← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 41

Sashe 39

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kyaleki za su yi ki huta da habaicinsu ba balle sauran an bani na iya mahassadanki." Hajiya ta gya a kai. "Ba ma za ta kai ga wannan ba Gwaggo, ba wani aton gardin da zan ara zuwa na dur usa gabanshi na saki aljihu. Na fasa duka wannan, zan nemi aiki wanda ba zai zo da kowace matsala ba. Ba dai sun wuce Kaduna ba?" Wani murmushi ta yi mai tarin fassarori. Gwaggo dai tana taunar goro tana dubanta ba tare da ta tari numfashinta ba har ta ora. "Ina nan ina jira har su dawo Kanon, na rantse sai na kai Laila lahira. Sai ta bi uwarta! Zan nemi an daba, kashemin ita nake bu atar a yi!" Gwaggo ta shiga gya a kai tana dariya. "Ko kefa, yanzu naji magana!" Suka dara lokaci guda. *** Hajja ta yi shiru tana fidda hawaye, kallonsu kawai ta ke yi domin kuwa yanzu Alhamdulillah tana tafiya ka an-ka an hakanan tana magana ra au. Yaranta ne durkushe a gabanta kowanne na faman ro o da neman gafara. Su Kurfi na gefe su na sharar kwalla. Adda Maijidda ma kukan ta ke. Ganin Hajja ba niyyar magana, Engineer ya sa ba ki. "Ha uri za'a yi Hajja, mun riga da mun san ba laifinsu ba ne. Abinda zai faru ya riga ya faru sai addu'a, mu godewa Allah ma da Ya amsa addu'o'inmu tun ma ba'a je ko'ina ba." Hajja sai a sannan ta yi magana. "Ba wai yafe musu ne ban yi ba, raina ne ke aci da zarar na tuno irin..." "Aa Hajja, ki yiwa girman Allah ki yi ha uri ki yafemana abar tone-tone. Wallahil azim idan na tuna yanda abubuwa suka kasance ina ji ne kamar na ha a rami na shiga. Mun riga da mun rabu da an kwal uban, ki tausaya mana Hajja. Ke uwa ce." Baba Mudassir ke wannan zantukan yana hawaye. Gaba aya ba wanda abin bai ta a ransa ba, nan da nan Hajja ta saki fuska gami da sa musu albarka. Ta kuma nuna komai in ya wuce ta yafemusu duniya da lahira. Hira sai ta koma ta da i, mazan gaba aya suka fice sallar Azhar. Matan ma sallar suka yi. Kurfi na ri e da Mu'azzam tana kallon yanda ya ara wayo. Kamanninta d shi ya ara fitowa zahiran. Sai ka rantse ita ce tana arama. Shima sai manne mata ya ke sosai. Hajja ta dubeta fuska auke da murmushi. "Lailatu, kin yi halin mahaifiyarki. Allah Yay mata rahma. Ban ta a kawowa za ki yi irin wannan ha urin ba, kullum kallon mai iriniya kuma rigimammiya nake maki. Sai ga shi nan Lailar nan ta bamu mamaki. Tunda na ji kin ce ke za ki zauna a gidan nan, hankalina ya tashi sai dai abinka da mutumin da ba baki ba. Na ji har a zuciyata Allah ne ka ai zai iya tsallakar da ke daga musibar wannan matar. Na tsorata domin na tabbatar akwai unci da damuwa. Sai ga shi da taimakon Allah kin yi arin da ya ara min kaunarki. Ko yau na fa i na mutu, ba ni da abinda zan saka maki da shi. Allah Ya ji an Sadiya, Allah Yay miki albarka Laila, Ya dawo da mijinki lafiya." Murmushi ta ke ta na goge yar kwallah, kai ta girgiza. "Kayya Hajja, idan fa kina haka sai ki ararmin da hawaye. Wato ke kin tsufa da idanunki ni kada na tsufa. To na i wayon." Ta wayance da maida abin raha, Hajja ta yi dariya. "Ai fa, mai hali ba ya fasa halinsa. Sai dai kam yanzu kin yi hankali. Matarnan dai Allah Ya isa tsakanina da ita." Dariya kawai Kurfi ta yi don ta gaji da ba Hajja ha uri a kan ta yafe mata. *** Kwanansu aya a Kaduna, komai ya wuce sun koma tsintsiya ma auri aya kamar ba'a yi ba. Dakyar iyayen suka shawo kan Hajja ta bi su don ta ce ba fa za ta koma ba. Yanzun ma sai da Daddy ya ba ta tabbacin zai je ya dawo da Raliya ya ba ta ha uri san nan ta amince. A hanya ta ke jin labarin auren da Abba ya ke shirin yi ya fasa. Hajja ta hau fa "Aikin banza, ka ce ka sanya anyi bincike yarinya ba ta da wata aibu komai lafiya kuma an samu kyakkyawan shaida yo me ake jira? Ka manta da silar wadda ka santa ka yi aurenka. Ga ta marainiya kuma ko ba komai ka yi jihadi." Abba ya murmusa yana mai tu i hankali kwance don shi kansa ya yaba da Yasmeen ganinta mace mai kunya da sanin ya kamata. *** Sati aya da komawarsu, gida ya dawo hayyacinsa, Hafsat da Rukayya sun sha koke-kokensu na rashin uwa a gida a arshe su ka ha ura ganin dai dagaske Baba Mudassir bai ha ura ba asalima da suka matsa ya yanke shawarar yin aure lokaci aya da Abba don ma su bar saka ran zai maido Zahida. Ummi ta dawo akinta bayan Daddy ya sanya an ara yi mata gyara na musamman an kwashe komai na Hajiya an kai mata. angaren Hajiyan ya fi nata kyau da tsaruwa sosai, nan aka gyara har da fenti da zuba sabbin furnitures duk a arinsa na wanke laifinsa a wajenta. Asalima yanzu wata zazzafar soyayyarta ya ke ji domin kuwa ya san ya yi rashin adalci gareta a baya sosai. angarenta sai ya koma wajen zaman Hajja da su Kurfi, dakyar ya samu Hajja ta dawo kusa da su maimakon can angarenta. Aka gyara sashin Ummi tsaf suka koma. Kurfi ciki da falo aka bar mata, a gefen akinta nan ne wurin Mu'azzam, shima an ha a mishi kayayyakin aukar hankali na wasan yara kala-kala. Tuni Balaraba ta dawo. Ko bayan zuwanta ta sha kukan murna. osai ta komai yi a bakin titi don rufa wa kai asiri. Su Adda Salamatu kam komai ya wuce domin su kansu har gidan sun tako an ara yafar juna. *** Ranar litinin su na zaune a falo har Hajja da Ummi, Kurfi ke batun zuwa ganin an uwan Mami, Hajja na zolayarta wai sai da iznin mijinta ta kirashi. Haka sallamarta ta ratsa dodon kunnensu. Tasleem ce, da sauri Kurfi ta mi e, itama a guje ta taho suka rungume juna ana murna. Sai kuma aka fashe da kuka, ashe ma ba ita ka ai ba ce. Tare suke da Anti Rumaisa da sauran yaranta. Ta saki Tasleem ta arasa a guje ta fa a jikin Anti Rumaisa, itama ta rungumeta tana fidda kwallar farin ciki. .Sai da suka nutsu sannan suka arasa ga su Hajja. Bayan gaishe-gaishe da maida yanda akai Anti Rumaisa ta ce. "Dama fa komai ya yi farko to akwai arshensa. Lokaci ne kawai kuma ga shi nan Allah Ya nufa da zuwansa. Sai dai a yanzun ma ba a ga ta zama ba, yanzu ne lokacin nemawa kai tsari daga sharrin masu sharri don ba'asan ta inda kuma za'a ara ullowa ba duk da cewar ba fata ake yi ba." Ummi ta gya a kai. "Wannan gaskiya ne kam." "Yo ina fa, ai dama tsinannu ba za su ha ura da daular nan ba. Kwa ayayyun banza, shi ka ai ne abinda ya ri e su a gidannan. Karr nake kallon kowaccensu." Maganar Hajja sai ta basu dariya. A arshe dai Kurfi da Tasleem suka sulale suka yi aki. Tasleem ke dubanta tana murmushi. "Fa in irin halin da na shiga abu ne mai matu ar wuya wallahi. Ke kam sai addu'ar kada Allah Ya maimaita mana irinsa." Kurfin da ke kwance rigingine saman gadon ta yi matashi da filo ta amsa da ameen. "Tsakaninki da Yaya Khalid yanzu fa?" An sosa mata inda ke mata aiyi. Ta mi e zaune ta labartawa Tasleem yanayin zamantakewarsu kafin tafiyarsa da rashin waya da sauransu. Tasleem da ta saki baki kamar wata sokuwa ta jinjina kai. "Ki mishi uzuri domin na tabbatar har shi abin nan ya shafa wallahi." Kurfi ta muskuta gami da ta e baki ka "Na fa san wannan, babbar damuwar ia yin son maso wani. Mutumin da ba sona ya ke yi ba ki tuna. Matarsace a ransa har yanzu, ba zan bari kuma ya ta a gane son da nake mishi ba koda hakan shi zai zama ajalina. Ba zan bari na ji kunya ba Tasleem." "Yes, ina bayanki idan har akan wannan ne. Wallahi bana son irin wannan soyayyar domin kuwa takan wahalar da mutum. Sai dai fa ina ji a jikina Yaya Khalid na kaunarki. Zai ma so ki in sha Allah." Baki Kurfi ta ara ta ewa. "Ke ni ba wannan ba, ya maganar auren naki?" Dariya Tasleem ta yi. "Ko yau aka aura bani da case tunda ga ni ga ki." Kurfi ta fa a murmushinta, kaunar da suke ga junansu mai tsafta da kyau ne. Ranar kamar kada a rabu, sai yamma suka tafi. *** Washegari misalin arfe hu u na yamma ta shirya tsaf cikin white an d brown Atamfa wacce inkinta ya yi daidai a jikinta ya kwanta luf. Zuwa yanzu jikinta ya soma yin kumari ya dawo hayyacinsa, hakanan fatarta ta soma she i kamar yanda ya ke a baya. Ta ci ado sosai, ta fito a LAILA KURFI inta sak. Saloon za ta je sakamakon gashinta da ya dameta saboda cikar da ya yi. Sabuwar wayarta Iphone xs max ta ke dannawa daidai sadda Yakubu ya faka motar a gabanta, ta cikin gilashinta ta ago ta dubi motar da ke faman kyalli sakamakon wankin da ta sha. Ta bu e mazaunin baya ta shiga bayan ta gabatar da addu'ar hawa abin hawa. Suna fita daga gidan ta ji wata iriyar kasala ta rufeta, wannan tasa ta kwantar da kai jikin kujerar motar ta lumshe idanu. Muryar Naziru Ahmad ke tashi a wa arsa ta BAWA. Sosai wa ar ke shigarta yana ratsa ta. ar Mami, wannan farar motar fa kamar mu ta ke bi." Jin abinda Yakubu ya fa i yasa ta bu e idanu gami da waigawa. Farar honda ce nai tinted glass ba abinda ake iya gani, sai ta sha jinin jikinta, dabara ta fa o mata.
Chapter 39 · 0% Book details