← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 41

Sashe 29

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fita ba tare da ta damu da aukar jaka da takalmanta ba ta yi angaren Hajja. Hajja na kwance tana bacci ta fa a kanta cikin matsanancin kuka. Kusan a gigice ta farka tana mai dubanta. "Hajja ki tashi, Abbana ya haukace. Abbana ke kiran na je na zauna a sashin Hajiya. Hajja koda Abba ya bar sona nasan za ki yi mishi fa Hawaye kawai ke sharara daga idanun Hajjan amman fa ba motsi ballantana ta yi magana. A hankali ta ke bin ta da kallo daga sama har asa ya yin da le anta suka shiga ka awa tamkar mai rawar sanyi. "Laila." Ta ji an kira sunanta daga baya, ta juyo da sauri, Balaraba ce aya daga cikin hadiman Hajja. "Balaraba, meke faruwa a gidan nan wai?" Balaraba ta yafito ta da hannu alamar ta taso, ba musu ta tashi amman idanunta akan Hajja tana yi tana waige ga ruwan hawaye kwance saman fuskarta. Suka ja can gefen kicin, Balaraba ta share kwalla da gefen zani san nan ta soma magana. "Sharrin shai an ne da na Hajiya, shekaranjiya ina daga gefe ina damun furar Hajja, ta sanya na kira mata Alhaji Babba (Daddy) a waya ta kar a ta ce ya zo tana son ganinsa. Dama kuma tana ta mamakin yanda akai kwana biyu a yaranta ba wanda ya le o inda ta ke domin ya gaishe ta. Ba jimawa ya zo tare da Hajiya. Dama daga yanayin da Alhaji Babba ya shigo muka sha jinin jikinmu, gaba aya kamar wanda akai wa mutuwa ya murtuke fuske ita kuwa Hajiyar sai taunar cingam ta ke tana kallon Hajja ai. Akan maganar ku en da shi Alhajin ya saba bayarwa a kai can gida Kurfi ganin shi Kawu Bello ( an uwan Hajja) ya kira akan wa anda ake wa aiken su na da bu ata a taimaka. Toh fa sai Hajja ke mishi magana akan ya ara ma saboda yanzu akwai marayun da iyayensu sukai hatsari kwanaki, nasu kason ya fi na saura yawa. Nan ne Hajiya ta soma sababi, wai ai ku in ba daga sama ake musu ruwansu ba, su auyen basu san babu bane? To ba sisin Alhaji da zai fita akan wasu can cima zaune. Hajja ranta ya aci, ta ce ta rufe mata baki tunda ba da ita ta ke magana ba da anta ta ke. Bu ar bakin Alhajin sai ya rufe Hajja da fa a. Wai ai da gaskiyar Hajiya Sa'adatu, akan me za'a dunga tatsar shi sai ka ce Sa? Shi wallahi dama ya gaji da ciyar da attai ba gaira ba dalili, dukiya ai guminsa ne don haka su ma su tashi su nemi rabonsu. Hajja sakin baki kawai ta yi da mamaki arara saman fuskarta. Can kuma ta ce. "Yanzu Hamza ni ka ke gayawa wannan maganar?" Ya kuwa karya wuya ya ce. Eh, ai gaskiya ce kuma zai fa a ko a gaban waye idan ta kama. Da wannan suka bar mu baki bu e. Hajja ta yi salati ta sanar da Ubangiji, arshe tana hawaye ta ce na danna mata lambar Baba Mudassir da Abbanki. Na kuwa kira su aya bayan aya na sanar da su kiran Hajja don ita a sannan ma magana ta gagare ta. Ba jimawa suka hallara. Nan dai cikin hawaye ta kora musu bayani, amman abin mamaki Mudassir ne a zafafe ya soma mi ewa ya na mai jan guntun tsaki. Wai shi ya auka magana ce ta arziki, ya ce ai dama ya jima yana takaicin salwantar da dukiyar da ake kan wasu maciya tuwa da miyar kuka. Don haka abinda Alhaji Babba ya yi a wajensa daidai ne. Banda kwa ayi mene nasu na hangen dukiyar da ba tasu ba har ma da arin yin tuni idan ba'a aika ba? Daga haka bai ma tsaya saurarar komai ba ya fice, shi kuwa Abbanki bai ce uffan ba ya juya zai fita. Anan ne Hajja ta ce Kaima ka bi bayan an uwanka? Ya ce shi ba shi da ta cewa, duk abinda suka yanke daidai ne a wurinsa. Ke Laila ranar naga tashin hankali, Hajja kuka ni da su Lami kuka. Wallahi ranar baiwar Allahn nan sai ta ba ki tausayi, abinci wannan kasa ci ta yi, toh fa a wannan daren ni dai ba zan ce ga abinda ya faru ba, mun yi sallama da Hajja ta shiga makwanci, wayewar garin jiya sai shiga nayi na ganta yashe a asa cikin kashi da fitsa..." Kuka ya hana Balaraba arasawa, Kurfi da ke kuka ta ce. "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un, wai meke faruwa? Ni fa ban gane komai ba. Amman shi ne ba ku mi a ta asibiti ba?" Balaraba ta ja majina. "Sun i, na bi su na fa amusu amman ba wanda ya saurareni cikinsu. Maman Munira (Ummi) na son ta taimaka amman wallahi Alhaji ya ce muddin ta yi wani yun uri a bakin aurenta. Ni ban ma gane mata ba domin wallahi mugun tsoron Hajiya ta ke ji yanzu. Zan iya rantsuwa cewar Hajiya ce silar komai da ke faruwa a gidannan." Wai mafarki ta ke ko kuwa dai film ne ta ke kallo? Ita fa ba abinda ta ke fahimta, ta kasa gane komai. Daidai nan Lami ta shigo goye da Mu'azzam, ganin Kurfi sai ta arasa itama kawai sai ta sa kukan. "Laila ya muka ji da wannan sabuwar rayuwa?" Kurfi ta kasa magantuwa, wallahi har sannan ganin abun ta ke tamkar mafarki. Toh wai dama ana haka a rayuwa? Shigowar Aliyu ce ta katse hirar. Yana feeto kamar yanda ya saba, ganin su na koke-koke sai kawai ya tuntsire da dariya gami da yin as da hannu. "Ikon Allah, yau kuma duniyar baya ta juyamaku? Ah kaga su Balaraba da Lami, wato har da su kaza a cin danko? An zo gidan mutane an kanainaye ana cin arziki, to yanzu sai mu ga ta yanda za ku ara yin rawar gaban hantsi. Ke kuma ar taya era ari, ki zo inji Hajiya." Ya arashe gami da kanne mata ido aya kafin ya tuntsire da dariya ya juya ya bar wurin yana wa e-wa Durkushewa ta yi ta ara ri e kirjinta tana mai ambaton Allah, sanin da ta yi ba abinda ya fi arfinSa. Dakyar ta samu ta ji wani arfi ya zo mata ta mi e ta share fuskarta sannan ta doshi angaren Hajiya tana mai ci gaba da ambaton Allah a asan ranta. Har ta samu ta shiga da warinta. Sallama ta yi har sau uku babu amsa, ta le a kanta, ga mamakinta Hajiyar na hakimce cikin kujera ta na danne remote. Bayan ita babu kowa a falon sai kuwa akwatin kayanta da ta hanga a can gefe a yashe a asa. Ta ha iyi miyau mai aci kafin ta arasa shiga, babu wani tsoro ko fargaba a ranta, asalima sai ta ji kallon wata ba ar azzaluma ta ke mata. arasawa ta yi ta zauna asa kamar yanda ta saba yi a sashin. Ta gaishe ta dakyar. Daga yanda ta yi furucin ka san zuciyar a dake ta ke, ta shirya kar ar kowane irin sakamako. Hajiyar kanta yanayin yarinyar ya bata mamaki, ta riga da ta auka an wuce wurin. Ta yi zaton babu wata matsala da ta saura, sai dai a cikin idanun yarinyar har ma da kalamanta akwai wani irin oyayyen jarumta wanda ba lallai mai arancin tunani da hange ya ago ba a kallo aya. Ta daure firgicinta ta hanyar ara aure fuska. "Shi Khalid in bai fa a maki nan za ki sauka bane?" Ta yi shiru kanta a asa domin har ga Allah tsanarta ta ke ara ji, ta ji ma duk wani abu da ya dangance ta ba ta maraba da shi. "Habiba! Habiba!!" Da gudu ar aikinta ta fito tana mai amsawa. Ta dur usa. "Na'am ranki ya da "Ga ta nan ku je da ita angarenku, san nan kada inji ko na gani ayanku ya ba ta shimfi arsa. Ku bar ta ta gudanar da rayuwarta a tsakar akin. Ban yarda da ayanku ya kyautata mata ba koda kuwa na second aya ne. San nan ke kuma daga yau duk wani aiki da ya shafi na angaren nan, na dam a shi a hannunki don kuwa ba zan zauna da atuwar budurwa kamar ki da sunan wai matar ana ba, kuma na zuba maki ido ba aikin komai." Daga haka ta au waya ta hau latsawa. Aliyu ne ya shigo da saurinsa. "Hajiya, ga Yaya nan shigowa." Da sauri Hajiyar ta dubesu. "Maza tashi ki bita ku shiga ciki. Ga akwatinki ki auka." Yanda ta yi furucin da sauri sai ya ba Kurfi mamaki, ta mi e ta auki trolley in ta bi bayan Habiba. Sun kusa ficewa ta juyo, sai gadon bayansa ta gani yana amsa waya inda ya ke cewa na kan wayar yanzu zai koma ya shirya. Ta auke kanta ta ara aga afa don ba ta aunar ganin nasa. Komai yanzu ya fita a ranta, ta kasa fahimtar kanta. Rayuwarta ta koma wata sabuwa. Bayan shigarsu ta mi e ta bi ta ofar baya zuwa angaren Abbanta. So take ta ara tabbatar wa kanta abinda ya faru tsakaninta da Mahaifinta. So ta ke ta ga ko zai yarda ya yi mata kallon rahma yanzun. Sai dai tana tura ofar falon ta ga ba ya nan, kiraye-kirayen sallar Magrib ne ya bata tabbacin wata il yana shirye-shiryen sallar. Ta arasa inda ta ga tulin iv cards ta au guda aya tana dubawa. "Ya Rabb, Allahumma ajirni fi musabatii." Sai wani sabon shafin kukan ya alle, Abba anwar Hajiya zai aura? Ita kuwa ta san Anti Luba, anwa ce ga Hajiya wacce ta doshi shekaru arba'in amman ko auren fari ba ta yi ba, shekarunta kusan ashirin da uku a Saudia. Gogaggiyar ar duniya. "Dole na au mataki." Ta ja jakarta da ta bari anan da takalmi ta fice. Tana shiga angaren su Habiba ta ciro waya, ita ba ta ma da nutsuwar wani tsayawa kallon makwancin da sauransu. Kiran Adda Fatima da sauran yaran Hajja matan ta yi niyyar yi, sai dai kuma idanun dattijuwa Habiba da Lauratu suka hana ta aiwatar
Chapter 29 · 0% Book details