Sashe 33
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Basira wacce daman abin nasu rufin asirin Allah ne, ba wani ja in ja ta amince da hakan. Ta ara da fa "Amman kema kin san halin iyar taki, anya za ta amince?" Murmushi Mama Zahida ta yi. "Haba Basira, kema fa kinsan ba na wai sai da zakara. Ina yi mata kallon wacce ba za ta yi wuyar sarrafuwa ba saboda miskilancinta. Ina mai tabbatar maki duk wani jin da in rayuwa za ta samar maki. Ke dai kawai ki yarda da dukkan tsarina." Babu batun ja in ja Basira ta amince bayan ta duba maraicin da yaranta ke ciki tun bayan mutuwar babansu. Tattalin arzikin da ya saurar musu ne aka lalla a aka gudanar da bikin yaranta mata uku saura ita Yasmeen da ta rage a gabanta. Ta kira hakan da tsuntsu daga sama gasasshe. A ranar Alhamis Kurfi da Munira na aikin gyara sashin Hajiya domin kuwa tuni Hajiya ta zuge Daddy yaran suka dawo angarenta. Burinta bai wuce ta untata rayuwarsu ba. Darajar su Munira ya raba Kurfi da in su Lauratu wa anda a lokacin har sun soma sabawa duk kuwa da garga in Hajiya. Sabon bai wuce a dalilin su na aruwa da ita ta fannin addini ba. Wannan ya yi silar da ita kanta Lauratu ta jefar da makaman ya i da agawar da ta ke nuna wa ar gida ta kwantar da kai tana kwasar ilimi tun daga tarihin Annabawa da kuma yanayin zamantakewa na matan Manzon Allah s.a.w da Sahabbai. Da wannan Kurfi ta siye zu atansu. Barin ta daga akin ya an musu ba da i sai dai sanin su na tare ya sa ba su wani damu ba. akin da su ka koma ba wani aki ne na a zo a gani ba, shi inma don Daddy ya ce su Munira su zauna ciki ne. Hajiya ba ta ja da hakan ba bisa bin umarnin Malam da ya ce komai za'a yi kar ta tsawaita jayayya har sai ya gama gyaran aikinsa.