Sashe 27
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na hango kalar damuwarsa tattare da ita. Abu aya kawai ya ri e da zai iya kare kansa da shi. Wato a dalilin Maminta da amanar da ta bar mishi nata ne ya ke janyo mishi tausayinta da son kyautata mata ko yaya. Wannan ya ri a a matsayin hujja ba wai wani abin daban ba. Ya au saura a sa e-sa en zuciya. Mi ewa ya yi sannan ya amsa. "Amin, na gode sosai." Sannan ya fice ita kuwa ta bi bayansa da kallo. Sai da ya fita da mintuna kafin ta jawo wayar, balance ta duba ta ga kati har na dubu biyar ya sanya mata, ta yi dialing lambar Tasleem da ta ri e a kanta don ba ta kai ga zaman yin copy ba. Sai da ta kusan yankewa kafin Tasleem ta aga. "Assalamu Alaikum." Fa in Tasleem. Itama ta amsa kafin Tasleem ta ce. "Wa ke magana please?" Murmushin mugunta Kurfi ta yi don kawai sai ta ji ta na son tsokanarta hakan yasa ta ara yin asa da muryarta wadda a sanadin kuka ta an sha "Ai bai zama lallai sai kin sani ba, abu aya nake so da ke. Ki saurare ni sosai ki kuma fahimce ni." Tasleem ta an yi shiru daga angarenta. Sai kuma ta ora da fa "Ikon Allah, toh ina jinki." Dariya ta so su ucewa Kurfi ganin yanda muryar Tasleem ke an rawa. "Ki fita a hanyar mijina, ki nisanta kanki da zuciyarki daga gareshi domin idan ki ka ci gaba da amsa kiran wayarsa ko hira da shi ta chat abin ba zai kyau ba." "Wane mijin kenan? Malama ni ban san me kike nufi ba kuma saboda ni dai duk a masu zuwa wurina babu mai aure." Ai jin wannan arya sai kuwa Kurfi ta kece da dariya, dariyar da ta mantar da ita damuwarta na an lokaci. "Ashe dai kina da tsoro? Toh ni ce Kurfi." Wani tsaki Tasleem ta ja itama ta hau dariyar. Sai da suka gama an nanayensu kafin Tasleem ta nemi sanin ya akai ta sauya lamba. A takaice ta fa i mata yanda akai, sai kuma sannan damuwar ta dawo mata. Ta labarta mata komai. Tasleem ta yi ar dariya. "To ke meyasa tafiyar za ta dameki alhalin ba son junanku ku ke ba?" Maganar ta ata ranta. "Ai dama ba cewa na yi muna son juna ba, amman dai kin san ba da i irin wannan ko yaya dai. Da sunan an maka aure kuma sai ka koma gida zaman shekara, ki fa gane tsaurin da ke a ciki. Hatta fita fa ban isa ba yanzu sai da izninsa. Kuma ki duba yanda ya aukarwa Hajiya alkawari a kaina fa." Tana kaiwa nan sai zuciyarta ta karye ta soma rera kuka. Tasleem ta an yi shiru tana sauraronta, amman a gefe aya murmushi ta ke iyakar iyawarta. Wani irin sanyi da rahma ke ratsa zuciyarta, hamdala ta ke ga Allah tana mai arawa da ya soma amsar addu'arsu. Ta riga da ta gama ganewa, Laila Kurfi is deeply in love with Khalid Kurfi wanda ba lallai idan ta fa i ta yarda ba. Yanzu ne Kurfi za ta iya ya i da kiyayyar da Hajiya ke musu, wannan ce damarta sai dai kuma kash! Gogan zai tafi, tafiya mai nisa. "Dilla ni kin yi shiru kin i magana!" Tsawar Kurfin ya katse tunaninta ta yi firgigit. "Au yi hakuri, na bar ki ki gama sharar hawayen ne. Ki yi hakuri, yaushe ne tafiyar?" "Bai fa amin ba Malama, ba na ce miki kawai ya ce cikin satin nan ba?" "Hakane na an manta, ke dai ki danne duk wata damuwa. Ki yi hakuri idan kin koma gidan zan shigo. Ki godewa Allah ma za ki samu ki ci gaba da karatunki. Kinga kafin ma ya dawo kema zuciyarki za ta samu nutsuwa." Tasleem ta lalla a ta kwantar mata da hankali a karshe suka rabu cikin wasa da dariya. To shima dai Abba da ta kira kusan bakinsu ya zo aya da Tasleem, kwantar da hankalinta ya yi gami da nuna mata ci gabansu ne baki aya. A gefe aya kuwa farin ciki ne ya cika zuciyarsa ganin ta damu da tafiyar mijinta. Yana ji a jikinsa akwai alamun nasara a zamantakewarsu nan gaba. *** "Cin fuska arara!" Hajiya ta furta rai a matu ace sa'ilin da Mama Zahida ta dire mata ledojin kayan ma ulashen da Huzaifa surukinta ya kawo musu. Mama Zahida ta hangame baki kafin ta nemi wuri ta zauna. "Ah, to abin bai kai haka ba. Yi ha uri. Ke in ce ma Hajiya ba shawara ki ke auka ba, kin i maida hankali ga abinda ya dace. Ta ya ya yarinya arama za ta tsonemaki idanu ta hana ki kwanciyar hankali alhalin manyanta ma kin san ya za ki tafiyar da su balle kuma ita? Haba Hajiya, a zamanin nan ne za ka wani kafawa yaro shara in kar ya kusanci matarsa? Wannan ma kema kin san ba mai yiwuwa bane. Allah Yasa Khalid ba ya motsawa nan da can sai da izninki, to wallahi sadda zai bijire a nan ba za ki sani ba." Hajiya ta yi shiru alamun zantukan sun shige ta. Ta numfasa. "Kema fa kin yi magana Zahida, amman bar ni da su. Bari ki gani." Rai ace Hajiya ta jawo waya ta danna wa Malaminsu kira. Ringing uku a na hu u ya aga. Bayan sun gaisa ta soma karanto mishi abinda ta ke bu ata, baki sake Zahida ke kallonta tana mai mamaki. Ashe dagaske Hajiya ta fi ta iya shu'umanci, wani da i ya ratsa ta jin abin ba'a iyakar Laila zai tsaya ba. Bayan gama magana, daga can Malamin ya amsa. "Wai wai wai! Aikinki ga sau i ga wuya. Koda dai dama na ce miki auren ne ba makawa sai an yi shi, amman sauran abinda zai biyo baya a auren mu mun san hanyar da za mu shawo kansa. Wuyar aikinki bai wuce na binne-binne da kuma dokokin da za'a gindaya mishi ba. Da in da awa, mu na bu atar kayan kowannensu kala bibbiyu saiti kenan. Idan da dama kuma kema ki taho da hular shi maigidan naki da an uwansa. Kaf dai wa anda ki ka ga ya dace a yi miki aikin a kansu. Wannan ba irin wanda muka saba bane Hajjaju, wannan ya sha bamban da kowanne don haka dole a kula kuma a yi takatsantsan. Sai dai sau inta, muddin an aiwatar yanda ya kamata to ba ki da matsala, akwai romo mai yawa da za'a sha don nikam ina ga idan ba ki kaini Makkah ba to fa za ki yimin kyautar kece raini." Wata dariya suka sanya a tare shi da ita. "Ranka ya da e kenan, kai kanka ka san ba matsala bane. Fiye da abinda ka furta ma za ka samu muddin aiki ya kammalu. Kar ka damu, idan na ha a komai da ka bu ata zan zo har inda ka ke na sameka. Yanzu dai ka ara aikomin account number zan turo da na shan ruwa." "Yauwa Hajjaju, shiyasa na ke son himmarki. Ki taho har da ita Hajiya Zahidar, saboda itama dole sai ta yi aikin can wuraren nata." Hajiya ta gya a kai tana murmushi ranta fari tas. "Wannan ba matsala bace ranka ya da e. A huta lafiya." Daga nan sukai sallama, ta maida dubanta ga Mama Zahida, suka saki shewa gami da cafkewa a take. Nan ta labarta mata komai, sosai abin ya yiwa Mama Zahida, ta shiga jerawa Hajiya kirari kafin su rabu akan kowa zai iya arinsa. *** A kwanakin gaba aya Khalid bai samu zama ba saboda shirye-shiryen tafiya. Idan ya fita aiki bai cika dawowa da rana ba ha ka nan da dare sai kusan bayan sallar isha. Ita kuwa Kurfi ba ta fashi wurin kula da wasu a ha insa da suka ratayu a wuyanta, burinta ko ba ta zama kamar Maminta ba, to ta yi koyi da abi'unta wajen tsaftar gida da kula da miji duk kuwa da ta san ba duka ne za ta iya ba. Ta fahimci akunan gidan sosai musamman sashinsa. Akwai sadda karambaninta ya ja ta fa a study room insa, anan ne ta ga litattafai kala-kala daga na abinda ya shafi karatunsa har ma da novels na turanci. Ga mamakinta ma Love stories sun fi yawa, abin ya aure mata kai har ba ta san sadda ta ta e baki ta ce. "Ikon Allah, shi har wani love ya iya? Ya dai jera kawai don cika wuri. Gwanin na iya." Ta arashe da dariya gami da maidawa, ta juyo kenan ta ga mutum tsaye bakin kofar. Ya yi crossing kafafunsa, suit ne a jikinsa, sai dai ya cire top in ya sakalo shi saman kafa a gami da ri ewa da hannu aya. aya hannunsa na dama makale cikin aljihun wandon, necktie in kuwa tuni ya sassauta shi. Kallo aya za ka yiwa fuskar ka fahimci ba aramin gajiya ce ya kwaso ba. Idanun gaba aya sun juye sun sauya zuwa ja ha ka nan sun ara narkewa. A lokacin gaba aya arfe uku da wasu mintuna na rana, gabanta ya hau bugu da sauri-sauri, ba ta ta a zaton ganinsa a lokacin ba ganin da ta yi ya ci kusan kwanaki uku ba ya zama gida. Daga ita sai riga off shoulder ja iyaka ugu da dogon wandon jeans fari mai adon duwatsu daga cinyoyi. Kallon tsaf ya ke mata irin wanda bai ta a yi mata ba idan ya gan ta da shiga haka, sai dai ya kora ta ko ya dakamata tsawa. Shape ne da ita sosai, tana da ira mai kyau. Ita kuwa duk sai kallon ya gundure ta, ta sha jinin jikinta. Tsoro ya kamata, ta yi azamar komawa bayan bookshelf mafi kusa da inda take. Ta an ci mintuna kafin ta leko a hankali da zummar ganin ko ya bar wurin, ta yi mamakin rashin ganinsa kuwa. Ta sauke ajiyar zuciya ta fito, ba ta yi aune ba ta ji an ri ugunta an mur a, ta kuwa juyo ba da shiri ba har ta kusan fa uwa ya yi mata kyakkyawan