← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 41

Sashe 5

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

***
Tana shiga bangarensu ta nufi Maminta ta kwantar da kai saman kafadarta fuska a tur6une, Mami ta dan dubeta tayi murmushi. Baba Asma'u ta kalleta.
"Aa, 'yar gidan Mami lafiya kuwa? Wa ya ta6omin ke?"
Kurfi ta k'i magana, ranta zafi kawai yake, tsanar Yaya Khalid take ji kamar ta shak'eshi idan da hali.
Mami ta dagota tana kallon fuskarta. Cikin sanyinta ta ce.
"Ke da wa kuma?"
Sai hawaye ya soma zubomata.
"Yaya Khalid ne, wai Mami meyasa ni kadai ya tsana duk a cikinmu ne? Kowaccenmu muna zaune amman ya rasa wacce zai yiwa fad'a sai ni. Kullum idan ya zo sai ya nemi abinda zai takuramin da shi. Na tsaneshi wallahi."
Mami ta yi murmushi gami da sharemata hawayen. Hannunta ta riko ta sanya cikin nata.
"Ke yanzu ba ki ga kuskuren da kika yi ba? Tun farko ba sai da na ce kar ki fita haka ba amman kika k'i saurarona? Kada ma na kara jin kin ce Khalid ba ya sonki, soyayyar kenan. Shi ya sanya har yake kwa6arki idan kin aikata ba daidai ba kin ji ko?"
Ta ji, ba don zuciyarta za ta iya gaskata cewar yana son natan bane, ita dai tasan ta amince ta yi kuskuren fita a hakan. Mami ta ci gaba da rarrashin diyarta har sai da ta sake, Baba Asma'u ta tayata da hira da hadawa da ban dariya. Su na a haka Yaya Hussain ya biyo bayanta ya kawomata Laptop san nan ya fice. Mami ta dubeta.
"Chanja kayan ki fito kada ya zo ya iskeki haka." Ba musu ta mike ta sauya ta dawo, nan ta ci gaba da kallonta tana shan kunun gyadar da Mami ta yiwa Abba.
A haka ya shigo ya risketa. Ita kadai ce a falon, Mami ta wuce sashen Abba yayinda Baba Asma'u ke aikin tuwon dare.
Ta chanja zuwa riga doguwa pink mai karamin hannu ta shan iska saboda garin akwai yanayin zafi. Ya kai duba ga fankar da ta ware har lamba biyar, itama irinsa ce, akwa
i jin zafi. Kamshin turarensa yasa ta daga kai tana kallonsa, ga mamakinta murmushi ya danyi, ta dan runtse idanu ta budesu sosai don ta dauka gizo kawai yakemata. Sai dai ta ga ba haka ba, shima ganin ta rainamasa wayo ya sanya shi tamke fuskar. Ya karaso ciki. Sai san nan ta tabbatar dagaske shi dinne, a hankali ta cire headphone ta ajiye.
"Mami fa?" Da hannu ta nunamasa hanyar sashen Abba. Ya dan tsaya kallonta kafin ya kama hanya. Bayan tafiyarsa ta sauke ajiyar zuciya tana murmushin mamakin nasa murmushin. Can kuma ta ta6e baki.
"Duk cikin salon mugunta ce."
Daga nan ta dora daga inda ta tsaya a kallonta.
***
Bayan Sati Biyu
Yau juma'a suka kammala jarabawa a makaranta wanda da zarar sun dawo hutu zasu shiga ajin karshe a sakandire yayinda su kuma Hafsat shekarar fitarsu kenan. Washegari suka halarci makarantar su Hafsat (makarantarsu ba daya ba) inda aka yi bikin yayesu. Bakin Hafsat kamar ya tsage don murna, gani take burinta yanzu zai cika na auran Yaya Khalid kamar yanda Mamanta Zahida ke bukata.
Ko sati Kurfi bata kara a gidan ba suka tattara tare da Zeenat zuwa gidan kanwar Mami, Anti Rumaisa. Tana son zuwa gidan sabida tana samun yancin zance da samarinta, haka zasu hadu da Tasleem diyarta su yi ta yawon zagaye gari kasancewar Anti Rumaisa ma'aikaciyar asibiti. Sai ta wuni bata dawo gidan ba. Wannan ya kara basu dama, su fice abinsu yawon shoprite da sauran wuraren bude ido a motar saurayi su barwa Zeenat kula da yara.
Yau dinma hakan ce ta faru, bayan fitar Anti suka shirya tsaf cikin doguwar rigar atamfa da ta sha dinkin balloon gown suka yafa dan fingilin mayafi suka fice har Zeenat da ta ji tana son binsu. Suka bar gidan daga yara sai Ladi mai aiki.
Karfe biyar da rabi na yammaci, wannan karon Dalal suka nufa siyan shawarma. Keke napep suka hau, a hanya Kurfi ke ta daukar hotuna da wayar Tasleem, tana yi tana mitar rashin mutuncin Yaya Khalid na kwacemusu wayoyi. Zeenat ta dara.
"Kuma dai, ni dama tun sadda ya nuna baya so na ji rikewar bai burgeni. Gwara idan ya bani da hannunsa kamar yanda ya bawa su Hafsat sai ya fi burgeni. Kuma banda abinki muma ai kamar yau ne zamu yi Candy din ya mallakamana."
Jin haka Kurfi ta dubeta.
"Eh fa, ai na manta ba'a ta6a shi a gabanki, yanzun sai ki murd'e ki hau nuna ba laifi ya yi ba komin girman laifin. Laila ta Majnun, kina shirme ne baisan kina yi. Na gwadamaki hanyar yi kin k'i dauka."
Zeenat ta harareta.
"Allah Ya sauwake, don Allah Tasleem kawai don kana son mutum sai ka zubar da mutuncinka ka je ka tallata kanka?"
"Inaa, sam wallahi, ban goyi bayan kiyi haka ba. Rabu da waccan yar iskar itama ba aikatawar za ta yi ba" Cewar Tasleem.
Kurfi ta buga tsaki.
"To yan iska, an fadamaku nufina ta je da kanta? Ai cewa nayi ta barni na sanarwa ko? Kuma kinsan dai komai na tambayi tana yimin. Wallahi sai kiga ta hadaku ma auren a satinnan."
Zeenat ta kai mata bugu a cinya tana kiran bata so suka kyalkyale da dariya gaba daya. Haka suka yi ta hirarrakinsu har suka isa.
Suna shiga katafaren shagon na ciye-ciye, suka nufi bangaren shawarma. Yan matasan wurin sai kallonsu suke yi, ko babu komai sun burgesu don kuwa sun yi kyau kwarai. Daya a cikin samarin wajen ya kasa hakuri ya taso ya iso inda suke. Tun shigowarsu yake kallon Kurfi, bisa kwarin gwuiwar da abokinsa ya basa ya sanyashi nufarta.
Sallamar da ya yi ta sanya ta juyo ta dubeshi ta kauda kai. Dakyar ta motsa le66anta ta amsa. Ya numfasa yana kara jin kansa a sama, lallai idan ya samu soyayyar mace irinta ya ca6a, wannan irin aji? Ya maida hankali ga abokan tafiyarta.
"Sannunku."
"Yauwa." Suka amsa fuska a sake, Tasleem za ta biya kudin, ya girgiza mata kai.
"No, bari yayanku ya biyamaku ko?"
Kurfi ta dubi Tasleem tayi mata ido, murmushi Tasleem tayi gami da daga kafada.
"Ok, thanks."
Ya biyamusu bayan ya karamusu da lafiyayyar kaza da youghurt mai sanyi.
Jansu ya yi har mazauninsa da abokinsa, ya ja wa Kurfi kujera ta zauna. Suma suka ja suka zauna.
Nan ya dubi Kurfi fuska dauke da murmushi.
"Sunana Nasir ana cemin Nas, shi kuwa abokina sunansa Dawud. Idan ba damuwa ko zamu iya sanin sunayenku?"
Tasleem za ta yi magana Kurfi ta takemata kafa. Nan ta gane karatun hakan yasa ta sauya salon zancen ta hanyar yin 'yar dariya.
"Sure, ni sunana Badiyya, ita kuwa wannan (ta nuna Zeenat), Iklima sai wannan (ta nuna Kurfi) Farha."
"Wow, what a nice names! Na ji dadin haduwa da ku musamman ma Farha."
Ya karashe yana kannewa Kurfi idanu, ji take kamar ta yi tsuntsuwa don murna, ita a duniya burinta kawai ace ana sonta koda bata son mutum to tasan tana da masoya. Murmushin yak'e ta sakarmasa sa'ilin da ta sauke robar youghurt.
Nan suka dan ta6a hira yana bata labarin rayuwarsa kadan, a karshe suka mike da zummar tafiya, shi da Dawud suka mike don yi musu rakiya, ganin basu zo da abin hawa ba yasa ya rok'i da su kaisu gida. Ba musu Kurfi ta ce toh ba tare da tunanin komai ba.
Tare suka jera har gaban motarsa kirar Ford. Kurfi ta kalli su Zeenat, suka saki murmushi, sosai motar ta burgesu.
Gaba daya suka d'uru a baya, ya ja motar. A hanya ma kid'a ya ware yana tuk'i yana kallon Kurfi ta gilashin motar, ita kuwa sai wani kashemasa idanu take kamar gaske. Tasleem da Zeenat su na dariya ciki-ciki.
Chapter 5 · 0% Book details