Sashe 24
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mijinta. Mutumin da bata ta a jin sha'awar ta aureshi ba. Duk wannan so da zuzutashi da an uwanta ke yi, babu ita a ciki. Har zuciyarta ba ta jin sonsa, ari dai yanzun tana ganin mutuncinsa akan baya. Ko don saboda yanda ya dunga kula da Maminta kafin ta rasu. Sauke ajiyar zuciya ta yi a hankali, sai kuma gashinan Allah gwanin hikima Ya ha asu aure. " *MU ADDARI* " Ta yi furucin a fili san nan ta samu ta mi e da bismillah. Sai da ta gyara akin tas ta fidda kayan da ta ci kaza jiya da komai ta share kafin ta fa a wanka. Bayan ta fito ta shirya tsaf cikin doguwar rigar material mai yellow da ba i, hoda kawai ta an goga a fuskarta ta fita falon. Sai a san nan ma ta samu nutsuwar arewa falon kallo. Murmushi ta dunga yi don kuwa ba aramin burgeta ya yi, shakka babu Daddy ya yi arin ku i domin kuwa tana da labarin shi ya au nauyin komai. Kujerunta ba e masu orange pillows, hakanan labulen in orange ne da kuma kafet in tsakar akin orange da sirkin ba i. Sai ya zamana duk sauran kayan da aka zuba na awata aki kalolinsu bai wuce hakan ba. Ta numfasa ta arasa sauka asa, nan ma falon ya yi kyau don komai na ciki dark brown ne da milk. Ya yi kyau sosai kuma ya an sanga komai na adona muhallin da ya dace, Cikin kicin in ma dai ya yi kyau warai, ya sha kayan electronics da utensils masu kyau da tsada. Ta wanke plates ta tattara, falon ma ta an gyara shi don ba wani datti ya yi ba sosai kawai saboda jama'a da ya tara a jiya ne ( an kawo ta). Sai da ta tabbatar ya koma yanda ya ke san nan ta maida hankali ga kwanukan abincin da ta gani saman dinning table. Kallo aya ta yiwa kayan tasan na gida ne ba wai odar abincin ya bayar daga waje ba. Tea kawai ta ha a ta sha san nan ta wanke kofin. Bata yi karambanin washe kulolin ba don ba ta da masaniyar bai ci ba ko ya ci. Falon sama ta koma, zama ta yi gami da buga tagumi. Ka aicin ya soma zama takura gareta, ta saba da gida na jama'a, zama a irin wuri haka sai ta ji duk ta takura. Wannan shirun ya janyomata tunani iri-iri, bata manta washegarin ranar da aka kai su Rahma ba, hirarsu da Mami ta zama akan aure. Inda ta ke cewa ita kam sai dai Abba ya bata Mamin su je ta an mata sati uku. Mami dariya tayi gami da tsaki a lokacin na wautarta. "_Shekara zan miki kin ji ko? Koda dai idan ba ki kashe nawa auren ba, naki zai mutu murus. Majnun zai maida ki majnuniya._" Dariya ta an yi a fili, sai kuma ta dawo duniyar da ta ke a yanzun, bata san sadda ta soma kwalla ba. Kewar Mahaifiyarta ya dawomata sabo fil. Cikin wannan yanayin ta tsinci muryarsa yana sallama, da hanzari ta share fuskar. Ya ganta sarai, ya san kuma kukan ta ke amman ya za i da ya basar. Zama ya yi saman kujerar yana an sassauta fuskarsa , kafin ma ya ce komai ta rigashi. "Yaya ina kwana." Ya an yi jim yana wani shan amshi kafin ya amsa. "Lafiya, ya jikin naki?" Ta soma da gya a kai. "Da sauki, na warke Alhamdulillah." "Hakan na nufin ba ki sha maganin ba yanzu?" Kamar ta ce A'a sai kuma ta daure ta amsa da Eh. Ya ha e fuskar. "Tashi ki auko." Ba musu ta mi e tana kunkuni don ita dai ta gaji da shan waya, acewarta. Ya bi bayanta da kallo kafin ya maida kai ya kwantar jikin kujerar, idanun ya lumshe yana tuna abubuwa da dama a ransa. Tambayar da ta fi yawo a kwakwalwarsa yanzun bai wuce na yadda zai soma rayuwa da Laila a matsayin da ta haura a wajensa ba yanzun. Kamar zai iya, kamar dai ba zai iyaba. *_'Laila amana ce a wajenka, kai ne mijinta, abokin kuka da dariyarta. Kai ne abokin shawararta. Ka yi ari ka zama namiji, ka sani rai da mutuwa duk mu addari ne daga Allah. Ka kuma sa a rai wataran za ka mutu ka koma gareShi, zai tambayeka bisa amanar da ya ba ka, muddin ka ci ba zai kyaleka ba. Khalid ka zama magidanci, ka ji tsoron Allah kar ka cutar da ar mutane.'_* Ya tuno duk zantukan Baba Mudassir gareshi a sadda ya shiga gaida shi. Yana cikin wannan tunanin ta fito, dubansa ta tsaya yi ta gefen idanunta bayan ta zauna, ta e baki ta yi. 'Kowa dai ya yi jinyar tasa zuciyar, nima ba ka bar tawa ta huta ba, tunda ka bari ka aureni ai shikenan ka jaza mana wahala.' Ta yi ta sa e-sa enta a zuciya, tana kallonsa sai kawai gani ta yi idanunsu sun sar e wuri guda, tar shima idanunsa a kanta yana aremata kallo. Shi kallon da yake na son tantance ko akwai inda ta kuskuro a fannin sura da kyan hali da bai ta a jin sonta ba. Ta gaji da kallon ta auke kai gami da an tsuke baki tana magana asa- asa. aya kenan.' Ya fa i a asan ransa, Kurfi bata jin magana, akwai iriniya shi kuma silent ne bai son hayaniya da mutum marar ji, yana tunanin ta sauya amman yanzu ya lura mutuwa ce ta an kawo sauyin. Wannan ke ha asu da ita shakka babu. "Kawo mu gani." Ta ji shi sarai amman don ta rama sai ta i koda motsi. "Ke, ba ki ji abinda nace bane?" Ta ara uluwa da ke in da ya kirata, ashe Lailar da ya soma fa i na an lokaci ne ma. Ta daure ta dubeshi kafin ta mi e ta kai mishi ledar. Ya sa hannu ya kar a gami da bata umarnin ta kawo ruwa, ta arasa ga inda firij yaka, a wani an jerin plates da cups da a ka sanyamata cikin cupboard ta au cup aya ta tsiyayi ruwan dispenser. arasawa ta yi bata ko kalleshi ba, ta sa hannu ta kar i maganin da ya allo, kallon maganin ta tsaya yi tuni ido ya raina fata, ba ta san ta yanda za ta soma sha ba. Ta dubeshi a sace, ya kuwa uramata idanu yana jiran ta sha. Ta kauda kai gami da an mazewa. "Yaya nifa na warke. Idan na sha amai zan yi." "Ko?" Ya furta yana kallonta girarsa a age. Sai ta ji kunya da tsoronsa, ta kauda fuskar tana mai gya a kai. "Ok, sha sai ki yi aman." Ta ga dai dagaske ya ke sai ta zauna a inda ya mata umarni, saman kujera. Ta kasa sha sai kallon maganin ta ke, wayoyi har biyar. Tunawa ta yi da yanda Maminta ke mata idan za ta sha magani. Da sauri kuwa ta mi e, ya yi saurin dakatar da ita. "Ke ni abokin wasanki ne?" Yanda ya yi maganar a kausashe sai ya tunamata ko waye shi, cikin muryar lalla awa ta ce. "Madara zan ebo, haka Mami ke min idan zan sha magani." Ta arashe murya a karye, ya ji har a jikinsa, fa in Mamin sai ta karya lagwonsa, ya bita da kallo sadda ta soma tafiya, tausayi ta ba shi. Shi kansa yana kewar Mamin sai dai ta koma ga wanda Ya fi su son ta. "Allah Ya yi mata rahma." Ya furta asa- asa gami da cewa amin. Ita kuwa magungunan ta ajiye cikin ledar. Kofi ta auka za ta nufi asa inda nan ta ga kayan shayi ya dakatar da ita da fa "Ki kawomin kayan abinci." Da to ta amsa tukunna ta sauka. Ta zuba madara da milo ta caku a sannan ta au babban faranti kamar yanda ta ga Mami na yi ta ora komai a kai ta nufi saman tana maida numfashi saboda nauyin coolers in, ta koma ta auko flask na ruwan zafi da sauran kayan shayi, har ta ajiye kawai kallonta ya ke bai ce uffan ba, ta gama maida numfashin sannan ta sha maganin, tana kammalawa ta hau shan madararnan da cokali. Bai san sadda ya soma jinjina kai ba, wato dai yanzu idan za ta sha magani haka Mamin ke mata? Lallai ar gatan Mami ce. Ganin ta kammala ya sanya shi mi ewa ya yi zaman dirshan saman kafet ya hau fidda coolers din, ita kuwa tana kammalawa ta nufi an sink da ke a falon ta wanke cup in fa Morning fresh ta goge ta ajiye. Tunani ta tsaya yi, ta an dakata tana satar kallonsa, tunani ta ke, ta je ta zubamishi ko kuwa dai ta kyale. Ita tsoranta kar ya gwatsaleta. Kamar ya san tunanin ta ya yi magana. "Ba ki iya ki zuba wa mutane abinci ba ko?" Jin haka ta arasa a hankali ta soma bu e coolers in, shi kuma ya shiga ha a tea. "Me kenan? Ba ki ci bane?" Ta dubeshi ta dauke kai. "Tea na sha, ya isheni." Bai tanka ba har ta kammala zubin san nan ta mike ta auko ruwa da lemun da ta gani a firij ta ajiye ta wuce akinta. Ya dubi ofar don ya ji sadda ta mur a key in, murmushi ya an yi kawai ya ci gaba da ha a tea hankali kwance. *** Ranar ta samu ba uncin an uwa da abokan arziki musamman an Kurfi wa anda a ranar wasu zasu wuce yayinda wasu kuwa sai washegari. Kwanaki uku ta yi tana kar ar baki kuma hakan ba aramin da i ya yi mata ba, koda ta ro i a bar mata Mu'azzam Hajja sam ta i ta ce ba yanzu ba, hakanan ta ha ura ba don ta so ba domin idan tana tare da jama'a mantawa ta ke yi ma da kalar auren da aka yi mata balle har ranta ya dunga sosuwa. Tana da kwanaki hu u a gidan sai dai ko angaren mijin ba ta ta a shiga ba sai dai ta an le a farfajiyar