah da ManzonSa s.a.w. Dole ya hakura amman bisa sharadin zasu je asibitin domin a dubata. Tayi na'am da hakan. Daga nan suka tattauna game da abinda ya faru a yau din ga Laila. "Bansan ya zan 6ullowa al'amarin ba, ina tsoron abubuwa da yawa, ina tausayawa Laila anan gaba." Fadin Mami cikin karaya. Abba ya daure fuska. "Kinga za ki sanyani cikin wani yanayi idan kina magana haka. In sha Allahu lafiya lau za ki haihu. Ke tashi ma ki shirya yanzu zamu wuce asibitin." Ta gyada kai tana murmushinta na sabo san nan ta dauki hijab dinta, sai ta k'ara dakin Kurfi, baccinta take shak'a kana gani kuma kasan na wahala ne, ta kada kai kawai kafin ta fita, sai da ta yiwa Zeenat sallama san nan ta bi bayan Abba. Karshe ya ce zai je ya samu Baba Hamza su yi maganar. A karshe ya ba Hajiyar hakuri koda ba haka din bane. *** A bakin Munira yake jin komai, shigowarsa gidan ya tarar ana ta tattauna magana tsakanin ma'aikatansu mata. Jin abin ya yi gingim a kansa, yana da tabbacin Laila ba zata aikata hakan ba. Gama sauraron bayanin ya ba Munira umarnin tafiya. Bayan fitarta ya yi alwala ya nufi masallaci, ana idar da Sallar Magrib ya nufi sashen Abba. Zeenat ya tarar a falo, ta gaisheshi a ladabce, ya tambayi Mami ta sanarmasa sun fita da Abba. Zagayawa ya yi ya zauna saman kujerar, duban Zeenat ya yi fuska ba walwala. "Uhum, meyafaru ne a gidannan?" Nan ta labartamasa komai har da abinda Kurfi ta cewa Mami. Yana gama sauraro ya tambayi inda Kurfin take, ta nunamasa hanyar daki. Kai tsaye ya mike ya shiga da sallama, jin ba'a amsa bane ya sanyashi shiga. Juyi ya tarar tana yi hannunta akan cikinta tana ambaton wayyo a sannu-sannu. Ganinta dishi-dishi bata san ma waye a kofar ba, hannu kawai take mik'awa cikin tsananin bukatar taimako. Da hanzari ya karasa ya rik'ota. "Marata, zan mutu." Ya kwalawa Zeenat kira, da sauri ta shigo. Ita kanta ta razana da ganin halin da Kurfi ke ciki. "Ke haka ake yi a barki da yarinya ki kyaleta ita daya?" Ya karashe da guntun tsaki. Waya ya zaro ya danna kira ga Family Doctor dinsu, kasancewar ta san matsalar Kurfi na ciwon mara yayin period ya sanya ta fadamasa maganin da za'a siyo daga karshe su ka yi sallama. Umarni ya ba Zeenat na kada ta bar inda ta ke san nan ya fita. Can sai ya shigo rike da maganin ya ajiye gami da ba Zeenat umarnin ta bata. Ya lura da yanda jikinta ya yi ru6u-ru6u da shatin duka, ransa ya kara 6aci. Aliyu hauka ya yi ba kuma zai kyaleshi ba. "Ki tabbatar ta sha, kada ki kara yin nisa da dakin." Ta amsa da toh, shi kuwa ya fice. Kurfi ta dubi Zeenat hawaye na zuba a idanunta. "Zeenat meyasa Umma ta tsani Mamina wai? Na rasa dalilin wannan tsana, Mamina ake kira munafuka." Hannu ta sanya ta rufemata bakin. "Haba Kurfi, maganar ta wuce ko? Kada ki kara yinta don Allah, ki ji da lafiyarki ma. Sannu kin ji." Ta maida idanunta ta lumshe, har lokacin bata bar zubda hawaye ba. Yana daga kofar, ya ji duk abinda ta ce, jikinsa ya kara sanyi, tausayinsu ya kara yawaita a ransa. Ajiyar zuciya ya ja san nan ya karasa ficewa. *** Da mamaki Baba Hamza ke kallon Hajiya Saudatu yana sauraron dukkan bayananta, sai kuma ya girgiza kai. "Kayya, Laila ba zata ta6a aikata wannan wautar ga ya'yanki ba balle kuma ke
Chapter 7 · 0% Book details