Sashe 23
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saudatu! Ki kiyayeni, masu ku i fa ba wawaye bane, ina ankare da duk wani takunki." Daga haka ya mi e ya barta zaune tana binsa da kallo kamar wata wawuya. Gaba aya sai ta sha jinin jikinta ganin babu alamun wasa a duk furucinsa, tabbas zai iya aikata duk abinda ya fa i. Gwara ta fasa batun saki ta nemi dai wata mafitar. Daga nan ta sa a ta shiga wanka, shi kuwa Shafa'i da Wutri ya tayar. *** Washegari da misalin arfe biyar ya kama lokacin da za'a kai Amare gidajensu, kowaccensu ta ci kuka har ta oshi. Kurfi koda aka kai ta ga Abbanta, fita akai aka basu wuri. Da zolaya ya soma. "Ah ah, yau Laila ta samu Majnun in da Babanta Hamza ke yawan fa i ko?" Ta tur une fuska sai kuma kukanta ya dawo sabo fil. "A'a, yau kam dole ki yi kuka. Aure ba abin wasa bane Laila. Ki yi ha uri, ki koyi ha uri a zamantakewar aurenki, ki kasance mai koyi da iyar Ma'aiki s.a.w a rayuwar gidan miji. Ke ba kowa bace, kuma ba ar kowa ba, ki zubar da duk makamanki ki fuskanci ibada gadan-gadan. Miji da kike gani, ya wuce duk inda kike tunaninsa, ki bar ganin Khalid a yayanki, yanzu ya haura matsayin da babu wanda ya kai shi a wurinki. Zan iya umarnin ki zo gidannan, idan Khalid ya hana ban isa ba. Zan iya wanciya rashin lafiya, idan mijinki ya ce ba za ki fito ki duba ni ba nan ma ba ki isa ba duk dai nasan kin sani, kin je Islamiyya, an kuma koyar da ke abubuwa da dana game da aure kamar yanda ki ka gani daga iyayenki." Shiru ya an biyo baya kafin Abba ya ora. "Ki ji tsoron Allah ki bi mijinki da zuciya aya, ki mishi biyayya tsakaninki da Mahaliccinki. Kar ki tauyeshi ta ko'ina, kar kuma ki zama mai juyamasa baya kamar yanda Allah da ManzonSa (s.a.w) su kai hani. Wallahi idan kina etare dukkan wani umarninsa to fa ki sani Laila, ni AbdulHamid gobe iyama bani da abinda zan iya yi domin cetonki daga azabar Ubangijinki, hakanan Mahaifiyarki. Mijinki sai ya aga afa san nan za ki shiga aljanna. Kinga Maminki? Shekarunmu ashirin da wani abu, ban ta a kai ararta ba koda sau aya kuwa. Tun mahaifanta na raye bani da matsala da ita, mace ce mai kyawun halaye, tana biyayya gareni, tana kyautatamin, tana gudun acin raina ko yaya ne, wannan ya sa muka samu fahimtar juna da ita. Muka samu daidaito a zamantakewa. Ki yi ha uri ki bi mijinki, ki yarda da komai *MU ADDARI* ne, kamar rubutu ne akan dutse, kinga kuwa har abada ba zai gogu ba sai idan ayanmu ya mutu." Abba ya yi maganganu sosai masu ratsa zuciya tun bata iya magana dai kuka har ta soma neman gafararsa gami da ro on ya tayata addu'a ta zama cikin matan aljanna masu biyayya ga mazajensu. Murmushi ya yi ya ce ya yafemata duniya da lahira, arshe ya bata Alkur'ani Mai Tsarki. "Babu maganin da babu a cikinsa Laila, shi ka ai ya wadatar da ke." Ta rungume tana mai jin sanyi a zuciyarta. Lokaci na cika aka mi a ta gidan mijinta da ke can Sardauna's Crescent, yayinda Zeenat ta ke wuraren Zoo road. Sauran ma dai daga ta cikin gari sai ta orayi, kusan dai Kurfin ma ta fisu kusa da gida. Har aka kaita bata bar kuka ba, gidan sama da asa ne, a saman aka zuba mata kayan aki da sauran kyale-kyale hakanan shima asan falo ne na gani na fa a. Tana ji su Tasleem na i rarin ba wanda zai tsaya siyan baki saboda gudun halin Yaya Khalid. Kuka da magiya gami da ru ume an uwa, babu wanda Kurfi bata yi ba sai dai ba wanda ya saurareta haka suka tattara suka watse. Wannan na aya daga abinda ya aramata takaici. Haka ta zauna shiru, can kuma dabara ta fa omata, kafin ya zo ya bata kunya gwara ita ta soma nuna mishi bata damu da shi ba, don haka sai ta nufi ofar za ta sanya mu ulli. Nasihar Abbanta da iyayenta mata ya fa omata a rai, a sanyaye ta fasa ta koma ta ara dun ulewa tana kuka bata ko damu da kanta da ke azababban ciwo ba. Tana a haka ta ji an turo ofar akin an shigo, sallamarsa ta ratsa kunnuwanta, ta mi e zaune a hankali tana ara rufe jikinta da mayafi, a sannu ta amsa don idan ba'a nutsu ba lallai ba a ji. Bata ago kai ba ballantana ta kalleshi, ta dai san wurinta ya nufo. Zama ya yi a gefen gadon, shiru ya ratsa akin, jin shirun ya yi yawa ne ya sanyata agowa ta kalleshi da jajayen idanunta wa anda kuka da ciwon kai su ka kara antar da su. Shi in ma ita ya ke kallo a lokacin. aure fuska. "Ba ki da lafiya ne?" Ta ga dai idan ta yi shiru za ta cuci kanta, kawai sai ta gya a kai. "Eh, kaina ke ciwo." Ta fa i da sha iyar murya. Gani kawai ta yi ya mi e ya hau duba jakarta arama da aka ha ota da shi. Sai lokacin ta are mishi kallo a sace. Maroon shadda ce ya sanya har da babbar riga. Ta hau sosai da farar fatarsa ta yi kyau, agogo kalar azurfa ne a hannunsa sai kuwa zobunansa na azurfa da su ka ha u da ananun gashi gashin da ke a can arshen yatsunsa. Ta kauda kai, duk wannan kumburin da shima ya ke yi don an auramasa ma iyiyarsa ne kenan. Ta lumshe ido ka an. Ko ba komai dai itama ai bata sonsa. Shi kuwa a nasa angaren kallon irin kayan da aka ha ota da su kawai ya ke, abin ya so ba shi dariya ganin har da wata shegiyar rigar bacci duk kuwa da bai aga ba ya san irinta . Allah Ya taimakeshi ya ga abinda ya ke nema in domin kuwa dama tun kan shigowarsa Anti Rumaisa ta kira ta ke mishi batun bata samu Laila a waya ba, amman ya duba jakarta akwai magungunanta ta sha su. Shi sai ma a lokacin yasan ta mallaki wata wayar. Ya maida komai yanda ya ganshi san nan ya dawo ya ajiye ledar magungunan a gefenta ya fita. Jimawa ka an sai ga shi ya dawo da wata leda fara babba sai kofi a hannunsa, ajiyewa ya yi saman an centre table in da ke tsakiyar akin. Sai da ya koma ya auko faranti san nan ya bu e ledar. Kaza ce gasashshiya, ya juye a farantin ya bata umarnin ta ci. Farko ta yi gardama sai da ta ga ba wasa a tattare da shi fiye da koyaushe san nan ta soma ci. Bayan ta kammala ya bu e ya ciro ruwa na roba ya tsiyaya ya mi amata. Kasancewar ba wani kallonsa ta ke ba, ya sanya maimakon ri e kofin ta ri e tattausan hannunsa. Sai kuma ta saki da saurinta, ya diremata kofin saman tebur, maganin ya alo wa anda ya kamata ta sha a ranar ya mi amata. "Ki sha sai ki kwanta, sai da safe." in haka keda wuya, ya juya abinsa ya bar akin. Idan ta ce ba ta ji da in fitarsa ba to dagaske ta yi karya, a gurguje ta mi e ta rufe akin, Allah Shaida ba ta son shan maganin domin kuwa ba sa shiri, amman hakanan ta daure dakyar sakamakon ciwon da ta ke ji, ita a duniya duk abinda ya shafi allura da magani ba ta so sai don dole. ai a san nan ne kuma ta rage kayan jikinta, koda ta duba jakar don ta sauya, ta yi mamakin ganin ingilar rigar da aka ha ota da shi. Riga ce mai hawa biyu amman daga ta wajen har ta cikin kamar abin tatar koko, sai aramin pant siriri da taho da rigar. Takaici ya cikata musamman da ta tuna Yaya Khalid ya gani, Allah ma ka ai ya san me zai ce a ransa. Don tsabar ba in ciki sai kawai ruwan hawaye ta ji ya zubomata, ta tabbatar wannan aikin sai dai su Anti Fahima. Ta ja tsaki gami da ara aga kayan, Allah kuwa sai ya taimaketa ta tsinto wata doguwar rigar cotton ja mai ba i layi-layi na ba i. Ta fiddoshi gami da cire an katin da ke jiki na sabon kaya ta ware ta sanya. Hula aya ta auka cikin ukun da aka sanyamata ta rufe kanta. Bayan ta kammala ta ora alwala a daddafe ta gabatar da shaf'i da wutri, ta yiwa Mahaifiyarta addu'a kamar koyaushe sai mahaifinta da malamai da kuma an uwa musulmi gaba aya. Cikin ikon Allah da ta samu ta kwanta saman gado, bata wani tsaya tunane-tunane ba kamar yanda ta saba a kwanakin aurennan, bacci mai cike da ni'ima ya yi awon gaba da ita. To shi inma ba wani zama ya yi ba, yana kammala dukkan al'adunsa na bacci ya kwanta don ba aramin gajiya da kujiba-kujiba ya yi ba a an kwanakinnan. *** Cikin bacci ta ji ana bugun ofar akin, kusan a firgice ta mi e sai kuma ta ambaci Allah. Zama ta yi dirshan a kan gadon ta na waige-waige. Sai lokacin ta tuna a inda ta kwana. Jin an ara buga ofar ya sanya ta mi ewa, hijab ta zura kafin ta isa ga ofar ta bu Yaya Khalid ta gani cikin farar jallabiya. "Sallah." Ta amsa da toh san nan ya juya ya tafi ta maida ta rufe sai dai wannan karon ba ta sanya mu ulli ba. Ko da ta idar gado ta haye sai bacci. Cikin baccin ta ji ana kiran sunanta a hankali. Ta bu e idanun, ta soma mi a ta yi ido hu u da shi da saurinta ta bari ba tare da shiri ba. Ya an yamutsa fuska don bai gane komai ba. "Ki tashi haka ki fito ki karya." Gya a kai ta yi ta bi shi da kallo har ya fice, ita fa har yanzu takan yi mamakin kasancewarsa