← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 41

Sashe 34

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aya daga cikin akunan masaukin ba i ne, sai dai Hajiya ta sanya a kwashe abubuwa da dama na more rayuwa a ciki. Kamar kashe Ac da lalata socket, auke gado da barin katifa sai kuwa kayan kallo da aka kwashe da sif na sanya sutura duk domin ta untata rayuwar bayin Allah. Wayar Munira da Batul duk sai da ta bi ta kwace. Kasancewar su na da damuwar da ta fi wannan ya sanya ko a jikinsu ba su wani nuna damuwa ba. Munira itama aikin bai fiye dagula lissafinta ba don kuwa angarensu ar aikin kusan ba abinda ta ke yi sosai kasancewar Ummi ta fi gane yin aiki da kanta tare da anta. Banda wannan ma, tun usuli ita Munira mai son aikace-aikace ce. Makarantarsu ta koma shan ruwan tsuntsaye, wataran su je wataran kuwa duk saurinsu to fa ba zasu iske motar ba, Hajiya sun sanya direba tafiya ya barsu. Haka dai karatun yaran ke samun nakasu. Idan kuwa Daddy ya dawo, basu da damar zuwa sashinsa, shi inma bai fiye damuwa da sanin halin da suka tsinci kawunansu ba. Zuwa lokacin ba waya wurin Kurfi don tuni Hajiya ta kwace a wata rana da ta kama ta su na waya da Adda Maijidda. Haka suke gudanar da rayuwarsu marar da i. Sosai ta sanya yaran ibada da yin azkar. Ita da Munira kuwa saukar Kur'ani suka au haramar yi saboda fatan ganin arshen abin. an uwan Ummi sun biyo sahu don jin dalilin da yasa Daddy ya kora ta gida ya nuna cewar tarbiyya ya ke son ta koyo na zama da miji. Wannan magana ba aramin ciwo ta yi musu ba, arshe dattijon mahaifinta ya ce a kyaleshi har zuwa sadda zai tako da afarsa. Da wannan su ka zuba mishi na mujiya. A satin Aliyu ya aga zuwa London karatu. Tafiyarsa ba aramin nutsuwa ta samar wa Kurfi ba, ko ba komai tsangwamar za ta ragu. *** Da safiyar ranar asabar bayan su Abdallah sun fice makarantar Tahfiz. Kurfi su na kicin tare da su Lauratu gaba aya suna aikin girke-girke sakamakon Hajiya da ke da biki za ta fita. Kusan ran Kurfi tas ya ke a ranar don kuwa fitar Hajiya dama ce ta samu da za ta shiga sashin Abbanta don nemo zamzam da za ta aiwatar da addu'o'inta. Su na kammalawa aka sanya a manyan warmers aka mi a mota. Daga Hajiyar sai Mama Zahida da yaransu suka fice. Bayan fitarsu Kurfi ta sulale zuwa sashin Abbanta bayan ta ba Lauratu ta samo mata ganyen magarya a kasuwa. Babu wani ja in ja Lauratun ta kar a don kuwa an yi sa'a Hajiyar ta aike ta kasuwa a sannan, idan ba don haka ba, babu ta yadda za'a yi Buzu sabon Maigadinsu ya bari a fita ba da iznin Hajiya ba. Tana shiga ta tsaya tana arewa hanyar akin Maminta kallo, wai wata ake son a kawo matsayin matar Abbanta. Watan ma ba wai ta kirki ba shai aniya irin Luba. Hawaye suka gangaro nata ya yin da ta ke kutsawa sashin Abba tana kallon ko'ina, akwai memories da kowane angare na gidan ke tuno mata na yanda su ke rayuwa a baya ita da iyayenta mafi soyuwa a ranta. Har wasan uya da ta ke yi a baya da Abbanta da irin shagwa atan da ya yi ba wanda bai fa o ranta ba. Ta tuna sadda ya dam a musu laptop yanda ta dunga tsalle tsabar farin ciki kafin daga bisani ta zauna tana mishi godiya kamar yanda Zeenat ta yi. Ta share domin duk wannan ba na yanzu bane, hakan yasa ta share idon don su yi mata hasken da za ta ga hanya tar-tar. Ta rasa dalilin da yasa Abban bai rufe ofofin angarensa, sai kuma zuciyarta ta tunasar da ita dama mafi akasari Mami ke rufewa idan ta ga ya fice ya bar angaren haka. Kai tsaye ta kutsa kai ta shiga. Ba ta yi mamakin ganin wurin ba a tsaftace ba, har da su robobin take-away yashe a asan. Ita ba ta san meke faruwa ba ya ta a Abbanta har haka, to mene amfanin ma'aikatan da ba ya basu umarnin gyarawa? Batu na girki kuwa, dama ta riga da ta san cewar girki kam na Maminta ka ai ya ke ci. Mami ba ta da mai girki sai kuwa Baba Asma'u mai taya ta hidimar da ba'a rasa ba. Ta zauna a hankali a asan carpet, Abba mai son tsafta ne, ko abu aya ya tarar ba'a gyara ba, nan da nan zai ji ba da i har ya kai ga magana. A yau Abbanta ke zaune cikin wannan dau ar? Kuka ya zame mata abokin hira, shi ta shiga rerawa tana shesshe a, rayuwa a gidan ubanka ya gagaresu. Dama ana haka wai? Komai ya sauya lokaci guda? Duk arzikin gida ashe sadda arzikin ba zai iya taimakonsu da komai ba? Istigfari kawai Kurfi ke yi a ranta ya yin da tsoron Allah ke ara ninkuwa a ranta. Shakka babu jarrabawarSa ce, fatan da ta ke Allah Ya ba kowannensu ikon cinyewa. Ta udurta a ranta ko Hajiya za ta kasheta, ba abinda zai hana ta dunga gyarawa Abbanta sashinsa. Hakanan duk sadda sukai girki za ta dunga iba tana kai mishi. Tana gyaran tana ulle- ulle da yawa a ranta. A haka Munira ta shigo ta risketa. Ganin jimawar da ta yi ba ta dawo bane ta yanke zuwa ta ga ko lafiya. Nan ta taya ta, ganin haka Kurfi ta shige aka, ba laifi nan kam a an kimtse yake. Ta ara kimtsa shi kafin ta fa a ban aki ta wanke sai dai bini-bini takan share hawaye. Kirjinta har wani zafi ya ke. Bayan ta kammala ta hau duba Zamzam a inda ta san Abban na ajiyarsa. Cikin ikon Allah ta ga akwai har jarka aya da rabin. Wannan abu ba aramin da i ya yi mata ba. Ta auki rabin jarkar ta fito tana nuna wa Munira. Itama ta yi farin ciki sosai. Suka fice gami da rufe akunan. Karfe hu u ta yi girki mai rai da lafiya, bayan ta zuba na Daddy, ta zuba wa Abbanta ta mika sashinsa ta jera saman centre table inda ta ke da tabbacin zai gani. Har za ta fita kuma ta dawo baya ta au takarda ta nemi biro. Short note ta rubuta ta ajiye saman kulolin kafin ta fice a ranta wani irin nisha i ta ke ji ganin bayan wasu lokuta da yawa ta kyautatawa mahaifinta. Koda Abban ya dawo ya yi mamaki sosai sai dai kuma ya ji da in ganin ko'ina tas. Ya kai duba ga abincin da ke a ajiye, sai kuma abin ya aure kansa. Ganin ar takarda ya auka ya duba. _"Abbana, don Allah ka ci, ni na girka maka na kawo. arka Laila AbdulHamid Kurfi."_ Ya an yi shiru, a hankali ya ji cikowar kwalla a idanunsa ba tare da ya san na mene ba, yana jin wani abu na taso mishi sai dai ya rasa me ke danne shi, koyaushe ya na jin zuciyarsa kamar wani abu ya tokare, shi bai tafi ba shi kuma bai fito ba. Jin da ya yi kansa ya soma sarawa ya ha ura da tunanin ya shige aki. Nan ma lamarin ya mishi da i ainun. Ranar dai take away da ya taho da shi bai samu shiga ba don kuwa girkin Kurfi ya ci. *** Karfe sha biyun dare bayan kwanciyar kowa a gidan, Kurfi da Munira suka shiga aiwatar da addu'o'in karya sihiri ta hanyar amfani da ganyen magaryar da suka ni a da dutsen ni a sai zam-zam. Tofi suka shiga yi na ayoyi daban-daban na Alkur'ani kamar yanda aka koyamusu a Islamiyya na karya sihiri wanda matu ar an dage to In sha Allah a sati ma sai a samu biyan bu ata. Bayan sun kammala suka nemi empty robar ruwa biyu na Faro da suka shigo da su suka juye. Bayan kammalawarsu Kurfi ta dubi da idanuwanta da suka cika da bacci tana murmushi. "Alhamdulillah, in sha Allah zamu nasara akan iyayenmu maza. In sha Allah Kurfi's Family ya kusa daidaita." Murmushi itama Munira ta yi cike da jin da i da ara yaba hankali da hangen nesa irin na urfi duk kuwa da cewar ta girme mata da shekara aya, amman ita ta kawo shawarar yanda zasu yi komai. "In sha Allahu. Fatana a gareki kema Allah Ya dawo da Yaya Khalid ya kar e ki hannu bibbiyu." Anan Kurfi ba ta ce komai ba hakazalika yanayin fuskarta bai sauya daga murmushin ba sai dai ya koma na ya "Asuba ta gari." Abinda ta furta kenan gareta kafin ta mi e ta maida Kur'anin ma'adanarsa sannan ta cire hijab da zanin sallarta ta ninke ta nemi wuri ta kwanta. Tana jin sadda Munira ta kwanta bayan ta kashe musu fitilar akin. A hankali ta lumshe idanunta tana tauna maganar Munira asan zuciyarta. Gani ta ke dai abin da kamar wuya, ta sani koda ace Khalid ya dawo, bai zamo lalai ya ara kallonta matsayin matar aure ba. Tana ji a jikinta kamar auren babu inda zai je. A hankali ta lumshe ido hawayenta suka zubo, idan ta ce ba ta kamu da matsanancin soyayyar Khalid ba to kuwa ta yaudari kanta da zuciyarta. Tun tana jin tsanarsa ta zo ta fahimci cewar ashe na an lokaci ne. Zuwa yanzu ita aya ta san me ta ke ji game da shi a ranta, sai dai a kaan kanta ta ke ture abin, ta ke yakicewa gami da arin ganin bai yi tasiri ba a ranta. *** Washegari tun da safe Kurfi ta auki jarka guda na ruwan faro ta yi sashin Abbanta tana waige gudun kar Hajiya ko yaranta su hangeta. Sai dai har ta isa babu wanda ya ganta, zuwa lokacin bakinsu guda da su Habiba da Lauratu, wannan tasa ba ta samu matsala daga garesu. Tana isa ta tsaya a ofar falon ta yi sallama, ta san dai a lokutan da wuya a samu Abbanta na bacci, don kuwa muddin ya tashi sallar Asubahi to fa ba ya komawa sai rana ta fito. Ji ta yi an amsa
Chapter 34 · 0% Book details