Sashe 37
Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bedside lamp yana dubanta da alamun bacci a kwayar idanunsa. Ta wayance gami da fa "Cikina ya ke faman mur amin ne, amman na sha magani." "Allah Ya sauwake, sai dai zaryar ta me ce ce? Ki zo ki kwanta zai daina in sha Allahu." Kirjinta ya buga, to wai ma yaushe rabon da Alhajin ya sa Allah a lamuransa, ita dai ta saddakar yanzu aikin ya ta are, ba kuma za ta biyewa sa o daga India ba, za ta arawa wannan Malamin nasu ku *** Hajiya tun safe ta fice tare da Zahida daga gidan zuwa ga Malam, wannan ne ya ba Kurfi damar aukar ruwan addu'ar da suka ara yi ta nufi sashin Daddy. Da salamarta ta shiga ya amsa, yana zaune yana karyawa ya bi ta da kallo fuska auke da murmushi. Zo ka ga murna wajen Kurfi, ta arasa ta dur usa ta gaishe shi. "Lafiya alau Lailar Majnun." Ya Allah! Ta rasa yanayin da ta ke ciki na da i sai hamdala ta shiga jerawa a zuciya. "Eh fa, dole ki yi dariya ai tunda yanzu kin samu Majnun inki. azun nan mukai waya da shi nake cewa ya kira ki kuwa? Bai dai ba ni amsa ba ya katse, na fi zaton network ne." Ta kasa jurewa sai kuka, kuka ne na murna da farin cikin sun yi nasara. Daddy ya shiga ru ani, dama ya ga sauyi da yawa tattare da komai. Yana son tambaya sai dai ya rasa ta inda zai soma. "Wai ni kam meke faruwa ne har haka a gidannan? Dagaske kwanakin nan naga abubuwa da dama hakanan na yi mafarkai nasu firgitarwa. Kamar yanda na kasa manta ranar da su Maijidda suka aukk Hajja sadda muke ari wajen ha a ku in aikinta amman abin ya i yiwuwa. Ke iya ce a wajena Laila, ki taimaka ki fayyacemin komai har da wa anda na manta zuciyata ta kasa gaskata cewar ba mafarki bane." Anan ne ta samu nutsuwa gudun kada murna ta susuta ta, ta mike ta nufo inda ya ke ta zauna gami da tankwashe afafunta. Tiryan-tiryan ta ba shi labari, tana yi tana kuka, ba ta oyemasa abu aya da ke faruwa ba tunda ta riga tasan ko ma mene ba a hayyacinsa ya yi ba, idan ma ya ce ya manta ba zai tuna ba to kuwa iyakar gaskiyarsa ya fa Daddy tun yana ambaton Innalillahi, har sai da ya kai da ya soma kuka, kuka kuwa mai yawa ba wai hawaye ba. Hankalinsa ya tashi ainun da tuna irin cin kashin da sukai ga Mahaifiyarsu. Ya tuna komai, ya tuna abinda ke faruwa. Bai manta yanda ya ke jin tausayi da wani nauyi a asan ransa ba, sai dai kuma bai iya ya aikata komai ba. Toh fa a lokacin ba jimawa sosai sai ga Baba Mudassir da Abbanta sun zo sashin Daddy. Nan kuwa kowa ya dunga fa in damuwar ransa da yanda lamura suka juye har da ikon da matan suka dunga yi da su. Baba Mudassir mai zuciya kusa nan take ya furta kalmar saki ga Zahida. Daddy ya dubeshi. "Ai ba kai ka ai ba, nima..." "Aa Daddy, don Allah, kar ku yi haka, kar ku maida yaranku marayun karfi da yaji. Ku yi ha uri Daddy, ku yi ha uri ku yafemusu." in Kurfi cikin kuka mai tsanani na tausayin iyayenta maza ganin yanda sosai suke zubar hawaye. Daddy ya dubeta. "Ke wace irin zuciya gareki Laila? Anya kina a hayyacinki kuwa?" Ta gya a kai. "Eh Daddy, nasan me nake fa i, nasan komai. A hayyacina nake. Daddy ba zan so ku rabu ba, idan kun rabu da su kun san wa anda za ku auro? Ku yi ha uri Daddy, ku yi musu kowane irin hukunci amman domin Allah ban da saki. Baba kaima ka janye sakin nan." Ta karashe tana dua Baba Mudassir, su Munira ma wa anda tuni sun shigo jin hayaniya da kuma jin kalar hayaniyar irin wacce suka jima suna fata ne, ba su yi jinkiri ba gun shigowa. Baba Mudassir wafa ya yi bai ce komai ba. Hajiya tun shigowarsu ta ji gabanta na fa uwa, ta dubi Zahida. "Kinga motocinsu, basu fita ba. Na shiga uku, kada dai mun makaro aikin ya lalace kamar yanda yace?" Mama Zahida itama kanta ciki ya uri ruwa. "Kai aa, zo dai mu arasa." Daga haka suka fito daga motar bayan Mama Zahida ta gama saita parking inta, shiga ciki sukai. Don su tabbatar sai kowacce ta nufi sashinta duba mijinta. Hajiya tun kafin ta arasa shiga ta sha jinin jikinta ganin takalman su Mudassir. Ta daure ta shiga da sallama, ji ta yi kamar ta juya ta koma. Fitsarin da ya cika mararta ta ji alamun yana shirin kufce mata, ta kasa magana saboda kallon da kowannensu ke watsamata. Za ta juya muryar Daddy ya daki dodon kunnenta. "Saudatu!" Ta juyo a rikice, ta dubi Daddy kafin ta dubi Kurfi wacce ke kallonta fuska auke da tausayin irin rayuwar da ta za ar wa kanta. Ta kauda kai ta araso ciki. "Gani." "Kin cuce ni Saudatu, kin cutar da rayuwata. Kin kuma aikata abinda har na mutu ba zan iya yafemaki ba. Allah Ya isa tsakanina da ke Saudatu. Kece irin matan da wutar jahannama ke jiransu, ke ce irin matan da ba za su ta a jin amshin aljanna ba. Ba zan yafemaki ba Saudatu, na tsaneki. Tun farkon samartakana ki ka cutar da ni ta hanyar sanya wa na aureki ba da ra'ayina ba, hakan bai ishe ki ba sai da ki ka shiga tsakaninmu da mahaifiyarmu da dukkan an uwanmu. Wallahi ki sani kin zaluncemu kuma kin zalunci mahaifiyarmu. Kin kuma zalunci matar da na auro wacce ba tai miki komai ba, asalima Raliya burinta a koyaushe ta kyautata maki ta ga kun ha a kai. Ba zan miki baki ba, sai dai ki sani, ha okin da kika auka ka ai ba za su bari ki runtsa har ma ki samu kwanciyar hankali ba! Ki je na sake ki saki biyu! Har abada ni Hamza na gama zama da mace irinki mai aiki irin na an wuta! Ki fita ki bar min gidana kar ki ara minti biyar domi wallahi ki ka ara an sanda zan auko maki." Daga haka ya mike a fusace kamar zai kai mata duka, ji ta yi ta muzanta, ta fice daga akin da sauri ta fa a nata akin ta soma tattara abinda za ta tattara ciki kuwa har da dukiyoyinta. Tana yi tana kukan bakin ciki. Kurfi dai kuka ta ke sosai, har a ranta ta so a ba Hajiya dama, ta so ace zuri'arsu sun ha a kai. Tana son an uwanta. Sai dai kuma hakan shi ya fi musu alheri. Suka yanke a ranar zasu je Kaduna ba sai gobe ba. Sai a lokacin Kurfi ta samu matsawa jikin Abbanta ta rungume afafunsa cikin kuka da tsananin kewa. Shima ya ri e kafa unta yana hawayen. "Forgive me My Angel, Forgive me please." Ya fa i cikin zubar hawaye. Ta ago gami da girgiza kai. "Ba ku da laifi Abbana, har abada ba za ku ta a yi min laifi ba. Saboda na yarda komai *MUKADDARI* ne daga Allah. Ba ku da laifi, kar ku nemi gafararmu, Hajja ta fi bukatarku a yanzu." Ta fa i tana kallon Baba Mudassir da Daddy. Suka jinjina kai. "Allah Yay miki albarka Laila, ha a ke a ce ta gari wacce kowane uba zai alfajari da kasancewarki iyarsa. Allah Yay miki albarka." Baba Mudassir ke wannan furucin sadda ya araso ya dafa kanta. Ta yi murmushi cikin hawaye. "Madallah da a kuma suruka irinki Laila." Fa in Daddy yana murmushi mai bayyana ha ora. Ta sunkuyar da kai tsabar kunya. Daddy ya dubesu. "Sai ku shirya mu kama hanya gaba aya har yaran." Da wannan murna da farin cikin suka fito. Sun tarar tuni Hajiya ta fice. *** Mama Zahida na zaune a falo a tsorace, Baba Mudassir ya shiga. Ta wayance gami da basar da yanayin kallon da ya ke jifanta da shi. "Ah Baban yara ba ka riga ka fita..." "Dallah can rufemin baki! Ai ke da aminiyarki dai wallahi ba kwa tsoron Allah. Kuma ki sani tun kafin ki dawo daga yawon gidan Bokayenku na sauwa e maki, ki tattara ki ficemin a gidannan wallahi tun kafin na gama shiri, ban kuma yarda ki auki ana ko guda ba. Idan kuwa na fito na iske ki to wallahi ranki ne zai mugun aci! Shashashar banza!" Yana kaiwa nan ya fice sashinsa. Zufa ta shiga ketowa Mama Zahida ta hau kuka da ihu tana zagin Hajiya gami da tsine mata. A arshe ta ha a iyaka abinda za ta iya ta ara gaba bayan ta auki mu ullin motarta. Ta kuma rantse ta ara akan ko ku in aljihunta zasu are sai ta dawo cikin zuri'ar Khalid Kurfi. *** Bayan fitarsu Daddy ya yi shiru ya yin da zuciyarsa ke zafi, ya kira Hassan da Hussain ya ha a conference call, nan ya ke labarta masu komai. Hassan ya ce. "Haba, Daddy wallahi yau da munanan mafarkai na tashi, jikina ya bani ba lafiya ba. Abubuwa da dama da na aikata sai yanzu nake jin ciwonsu. Kullum na zo gidannan nakan ji kamar sauyi da unci. Yanzu Hajiyata keda wannan aikin?" Hussain kuwa Innalillahi kawai ya ke ta nanatawa. Nan Daddy ya an musu nasiha arshe ya sanar musu da cewar yau zasu shiga Kaduna. Suma suka ce zasu je, ba batun neman izni a ma'aikata Kasancewar kasuwancinsu ashin kansu su ke yi don haka suka soma shiri.