← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 41

Sashe 8

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kanki. Haba Saudatu, ke kenan idan zuciyarki ta tsani mutum ba za ta iya tankwaruwa ta dawo ta kaunace shi ba? Wannan ai rashin hankali ne ku ka aikata daga ke har shi Aliyun!" Harararsa ta shiga yi. "Kana nufin karya nake yi mata? Eh ai dama na tabbatar har yanzu soyayyar Bara'atu na nan k'ok'on zuciyarka. Shiyasa duk wanda ya ra6eta kake sonsa! To naji karya nake mata, sai ka dauki matakin dukan a kaina!" Ran Baba Hamza ya 6aci, ba ya daukar raini a wajen mace. A fusace ya soma magana. "Ke shashashar ina ce da za ki dunga had'ani da iyalin wani? Idan ke bakisan ciwon kanki ba ni na san nawa! Laifi ne kun yi ke da danki, idan ma ke kika zugashi ya aikata to kuwa wallahi kin ji na rantse Aliyu ya fasa zuwa Malaysia karatu, nan din dai da sauran yan uwansa suka yi shima anan zai yi." Shi kuwa Khalid yana shigowa falon Umma ya ci karo da Aliyu tare da su Hafsat ana kallo. Belt din jeans dinsa ya zaro a yayinda ya nufeshi gadan-gadan. Bai yi wata-wata ba ya saukemishi a gadon baya. Ihun da Aliyu ya sanya gami da zaburar da ya yi shi ya janyo hankulan su Hafsat har ma da iyayen da ke rikici a daya falon. Khalid dukan yake babu ji babu gani, a haka Baba Hamza da Umma suka shigo. Baba Hamza abin ya mishi kyau domin ko babu komai gobe ba zai kara gangancin dukan diyar mutane ba. Umma kuwa a rude ta karasa ga Khalid, hannunsa ta rike. "Ba ka da hankali?! Ko dai ka sha wani abu ne?!! Dan uwannaka za ka daka saboda ka je an shiryamaka karya da gaskiya ki? To na rantse da Allah zan sa6amaka yanzun nan." Kallo daya Khalid ya yiwa su Hafsa, sum-sun kowaccensu ta mike ta fice. Takaicinsu bai wuce na jin duk akan Kurfi ake wannan budurin ba. "Haba Umma, yanzu ko min girman laifin da Laila ta yi ai bai kamata yaronnan ya farfasamata jiki ba ballantana ma nasan ba zata aikata..." Shiru ya yi sakamakon hannun da ya ga Daddy ya dagamishi. Wannan ya bata damar ci gaba da magana. "Wa? Ai ni na gama sanin an rabani da kai! An mallakeka har ba ka ta6a ganin hawayena sai dai ka ga na mak'iyana ka sharemusu! Dukan da kai mishi kuma ka je..." "Hajiya Saudatu!" Tsawan da Baba Hamza ya bugamata ne ya sanyata yin shiru, karshe ta fice zuwa dakinta. Shi kuwa ya numfasa rai a matukar yace, karshe shima ya koma nasa sashen. A haka kowa ya kama gabansa rai babu dadi. Shi Khalid gaba daya ma ficewa ya yi daga gidan, dama kiran Baba Hamzan ya kawoshi, yasan maganar bai wuce aure shi kam bai kara takowa gidan ma sai nan da watanni. Zai ci gaba da maida hankali a aikinsa kawai. Mami kuwa sun je wurin Dr Arfat inda ta kara basu tabbacin matukar Mami ta kiyaye dokokin asibiti da yardar Allah lafiya lau za ta haihu, ta kuma kiyayi dukkan abinda zai sanyata damuwa ko yaya ne. A haka suka rabu cikin aminci. Washegari Kurfi ke jin labarin abinda ya faru a sashen Baba Hamza a bakin Munira, karo na farko a tarihin rayuwarta da Yaya Khalid ya burgeta. Ko ba komai ya ramamata, wan nan yasa ta ji zuciyarta ta wanku fes. *** A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, har bai fi sati biyu a soma bikin jikokin Alhaji Khalid Khalil Kurfi ba. A wannan lokacin ne ta had'a meeting inda a rana ta farko ta soma da gaba daya zuri'ar gidan idan ka cire Adda Maijidda da ke a nesa. Su Kurfi duk su na zaune sun yi jugum jugum, cikin kus-kus ta yiwa Zeenat rad'a. "Na fadamaki yau za ta had'aki da Yaya Khalid. Shikenan kin huta da ciwon zuciya." Wani murmushi Zeenat tayi, a kasan ranta tana adduar Allah Ya tabbatar da hakan. Kowacce cikin yanmatan gidan burinta ace ita zaa hada da Khalid. Shi kuwa gogan yana hakimce saman kafet a gefen tagwaye. Manyan iyayen suna saman kujeru, Baba Hamza ya bude da addu'a san nan ta soma magana. "Alhamdulillah da Allah Ya kara bamu aron rai da lafiyar da har muka ga wannan rana da muka kara haduwa domin abinda ya danganci zumunci da kuma kauna ta yan uwantaka." Daga nan ta ci gaba da jawabi inda ta bayyana farin cikinta ta hanyar godiya ga Allah bisa bukukuwan da Ya kaddara za'ayi a gidan, ta kuma yi fatan samun abokan zama nagari ga 'yan baya. Karshe ta gangara kan batun Khalid. Anan ta ce ta ba shi wata daya kacal don ya tsaida matar da ya za6a daga cikin yan uwansa, acewarta bikin magaji bai hana na magajiya, don ya rasa Sumayya ba kuma zai yiwu su zubamasa ido ya yi ta rayuwa hakanan ba abokiyar zama ba. Ta kara da cewa. "Bayan nan ina kara jaddadamaku, ku matan, ni ban hana kowaccenku ta yi karatu ba sai dai ku sani da zarar fa miji ya fito za'a aurar da ke ki ci gaba a dakin mijinki. Wannan kuma bai zamo dalilin da za ku yi abinda ku ka ga dama ba, idonmu na kanku, idan mun lura da takunku ba mai kyau bane, toh fa zamu dakatar da wani batun karatu mu aurar da ku ga wanda muka ga ya dace matukar ya kwanta maku." Ta karashe da addu'a kafin ta dubi yaranta ko su na da abin cewa. Baba Hamza dai ya tofa albarkacin bakinsa inda ya kara nusar da su muhimmancin zumunci da kuma illar barinsa kafin Baba Mudassir shima ya dan tofa a karshe ta sallami jikokin ta shiga meeting da yaranta. Tun a hanya su Hafsat suka hau addu'ar Allah Yasa Yaya Khalid ya za6esu. Ita dai Zeenat ba magana domin daga yanayin fuskar Khalid ta fahimci ba lallai ya za6i ko daya cikinsu ba. To su kansu sai da suka tattauna kan yanda ya daure fuska idanunsa suka kada sai dai bai ce komai ba. Kurfi kuwa suna tafe tana jan tsaki da mita. "Aikin banza, ji don Allah yanda duk suka rude akan wani Yaya Khalid, ni wallahi kamar na shak'esu haka nake ji, ke ni bana ma so ki aureshi, ki ma cireshi a ranki don wallahi yanda ya hade rai to cin fuskar mutane zai yi. Ke banda ma abinki me za ki yi da wannan mai shegen bak'in halin? Ai wallahi Zeenat kin fi karfin ajinsa, ji yanda Yaya Zahraddeen ke masifar sonki amman kin i sauraronsa, shima da zai san akan wanda kike insa sai ya ji tamkar ya sha eki ." Ita dai Zeenat bata ce komai ba banda murmushi da tayi. Ita kuwa Kurfi sai tsaki da ci gaba da mita kawai take, haka har suka iso bangarensh. Shigarsu ba jimawa sai ga su Madina diyar Adda Fatima da Rahila diyar Adda Salamatu sun shigo. Nan suka hadu su ka yi ta hirar Yaya Khalid, dama suma tasu bata zo daya da shi ba don ba ya ragawa kowannensu, kasancewar sukan zo hutu sun san halinsa sarai. Nan suka yiwa Zeenat caa, Kurfi tana kusheshi suna tayata. Wani abin su yi dariya wani kuwa takaici ya ishesu. "Ke wai baki ga yanda Rukayya da Hafsat suka kusan dambatawa ba? Tab, ai ni na sha kallo bayan tafiyarku." Fadin Rahila kenan, gaba daya suka maida hankali kanta. "Meyafaru?" "Kayan haushi mana, suna shiga falon Mama Zahida Hafsat ta ce Ba abinda zai sa ta k'i aurensa, ta tabbatar ko bata za6eshi ba toh fa Hajiya za ta hadasu. Rukayya ta ce wallahi bata isa ba sai dai ita domin ita ta fi dacewa da shi. Ku tun fa nk da su Zee muna daukar abin wasa har muka gane da gaske suke abinsu. Kadan ya hana ayi dambe wallahi." Wata dariya suka kwashe da shi, Zeenat da itama jikinta ke a sanyaye, dariyar tayi. "Ai fa mun soma ganin drama kenan, hum! Sai addu'a kawai wallahi." Cewar Kurfi. Haka su ka ci gaba da gulmar masu sonsa a dangi, abin ya karawa Kurfi takaici, kamar wani dan gwal? Ko shi kadai ne namiji dai ai bin ya isa haka. Misalin karfe takwas na dare bayan kowa ya watse ya shiga falon mahaifiyartasa, tana zaune tana kallon talabijin, sallamarsa ya sanya ta kashe kara gaba daya ta amsa. Ya karaso ya zauna a kujerar kusa da ita yana dubanta fuskarsa babu walwala don tun sadda akai maganar ya ji komai na rashin matarsa ya dawo sabo a zuciyarsa. Ga ta hargitsa lissafinsa, me zai yi da yarannan? Kaf cikinsu bai ga wacce zai iya aura ba don babu wacce ba fitsararriya ba a cikinsu. "Tunanin me kake ina magana ka yi shiru?" Sai a san nan ya gane ya yi zurfi a tunani, ya dubeta. Ta hango damuwa karara a kwayar idanunsa, bata kaunar 6acin ran yaranta, don haka sai jikinta ya yi la'asar. "Kada fa ka sanya wata damuwa a zuciyarka, wannan ai ba abu ne da mutum zai damu ba. da gaskiyarta, kar ka manta fa gaba kake k'ara yi ba baya ba, girma dad'a kamaka yake amma ace a shekarunka ba ka ajiye iyali ba? Haba Babangida, ai kaima ka yiwa kanka fada." Shi dai bai ce komai ba saboda ba ya son ma maganar. Karshe ya waske da fadin. "Kin ce zamu yi magana." Gyada kai tayi. "Eh ai nima duk akan maganar ce nake so mu yi, gargadi ne zan maka akan wani abu guda." Kai kawai ya gyada yana dubanta. "Ban yarda ba, kuma kar ka fara za6ar abinda ya fito daga sashen Balarabe domin ba zan ta6a hada jini da su ba. Wannan shi ne iyakar abinda nake son fadamaka." Baba Hamza da ke tsaye a kofar duk ya ji maganganunta, ransa ba karamin 6aci ya yi ba, ya karasa shigowa ciki bayan ya yi sallama ciki-ciki tsabar ran babu dadi. Suka dubeshi, ita kanta Hajiya ta dan sha jinin jikinta don kuwa kallo daya ta fahimci ya ji maganarta. Shima Khalid da baisan ma me zai ce mata ba, ya gama fahimtar cewa Babannasa ya ji. Ya karaso ya
Chapter 8 · 0% Book details